NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kiyi haƙuri fa”.

Budurwan me suna Safna tace, “no babu komi”.

Sannan ta duƙa ta soma kwaso ma Ɗahira files ɗin, itama duƙawa tayi ta taya ta har suka gama kafin ta’amsa na hannun ta ta wuce

Bayan ta Safna tabi da kallo har ta ƙule sannan ta saki ajiyan zuciya tana murmusawa a ranta tace, “Tana da sauƙin kai ba kamar wancan bugaggiyar da mu kayi karo da ita ba”.

Juyawa tayi taci gaba da tafiyan ta har ta’iso wajen lifter ta buɗe zata shiga, ji tayi an bangaje ta an shige, tana ɗago kai taga Yusra, a ran ta tana mamakin halinta, yanzu suka gama karo da ita ta balbale ta da tsiya but gashi yanzu ta buge ta bata ce mata tayi haƙuri ba. ɗauke kai kawai Safna tayi ta shige ciki tare da danna Number liftern ta rufe.

     Yusra ta soma sauka kasancewar office ɗin ta a hawa na biyu yake sannan ita kuma Safna ta sake latsa number yakai ta ƙasa, wasu files taje ta'amso a reception sannan ta sake hawa ya maida ita block 4 inda anan ne office ɗin ta yake, tana ɗaya daga cikin waɗanda aka ɗauka sabbi.

              ⚫⚫⚫

           Ƙarfe 01:00pm. Ta gama duba marasa lafiyan ta, miƙewa tayi ta shiga Toilet ɗin cikin office ɗinta ta ɗauro alwala ta fito, sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da Sallah sannan ta miƙe ta ɗau duk abinda take buƙata ta zuba cikin jaka ta fito ta rufe office ɗin, lifter ta hau ya kaita upstairs na 5 inda anan ne office ɗin mahaifin ta yake, Direct office ɗin ta nufa tayi nocking aka bata iznin shiga, tura ƙofan tayi ta shige da sallama a laɓɓanta

Abbu ganin ƴar shi da yafi ƙauna cikin ƴaƴan shi a office ɗin sa yayi matuƙar saka shi farin ciki, cike da fara’a ya’amsa mata yana cewa, “Mama na”.

Ɗahira da itama take faman doka murmushin ta ƙariso ta zauna tana cewa, “Abbu Barka da aiki”.

“Yauwa Mama na ya naki aikin?”

“Alhmadulillah Abbu”.

Abbu yace, “masha Allah haka ake so, har kin tashi kenan?”

“Eh Abbu, nazo ganin ka ne sai mu wuce tare”.

Murmushi yayi yace, “Mamana kenan ai ban tashi ba, ina ga yanzu sai zuwa 04:00pm.”.

Gyara zaman ta tayi tace, “to Abbu bari in jira ka sai mu tafi tare”.

“A’a tashi kije gida ki huta Mamana ba na son ki zauna nan, kin ma ci abinci?”

“A’a Abbu”.

Coolarn dake kan desk ɗinsa ya turo mata yace, “ɗauka ki ci”.

Duk da ba ta jin yunwa bata yi masa musu ba ta ɗauka ta soma ci, kaɗan taci ta tsame hannun ta ta shiga Toilet ɗinsa ta wanko hannu ta dawo

Lokacin ne Abbu ya ɗago kai daga rubutun da yake yi yace, “Kin ƙoshi kenan?”.

Gyaɗa masa kai tayi sai kuma tace, “Abbu ko ma ban ƙoshi ba idan na koma gidan zan sake ci ai”.

“To shikenan Allah ya miki albarka ki kula kinji”.

“To Abbu byee”.

Ta ɗaga masa hannu sannan ta fice tana murmusa wa, tana fita haraban asibitin ta shige motan ta taja tayi gida, bayan tayi parcking ta fito ta nufi Part ɗin su, sai da ta soma shiga ɗakin Mamanta ta sanar mata dawowar ta sannan ta nufi ɗakin su, wanka ta soma yi ta shirya cikin wata koriyar atamfa ɗinkin Buba ta ɗaura ɗankwalin shi, eyeglasses ɗin ta tasanya ta fito ta nufi kichen, abinci ta ɗiba ɗan kaɗan ta fito parlour ta zauna tana ci, lokacin ne itama Fadila ta dawo

Ɗahira amsa mata sallaman ta kawai tayi taci gaba da cin abincin ta idanuwan ta na kan t.v, bayan ta gama ta tashi tamayar da plate ɗin kana ta wuce ɗakin Mamanta, tana tura ƙofan da sallama Aunty Amarya ta ɗago kanta daga karatun Hisnul Muslim da take yi, ta kalle ta tana amsa mata sallaman

“Mama bari inje wajen Kaka”.

