NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

Yau dai su Aunty Zainab babu wacce tazo cikin su.

………. ………. ………. ………

      Babu jima wa aka soma shigo wa da abincin ana jera wa a dainning table ɗin cikin parlour'n dake can gefe, babba ne me cin a ƙalla mutane ashirin

Bayan an gama an hallara a lokacin ne itama Fadila ta shigo ta zauna cikin su, kowa ya zuba abinda yake so

Ɗahira kuwa tana can cikin Parlour tare da Kaka dake zaune kan Wheel chair ɗin sa, dama haka take yi idan har ba ya son zuwa kan dainning ita take zama kusa dashi tana taya sa hira, idan ta ɗibo masa abinci sai su zauna tana taya sa hira suna ci har su gama

Yau dai shima Baffa ɗauko nashi abincin yayi ya dawo kusa dasu yana ci yana saka musu baki

Haka Familyn suka kasance yau cike da nishaɗi

Bayan kowa yaci ya sha aka dawo parlour aka zauna, nan su Big Dady sukai ta tambayan matsalolin mutane, daga nan kuma Kaka ya soma yabon Ɗahira da ƙoƙarin ta kan aiki, haka su ma su Big Dady sai yaba mata suke yi suna saka mata albarka

Abbu da Aunty Amarya hakan ya saka su farin ciki matuƙa

Hajja Fatu kuwa baƙin ciki kamar ya karta, haka ma Shakira sai dai ko kaɗan basu nuna a fuska ba

Hajiya kam babu ruwan ta duk da itama ba wai yabon yayi mata daɗi bane, Umma ma dai na ciki na ciki

Fuskar Yusra kamar zai fashe saboda baƙin cikin yanda iyayen nasu suke yabon Ɗahira, ko kaɗan ta kasa ɓoye abin da ke zuciyar ta, sai cika take yi tana batse wa babu wanda ya kula da ita

Anan Big Dady yake faɗa musu Usman zai dawo gaba ɗaya gobe, iyayen sun yi farin ciki amma ban da yaran don sun san halin sa ba ya da mutunci bare ɗaukar raini, yanzu zai zo duk ya takura musu

Daga nan aka ci gaba da hira, masu abun yi sun tashi sauran kuma sun zauna

Fadila ce farkon tashi ta koma part ɗin su.

______________

   Ɗahira ce ta shigo cikin ɗakin nasu

Fadila dake waya tabi ta da kallo, sai kuma tayi dariya tana faɗin, “ga ta nan yanzu ta shigo ai”.

Cire wayan tayi a kunne tana kallon Ɗahiran da ta nufi wajen gadon ta tace, “Ga shi za ku gaisa da Yaya K.b”.

Murmushi Ɗahira tayi ta’iso wajen ta’amshi wayan tana kangawa a kunne kafin ta zauna gefen gadon Fadilan

“Yaya na”. Tafaɗa tana dariya

Shima daga can dariyan yayi yana faɗin, “ƴan mata kin ɓuya da yawa fa”.

“Haba ko dai ka ɓuya? Kaji min wannan mutumin”.

Dariya yayi sosai yana faɗin, “Allah Ni ina nan ke ce dai kika ɓuya”.

“Ai dama kai ba ka son laifin ka,
so how are you, how everyone?”

“Alhmadulillah. how about you?”

Ɗahira murmushi tayi tace, “lafiya sumul kamar yanda kuke, ina Shamsiyya?”

“Ai kam yanzu ta tashi anan ta gama min daɗin baki”. K.b yafaɗa yana murmushi

“Hmm kai dai ka faɗa gaskiya ko dai kai ne ka gama mata daɗin bakin? Ai nasan hali”.

K.B said, ” Let me call her and u ask her,”

“A’a Ni bance ba, ka barta nariga dai nasan Shamsiyya baza tayi maka haka ba, ya Ɗan kinibibi ina fatan yana lafiya? Duk da nasan kai dashi baku da zumunci, wai ace anyi Waliman mu amma kuka ƙi zuwa”.

K.b dariya yayi yace, “sorry Madam wlh kin san Ni aiki ne yayi min yawa, idan ma wani zai ƙi zuwa ai Ni bazan ƙi ba tunda har da my dear, amma insha Allahu kwanan nan zan zo Garin ma”.

Taɓe baki Ɗahira tayi tana kallon Fadila da ta shiga Toilet tace, “Mu dai muna zuba idanu; and Kar ka manta da saƙo na don Allah idan zaka zo”.

“Ok insha Allah, ga fa Mutumin naki nan ya shigo in ba shi wayan ne sai ki faɗa masa sunan da kika kira sa dashi?”

Rufe baki Ɗahira tayi cikin waro idanu tace, “don Allah rufa min asiri kar ka haɗa ni dashi”.

