KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Bakin zakiyya na rawa tace tare kuke aiki ? Mummy tace what do you expect?look young lady idan ma baki sani ba ki sani ayush ce kadai yata ke da yayarki a gidan marayu na dauko ku meaning? maman su safwan ma is not your biological sister that is you are all alone.

Zakiyya tace mummy me yasa zakiyi min haka? Mummy zakiyyan ki ne fa! Mummy…… yatsa mummy ta daura Mata a baki tace ya isa please no complaints. Riko hannun ayush tayi tace baby go ahead. Wani allura suka soka Mata a take ta zama paralyzed.

Mummy tace dont forget after three three months zakina yin wani okay? Tace okay mummy. Ya batun gidan anyi settling komai ? Tace yes nasa anyi photoshopping pictures din the guy is an American so ya iya aikinshi sannan umma hani ma bazata iya musa duk wani Abu da zamu ce ba tunda boka yayi mana maganin bakin ta.

Ayush tace wow mama na you are too great wallahi,naga pictures din. Nuna Mata tayi tace wow bazaka tana cewa hada hotunannan akayi ba. Tunba wannan da muke yara ba. Let’s hurry up mu kama hanyan Abuja nasan yazeed ma I mean bro ya suma already muje kamin ya tashi.

Dariya mom tayi tace sh*giyar yarinya wai bro, suka fashe da dariya. Zakiyya tana gani kuma tana ji amma banda ?yafta ido babu abinda zata iya yi.
Ko hawaye saide idonta su ciko. Wheel chair suka daura ta goje ya turata ya fitar da ita. Sannan suka fitar da minal ma.
Dadai maraba gaban karo international market suka yarda minal suka barta kwance Shabe shabe kamar macacciya……….

IS ANOTHER UPDATE

KOWACCE TA TOFA ALBARKACIN BAKINTA.

KUN TABA TSAMMANIN AYUSH CE MUNAFUKAR?

YA LAMARIN ZAI KAYA NE WAI? INA TSIMAYIN COMMENTS DINKU.

KARKU MANTA KUYI SHARING DOMIN WASU SU SAMU.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

Miss Untichlobanty ?

14th March,2020

??KURUCIYAR MINAL??

?by miss Untichlobanty ?

?CHAPTER 78?

RECAP
Zakiyya tana gani kuma tana ji amma banda ?yafta ido babu abinda zata iya yi.
Ko hawaye saide idonta su ciko. Wheel chair suka daura ta goje ya turata ya fitar da ita. Sannan suka fitar da minal ma.
Dadai maraba gaban karo international market suka yarda minal suka barta kwance Shabe shabe kamar macacciya……….

CONTINUATION

Cikin garin Abuja suka shiga inda suka nufi gida direct yayinda ayush ta tafi hospital saboda already an kirasu cewa yazeed is unconscious.

Koda ta isa asibitin dakin da yazeed yake aka kaita, kwance yake cikin kayan asibiti, fuskarsa tayi fayau ya Dan rame kadan. Baki ta tabe tare da yin murmushi tace soon I will be ruling everything sannan ta Sami waje ta zauna.

…..

Ummu Amina ce ta fito daga gidan ta damuwa dauke a fuskarta ta shiga makwabtan su. Sallama tayi uwani ta amsa tare da yi Mata barka da zuwa gaisawa sukayi a tsatstsaye uwani tace ummu amina haryanzu yarannan shiru? Anya lafiyar su kuwa ? Dan tsanani kwana uku suke dawowa gida amma yanzu dubi satin su daya ba ko labarin su. Ummu amina tace ai shiyasa nazo mu fita mu nemosu, Dan garin habujan nan? tsoro yake bani masu kudin nan yawanci yan shan jini ne balle yaran mu sun fito daga kauyen habuja yanzu sai a rudesu ga maraban nan badai mutane ba. AI muna samun su kawai tisa keyarsu zamuyi mu tafi Suleja? ko ya kika ce? Uwani tace nima dai haka nake gani amma zan shawarci me gidana, Allah dai ya shirya mana zuri’a. Ummu amina tace ameen. Nan uwani ta zaro mayafin ta suka baza cikin gari domin neman ‘ya’yan su wato sabi’u da lado.

Uwani dai itace mahaifiyar lado yayinda ummu amina take mahaifiyar sabi’u Wanda ake Kira da sabi nigga. Ummu amina batada burin daya wuce ta haifi dariya mace tasa Mata amina saide Allah bai bata ba sai da daya data Haifa wato sabi niga Wanda ya Santo mata ala?a?ai, dahaihuwar sa gara babu.

Yan jihar nasarawa ne amma a maraba suke zama, sai lokacin noma yayi suke komawa nasarawa su noma doya sai su dawo su siyar.