Gyaɗa mata kai kawai Maman tayi ta maida hankalin ta kan littafin ta, ita kuma Ɗahira ta fice.
[5/23, 8:53 AM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
             FAMILY DOCTORS
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
  NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT ????????‍

بسم الله الرحمن الرحيم

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION????

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A✍️*

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattpad: UmmuDahirah????
        

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

          NASIHA
Sallar natsatstsu ba ta samuwa sai an kare sallar daga duk wani abu mai shagaltar wa, a kuma yi ta cikin lokatai waɗanda ba su hana yin Sallah da zuciya ɗaya kuma ba su zama shamaki tsakanin zuciyar sa daga kome ban da tunanin Allah, sai Allah ya haskaka masa zuciyar sa, ya sami basira ya ji daɗin saduwa da Ubangiji. Daga nan sai ka ga Bawa kullum yana mayar da hankali sosai ga wanda yake ganawa da shi. Wannan ma ya fi ƙarfi cikin sujada domin kuwa Bawa ya fi kusa da mahaliccin sa lokacin da yake cikin wannan hali. Don more wa shi wannan muƙami an ji Manzon Allah yana cewa, “Bawa ya fi kusanta ga Ubangiji. Saboda haka ya yawaita addu’a.”

        EPISODE Nine

       Cikin siririyan muryan ta tayi sallama tana shiga ciki

Kaka dake zaune saman Wheel chair ɗin sa yana karatun jarida ya ɗago yana kallon ta, sannan ya’amsa mata sallaman yana cewa, “Maraba lale da matata abar ƙaunata, yau ga matata ta zo gare Ni”.

Murmushi me burgewa Ɗahira ta saki tana takowa wajen sa ta zauna a gefen gadon sa tana cewa, “Kakus kenan baka rabo da tsokana ta, sai kace ka daɗe rabon da ka ganni”.

Smile yayi yace, “Matata kenan ke baki san yanda nake ji dake bane, yau gaba ɗaya ba na jin daɗin rasa ki kusa dani, Allah da ba don kar in so kaina da yawa ba, da sai ince ki zauna a gida abinki ba sai kinyi aiki ba, tunda gani Mijin ki Ina son ki kusa dani”.

Dariya sosai Ɗahira tayi kana tace, “Kaka kenan hmm Mijin kwali ko, don dai a kan ka dai bazan iya ajiye aiki na inzo in tare a wajen ka ba”.

Zaro idanu yayi yace, “au kina nufin ban kai matsayin da zan iya auren ki bane na zama na ƙarfen?”.

Sai kuma ya girgiza kansa yana dariya yace, “to bari kiji Ni ɗin Ni ne dai Mijin ki da zaki yi alfahari dashi nan gaba don babu wanda zai so ki fiye da yanda nake ƙaunar ki, har da wanda kike son min gori akan sa”.

In ban da dariya babu abinda Ɗahira take tiƙawa, sosai Kaka yake ba ta dariya idan suna zancen nan, kuma sai ya fuske tamkar da gaske ne maganar tasa

“Hmm ci gaba da min dariya, ban da abinki ma ni fa taimakon ki zan yi, kin san Real Matata tafi ki komi baza ki haɗa kanki da ita ba”.

Wannan karon murmushi tayi tace, “Kakus nawa Ni kaɗai, kaima ban da abun ka me zan yi da tsoho irin ka, idan har matarka ta fi ni komi ai nima Mijina ya fi ka komi, kuma idan kace ƙarya zan kawo maka shi ka ganshi”.

Cike da jin daɗi Kakan yace, “yauwa Jabun Matata ki kawo min shi dama na daɗe ina burin ganin sa, kin ga sai a gwada aga wanda yafi kyau cikin mu, ke kaɗai ce dama ban san saurayin ki ba, amma kin ga su rasa kunya ɓeran tanka duk sun kawo min su na gani”.

Numfashi Ɗahira taja tana kallon sa don ita bata san ma me zata ce mishi ba, ita da bata taɓa yin saurayi ba taya zata kawo masa wanda zata aura?

“You are silent my wife? I love to see who you will marry more than the other children. Burina kenan inga Mijin ki inga wanda zai iya riƙe min ƴar ƙwai na da amana”. Kaka ya ƙarike maganar tasa yana kallon ta da alamun dagaske yake yi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button