NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

Bata yi yunƙurin hana sa ba, illa lumshe idanu da tayi tana matse bakin ta, buɗe idon tayi cikin rawan baki tace, “How can you tell you what is wrong with me? What have I done? How can Yaya Usman hate me? Meyasa yake son muzguna ma rayuwa ta? Shin na taɓa yin masa laifi ne a rashin sani?” Taƙarishe maganar cike da ɗacin zuciya hawayen na silalo mata daga kuncin ta

Sake damƙe hannayen ta yayi cikin nasa, cike da sanyin murya yace, “Ƙanwata ki dena saka damuwa a kan abinda Usman yake miki, babu abinda kika yi masa, kawai Allah ne be haɗa jinin ku ba, amma insha Allahu wata-rana sai yayi alfahri dake a rayuwan sa, tabbas watarana komi zai wuce my dear, ki saka wannan a ranki zaki ce na faɗa miki, duk inda akwai jini dole ne akwai ƙauna, ke ɗin ƴar uwan sa ce, dole zai so ki kuma zai yi nadamar hakan, Plz ƙanwa ta wannan ya dena ɗaga miki hankali, I’m not happy to see you in this situation. wlh ina ji kamar zan mutu duk sanda na ganki a damuwa, ko kaɗan ba na jin daɗi”.

Murmushi ta saki hawayen ta na sake silalo wa, cikin farin ciki tace, “haƙiƙa shiyasa nake sake alfahari da kai yaya, wlh billahi kai kaɗai ka ishe Ni a matsayin Yaya, ina son ka yayana ina matuƙar son ka fiye da yanda kake so na! insha Allahu kuma bazan sake damuwa da ko wani abu da ya nuna min ba, domin kai kaɗai ka ishe ni”.

Murmushi sosai Baffa yake yi sakamakon jin zantukan ta, tsaban farin cikin jin kalman so a wajen ta, be san sanda ya janyo ta ya rungume ta ba; duk da kuwa ba yau ya soma jin hakan a wajen ta ba

Sosai Ɗahira ta zaro ido da ganin abinda be taɓa faruwa da ita ba, tayi saurin jan jikin ta tana matsawa da sauri

Sai shima a nan ne ya gane abinda ya aikata, yayi saurin saka hannu yana sosa kai cike da murmushi a face ɗin sa yace, “I’m so sorry Ƙanwata, wlh na manta ne”.

Murmushi tayi kawai tana kallon sa, sai kuma ta gyaɗa masa kai

Hakan sai yasa yaji daɗi sosai, don be yi tunani hakan daga gare ta ba, a kullum faɗa masa take yi ba ta ƙaunar irin wannan rayuwan, duk da shi a wajen sa ya saba sosai ga friends ɗin sa da yayi school tare da su, irin wannan rayuwan wayewan shi ne Baffa ya taso dashi, babu ruwan sa don ya rungume mace, amma tun sanda Ɗahira ta soma taka masa birki shima ya rage yi, duk wani halayen sa mara su kyau da yasan za su ɓata mata rai, ya dena su, duk sabida farin cikin ta, shiyasa a kullum sake ji yake yi ƙaunar ta na ƙara wanzuwa a cikin ƙalbin sa, idan har ya same ta a matsayin matar sa kuwa; to, tabbas ya gama dace a rayuwan sa, ita ɗin haske ne cikin rayuwan sa, zai so ya kasance da ita har abada a duniyar sa..

“Yaya mu je kar muyi late”. Tayi maganar tana kallon Wrest watch ɗin dake ɗaure a hannun ta

Murmushi yayi kafin yace, “tom dear”.

A tare suka fita daga gidan.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

      Washe gari aka wayi gari Kaka be da lafiya, zazzafan zazzaɓi ya tashi dashi, sosai hankalin iyalan gidan ya tashi, nan da nan aka ɗunguma aka yi asibiti dashi

Su Ɗahira suna can labari ya riske su, ai nan ko wannen su ya kiɗime, domin ba ƙaramin ƙaunar Kaka suke yi ba, ko kaɗan ba sa son abinda zai taɓa sa, duk da kuwa ya tsufa amma suna matuƙar ƙaunar sa; ba sa son su rasa sa, ga shi be cika ciwo ba shiyasa hankalin su ya tashi da ganin yanda jikin sa yayi mugun zafi.