Shi da lado basuda aiki sai yawo a garin su daki wancan,su sari wancan, su ?wace kudin wancan, ayi bangar siyasa dasu, su tsokano yan sanda. Kullum dai cikin matsala suke gashi suki aure. Toh ko zasuyi ma wa zai basu yarsa?

??

Hadiri ne ya hadu baki kirin, sai tawa da cida ake yi hakan yasa ummu amina da uwani labewa a zauren wani shago aiko ruwa ya barke ba kakkautawa.
Ruwa daya fara dukanta yasa ta bude idanun ta da sukayi Mata nawi. Gaba daya jikin ta ciwo yake Mata dakyar ta zauna kawai sai ta fashe da kuka domin gaba daya ji take zuciyar ta mata nawi ga bakin ciki da takeji. Kokarin tuno wani Abu tayi amma taji dib banda sunanta ba abinda ta sani kamar yanzu aka cillota duniya. Jin motsi a cikin ta yasata kallah, me zata gani cikin da ita. Toh fa anan ake yinta.

Tunani ta fara wai shin hatsari tayi ne? Cikin waye? Tana ma da aure? Su waye iyayenta? Waye mijinta? Daga ina take? Ganin babu amsa yasa ta kara fashewa da kuka. Tsananin kukan da take yasa hankalin su uwani yayo kanta. Ummu amina tace Allah sarki wancan mahaukaciyar kyakkyawa ko wani azzalumi aka samu ya dirka mata ciki ? Ga ruwa na dukanta ka bibiya yunwa ma takeji yasa ta kuka. Uwani tace har ta bani tausayi amma yanda kika ganota da kyannan kika bibiya hamshakiyar karuwa ce. Ummu amina tace kai nide ban yarda ba, uwani li fadi ALKHAIRI ko kiyi shiru. Bari in dauko ta in shigo da ita kasar rumfannan kar abinda ke cikin ta ya lahanta.

Nufo minal din tayi jiki na rawa Dan tsoron kar mahaukaciyar ta rufeta da duka. Daga dan nesa nesa tace baiwar Allah, minal tana dago kanta cak, ta tsaya da kukan lokaci daya taji kaunar ummu amina ya kamata babu bata lokaci ta fara kokarin mikewa. Taimaka Mata ummu amina tayi ta Mike a take ta rungume ta. Tare da kokarin fadin umma ? amma me sai taji ta kasa magana. Jan hannun ta ummu amina tayi ta kaita kasan rumfan. Haka aka gama ruwa tace mu tafi ko ? Ummu amina ta kalli minal tace toh baiwar Allah mu zamu tafi ki tafi gida, kema ki tafi gida kar zazzabi ya rufe ki. Riko hannunta minal din tayi uwani ta yarfa tare da fadin sake Mata hannu Dan Allah. Kema ummu amina laifinki ne daga ganin mutum waike uwar taimako ko? Haka uwani ta rufe ido tanata masifa wai ummu amina ta fita shiga harka da ba’a gaiyace ta ba.

Ummu amina kuwa fadi take haba uwani ki bari ko abin ci mu bata mana, mai ciki fa abin tausayi ne.
Minal kam yunwa takeji ga sanyi, haka ta dinga karkarwa ga zazzabi daya rufeta. Tashi tayi ta fara tafiya ga jiri dake dibarta. Wani suya spot ta gani taje gefen wajen ta tsaya sai hadiya yawu take tana kallon yanda mai ke diga daga jikin naman. Wani guntun biredi aka bata aiko ta hau mamuka har tana ?warewa.
Kowa idan ya gama cin abinda zaifi sai ya bata guntun. Mai suya dai abin ya fara bashi haushi dan haka ya cika yayi fam saura fashewa.

Former lieutenant sabir (Wanda ya rasa aikin sa na dan sanda saboda yace bazaiyi rashin gaskiya ba)ya siyo doya Wanda za’ayi breakfast a gidan da yake gadi ya hau babur dinsa kawai yaji yana marmarin suya hakan yasa ya tsaya tukuban da minal ke gefe. Haka aka kawo mai yana ci yana kallon ta, ji yake kamar ya San ta amma da ta fara tunani sai kansa ya fara ciwo kawai sai yaji ya kasa ci saboda kallon naman da take ta yi.

Mai tukuba kam ganin kamar saboda ita sabir ya kasa ci yasa shi fara Koran ta kuka ta fara masa tana cijewa Dan bata koshi ba ya fara hankadeta. Sabir ne ya saka masa tsawa. Kwalarsa ya damka rate da fadin kai wani irin wawa dabba ne? Bakasan Kima da darajar mace bane, bakaga ciki ne da ita ba zaka na hankade ta? Ko muharramar ka ce da zaka taba ta?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button