K.b me zai yi in ba dariya ba

Ita kuwa Ɗahira wayan ta miƙa ma Fadila da ta dawo ta zauna kan gadon tana faɗin

“Riƙe wayan ki naga Yaya K.B yana son yaja min salalan tsiya”.

Fadila amsar wayan tayi tana maida wa a kunne, sai kuma tayi dariya tana faɗin, “ai har ta fice ma a ɗakin”.

Dariya ta sake yi tana gyara zaman ta, daga nan hiran su suka ci gaba da yi.

    Kabir K.B shi ne ɗa na uku wajen Hajiya IKRAM, ɗiyar ta na farko Sunan ta Nafisa, suna  kiran ta Aunty Mimi, tayi aure har da yara, sai Isma'il, suna ce masa Dady, sannan K.B ɗin, sai kuma Jalil sannan Shamsiyya, sai ƙannin Shamsiyyan guda uku

K.b ke son Fadila har kowa ya rigada ya san da zancen, yanzu kawai lokaci ake jira sanda Kaka zai ce su fito da mazajen aure ayi musu.
[5/25, 10:04 PM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
             FAMILY DOCTORS
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
  NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT ????????‍♀️

بسم الله الرحمن الرحيم

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION????

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A✍️*

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattpad: UmmuDahirah????
        

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

Wannan shafin naku ne masoyana, kuji daɗin ku.❤️

        EPISODE Fifteen

     Fitan Ɗahira ɗakin sai ta wuce ɗakin Maman ta kai tsaye, babu ita ciki tana can General parlour

Kan gadon ta tanufa ta soma kwashe mata kayan wankin ta dake ajiye an ninke, kwashewa tayi ta kai mata sif ta dawo ta soma gyara ɗakin, ba wani datti yayi ba amma haka ta sake gyarawa har da wanke mata Toilet, ta dawo Kan kujera ta zauna ta soma duba wayan ta, message ɗin da Masoyin ta ya turo mata yanzu babu jimawa ta buɗe

“Kyakykyawa ta Barka da hantsi da fatan kina lafiya? Ya Weekend Ina fata kina enjoying?”

Murmushi ta saki, a karo na farko yau tayi tunanin tura masa amsa, sai ta soma typing cikin ƙware wa

_”Alhmadulillah ina fata kaima haka? Please I want to know who?”

Sai tayi sending ɗin shi, tana nan zaune tana jiran ko za’a dawo mata da amsa but babu, sai ta gyara kwanciyar ta tasoma chatting da friends ɗin ta waɗanda sukai school tare

Can kuma sai saƙo ya shigo, da sauri ta buɗe tana murmushi duk farin ciki ya cika ta

“Hmm kyakykyawa ta Kar ki damu da sannu zaki san ko Ni wane ne, Ni dai fata na in samu soyyayyar ki, don Allah ki so ni ko da kaɗan da yanda nake miki”.

Wani irin farin ciki ne yake mamaye da Ɗahira, sai dai bata mayar mishi da amsa ba tunda bata san me zata ce ɗin ba, sai taci gaba da chatting ɗin ta cike da nishaɗi.

           ⚫⚫⚫

   Buɗo ƙofan Hajiya tayi ta shiga parlour'n da sallama

Yusra dake kwance cikin 3 Sitter tana kallo ta’amsa mata

Zuwa tayi ta zauna tana faɗin, “Yusra, get me some water.”

Tashi Yusran tayi ta nufi Fridge tana faɗin, “Hajiya wai don Allah da gaske gobe Yaya zai dawo?”

Hajiya bata amsa mata ba har sanda ta kawo mata ruwan, ta’amsa tasha sannan ta’ajiye sauran kan Centre table tana maida hankalin ta kan t.v

Turo baki Yusra tayi ta zauna gefen ta tana cewa, “Hajiya I am talking to you.”

Sai Hajiya ta kalle ta tana hararan ta tace, “dan ƙaniyar ki Dadyn naki ƙarya zai miki? Ina ce a gaban ki ya faɗa?”

Sake bunso baki gaba tayi tace, “to Ni Hajiya gaskiya bazan zauna ba zan koma gidan Aunty Zainab da zama, don wlh bazan zauna anan kullum ina cikin takura ba”.

Hajiya tace, “to Ni ban aike ki ba, idan kin tambayi Dadyn ki ya yarda sai ki fi ruwa gudu ma”.

“Don Allah Hajiya kiyi masa magana mana wlh bazai yarda ba in Ni ce”.

Hajiya bata sake mata magana ba

Ita kuma sai magiya take mata har da ƴar ƙwallan ta

Ko kaɗan ba ta farin ciki da dawowar Yayan nata, tunda sai tafi kowa takura kasancewar Part ɗin su ɗaya, ko kaɗan idan yana nan ba ya ƙaunar kayi ƙwaƙƙwaran motsi a gidan, yanzu sai ya zama laifi a wajen sa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button