KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Yazeed ya zama shock ma dan shi baya ko irin kai wa yan siyasa ziyara da akeyi balle ya saci kudi daga jin magana akwai tuggu a ciki. Bakinsa na rawa yace menene hadin companies din mahaifi na da za’a saka a ciki ? Luku yace saboda idan ta tabbata gaskiya zai zama na gwamnati wai shine hukuncin ka.

Yace ya batun Wanda na bayar dasu ga families Dina? Luku yace eh wannan basu da harka dashi tunda yanzu ba naka bane ajiyan zuciya ya sauke tace atleast munada yadda zamuci abinci maza ka hada meeting da uncles Dina baki daya on Saturday, Luku yace sure kamin ya fice.
Gumi ke tsattsafowa yazeed domin ba dukiya daya rasa bane ta dameshi yadda aka bata masa suna bai ji ba bai gani ba. Rungume sa minal tayi tare da kwantar dashi a kirjinta tace yazzy baby karka damu komai zai wuce is part of kaddarar mu.

Haka yaci gaba da basa baki har yayi bacci a kirjinta sai alaokacin ta lura da yadda hawayensa ya kika Mata Riga. Ajiyan zuciya ta sauke kamin tayi nata kukan Dan ta daure ne kar ta karya masa guiwa.

?????????

?Darius take shekawa abinta tare da cewa kai nifa shegiyace duk wadda ya taboni toh shida kwanciyan hankali sun raba kafa kamar aljanna da wuta.
Mummunin Alhajin da take zaune a cinyarsa ne ya sheke da dariya yace kaji shegiya wai dama kinsan akwai wuta da aljanna kike wannan tsiyar? Hade rai yayi Tace me kake nufi? Daidai lokacin wayanta yayi ringing ta dauka tace ya akayi ta dayan bangaren akace gaskiya fa madam mugu(bokanta) yana korafi cewa idan dai bazaki dinga zuwa yana biyan bukatar sa ba to saide ko dinga aiko da jarirai uku idan ba haka ba ku ?a?e. Tsaki Taja tace ni rabani da jarabarsa ban iyawa ga warin da yake zan karo ma 500k a samo Karin jaririn akai masa. Ta dayan bangaren akace hakan ma yayi.
Daga nan ta kashe wayan Alhaji yace amma baby wai me suka miki hakane kika tsanesu da kike kashe irin wannan kudi? Murmushin rashin imani tayi tace hmm bazata gane ba. Yace ada na barsu ganin abokin hamaiyar tawa ya mutu amma yanzu Dana hadu dake sai naji dole ma in ga kayansu musamman yanda dan ke nema yafi uban yin nasara.

Sauka tayi daga cinyarsa tare da fara safa da marwa a dakin tace kiyaiyar danake musu tafi Wanda kafirai keyiwa annabi na samesu fiye da yadda na tsani mutuwa ta kai Alhaji bari kaji idan har zanga sun kaskanta sun wahalu a duniya toh wallahi babu ja in ja na yarda in shiga wutar jahannama indai sun wahala. Banida matsala koda kuwa za’a ha?a ni da shedan a wuta a matsayin roommates.

Jinjina kai yayi kamin ya tattaro ya harhado tumbinsa ya Mike yaje ya rungume ta ta baya yace yanzu ne na ha? da macen data dace wacce bata tsoron ta baci indai saurinta zai cika gaskiya wannan jawabi naki ya kara sa min kaunarki a zuciyata.

Juyawa tayi tace Allah Alhaji na? Yace kwarai ma kuwa yanzu yadda zamuyi dasu Dan nima a shirye nake tsanani dai ace wuta za’a samu toh ni ALHAJI TUKUR GADON ?AYA na bada ticket din aljanna ta Dan in kuntata ma ahalin ALHAJI ABDULMAJEED UMAR. Dariya suka fashe dashi tace kaga mu hanzarta domin na koma gida daga nan suka shiga aikata ashararancin su.

WANENE ALHAJI TUKUR GADON KAYA? WANI ATTAJIRIN MAI KUDI NE WANDA SUKAYI TASHE TAREDA ABDULMAJEED WATO BABAN YAZEED INDA YAKE DAUKE DA MUGUN HASSADA MA ABDULMAJEED SABODA YA FISHI YIN NASARA.
DA FARI JEEDMAR A BAUCHI SUKE DA ZAMA TAKURAR DA TUKUR GADON KAYA YA MUSU YASA SUKA KOMA GOMBE NAN MA YA BISU,SUKA LULA ADAMAWA,YA BISU SUKAYI KANO, YA BISU SUKAYI, SOKOTO LOKACIN AN HAIFI YAZEED AMMA YA BISU NAN MA SAI SUKA KOMA ABUJA TOH ANAN NE SUKA ZAUNA NA SHEKARA 4 KAMIN YA SAKE BIYOSU SUKA KOMA KADUNA ANAN NE AKAYITA TA KARE TUNDA ABDULMAJEED DIN YA MUTU BA SHIKENAN BA? TOH ASHE
DAI BAI HAKURA BA GASHI KUMA YA SAMU WACCE TA FISHJ DAUKAN ZAFI LAMARIN SAI YADDA ALLAH YAYI.