    Gaba ɗaya iyalan gidan sun hallara a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Kaka, kowa hankalin sa a matuƙar tashe, da yawan su sun kasa zama sai zagaye suke yi, irin su Ɗahira kuwa sun kasa jure wa sai sharan hawaye suke yi.

    Su Abbu na ciki su ne masu duba shi, su kansu hankalin su ya gaza kwanciya, sabida halin da suka ga Kaka ya shiga, sun kasa shawo matsalar sai faman zufa suke yi.
[5/31, 6:58 PM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL.

SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT ????????‍

بسم الله الرحمن الرحيم

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION????

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A✍️*

???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️

????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????

        
????????????????????????????????????????
???????? ???????????????????????????????? ???????? ???????????????????????? ???????? ???????????????? ɗ????????????. ????????????????’???? ????????????????????????.

          NASIHA
   Sallah tana maganin duk cututtukan da suke samun zuciya. Ita ce haske mai kawar da duhu da zunubai. Abu Huraira ya ce, “Na ji Manzon Allah yana cewa:
      “Ku duba nan; idan ɗaya daga cikin ku yana da rafi a bakin ƙofar sa kuma yana wanka cikin sa sau biyar kullum, shin wata ƙazanta tasa za ta yi saura?” Sai suka ce, “Ba wata ƙazantar sa da za tayi saura”. Sai ya ce, “Wannan kamar salloli biyar ɗin nan ne waɗanda da su ne Allah yake wanke zunuban mu”.
       A sallah ne ake ganin tahƙiƙanin daidaituwa da adalci. Lokacin da Ladan ya yi kira da cewa: “ku yi gaggawa zuwa Sallah, ku yi gaggawa zuwa ga falala. Duk waɗanda sallar ta rataya a kansu, masu arziƙi da faƙirai, manya da yara, sarakuna da talakawa – dukan su za su taru a sahu guda ba wani bambanci tsakanin su, dukan su bayin Allah ne. Za su taru a bisa aƙida guda a ɗakin Allah, suna tuna Allah kaɗai, suna tawali’u gare shi.

        EPISODE Twenty Two

      Wajen awanni biyu da shigar da Kaka, kafin su Abbu su fito, sai dai basu ba ma kowa damar ganin sa ba, sabida a time ɗin sun yi masa alluran barci; yana cikin barci, domin ba sa son ayi hayaniya da zai ja har ya farka daga wannan barcin.

     Gaba ɗaya iyalan gidan sun kasa kataɓus a ranan, ko jirgawa sun kasa yi a baƙin ƙofar, sai da su Big Dady suka yi musu magana ne, akan “su tafi gida,” sannan ne su Hajiya suka koma gida, yayinda su Ɗahira kuma suka koma bakin aikin su, but jefi-jefi suna kewayo wa ko Kaka ya farka.

     Har dare be farka ba, haka ilayan Doctor Al’ameen suka kwana a cikin wani hali a wannan ranan, sai washe gari aka samu ya farka, sai dai sosai suka shiga farin ciki a ranan, sabida Kaka ya samu sauƙi tamkar ba shi ba, babu wanda yayi tunanin zai tashi da lafiya haka, sai ga shi har magana yana iya yi, kuma yana iya yin sallan sa, domin tunda ya tashi ya buƙaci a kai sa yayi alwala, sai da ya gabatar da sallolin da ake bin sa, sannan ya samu yaci abinci daƙyar, aka ba shi magani ya sake komawa barci, sakamakon alluran da aka sake mishi, sabida ana son ya sake samun hutu sosai.

   A ranan haka mutane sukai ta zuwa duba sa, gaskiya Kaka na mutane ne, ba ga talakawan ba; ba ga attajiran ba, manyan mutane kama daga ko wani gari duk ana ta zuwa gaishe shi, har mutanen Maiduguri dangin su duk sun zo wasu daga ciki duba sa, su Hajiya Ikram, Hajiya Laila tun a ranan suka shigo Kaduna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button