Ina mai lallashin ku na rashin jina da kuka yi abubuwa ne suka Dan taso min da fatan za’a min uziri?

Shin me zaku iya cewa gameda batun Alhaji TUKUR GADON KAYA? Ya kuke ganin lamarin nan zai kaya a tsakanjn su ?

Shin in karar da littafinnan da wuri ko kuma acid gaba da gashi?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

Miss_untichlobanty ?

14th September, 2020

??KURUCIYAR MINAL??

?by miss Untichlobanty ?

?CHAPTER 75?

Sauri minal keta yi tana tsallake steps da bibbiyu saboda lattin da sukayi domin yau jirginsu zai daga zuwa Abuja inda zasuje baban jeedmar group kuma anan ne za’ayi meeting din tallafawa yazeed kamin government ta wankesa.

Bude Mata kofa kurtu yayi ta shige luku ya finciki mota. Ba bata lokaci jirginsu ya daga sai federal capital territory of Nigeria.
Koda suka isa yazeed bai tsaya isa gida ba direct jeedmar group ya nufa. Sunayin parking ya fito cikin kwarjini da haiba yana? takunsa mai daukan hankali gwanin ban sha’awa. Dukda cewa a cikin damuwa yake hakan bai hana kyawunsa fitowa ba.

Ezekiel da lukman kawai aka bar masa a matsayin escorts dinsa, sai masu gadin gidansa shima an rage wasu daga cikin su. Haka masu yin hidima duk an rage masa kuma duk munafurcin Alhaji tukur gadon kaya ne.
Tun daga bakin kofa ake gaishe sa tare da buda hanya yana zuwa bakin kofan shiga kofan yace “new individual detected please wait ……” scanning iris dinsa yayi kamin yace “welcome president it is nice of you to visit kindly put your thumb”
Saka thumb din nasa yayi take kofar ta bude masa gaba daya directors sun jeru Dan haka yana shigowa suka bi bayansa.?
Files suka fara miko masa ya daga musu hannu alamun not now. Suna shiga gaba daya uncles din nasa suka Mike Yana zama suma suka zazzauna. Yace good day to you all ! As we already know we are here to discuss…….. nan ya musu bayani ya sanar dasu duk abinda yake wakana sannan yace zasuyi signing contract before abubuwa su wartsake masa zasu dinga bashi 10% percent na ribar da suka samu idan companies dinsa suka dawo zai biya su.

Abinda ya basa mamaki shine yanda sukayi caaa! Sukace Sam Sam basusan wannan labarin ba. Daga karshe ma watsewa sukayi ba’a gama meeting din ba hakan yasa ran yazeed ya baci kuma ya tabbatar da cewa hatta dan uwan ka zai iya cutarka sannan sai ka shiga matsala zaka gane masu sonka.? Fita yayi suka tafi ainihin family house dinsu dake central area, ba’a cewa komai domin yafi na Kaduna kyau masha Allah tabarakallah.

A parlour ya samu minal ga abinci an kawo Mata amma ta kasa ci tayi jungum jungum. Umma hanifa dattijuwa ce kuma me aikin su yazeed ne tun suna Abuja ganin batada kowa na dangi sai Allah yasa koda zasu bar Abuja basu sallame ta ba, sai suka barta taci gaba da zama a gidan tana gyarashi kuma ana biyanta kudinta har yau sannan ba ita kadai bane akwai maids guda goma.
Gaishesa sukayi kamin suka watse, gaisawa sukayi da umma hani kamin ta basu waje saboda ta fahimci suna bukatar hakan.

Riko hannun minal yayi zuwa daki duk ta kagu taji yadda aka kaya suna shiga tace da fatan komai lafiya? Ajiyan zuciya kawai yayi, hakan yasa ta fahimci me yake nufi baki ta basa kamin ta dauko musu abinci cikin Muryan shekiyanci yace bazai ci ba yasani ko akwai poison a ciki ta masa pancake kawai kuma hakan akayi.

Kwanciya yayi bayan yayi sallar azahar ta ja masa bargo kamin ta koma kan couch ta fara nazarin yadda lamarin zai bille. Zaro ido tayi tare da murmushi alamar idea tazo Mata hakan yasa ta nufi jakar yazeed ta dauko paper da pen ta fara rubuta list. Sallan la’asar da aka Kira? yasa ta tasheshi tana mai cigaba da rubutu. Saukowa yayi tare dayin bismillah yaga ta nata rubutu baibi ta kanta ba yayi alwala ya fito still tana rubutu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button