NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

Hannu ta saka ta dafa Wheel chair ɗin sa tana kallon sa, cikin murmushi tace, “to karka damu Kaka, idan ma tsoro kake ji karka mutu baka ga aure na ba ka kwantar da hankalin ka, zan roƙa maka Allah ya barka da ranka har zuwa ranan da zaka ga aure na, me kake ci na baka na zuba Tsoho na?”

Kaka dariya yayi yana jan hancin ta yace, “ja’ira kin ganki”.

dariya tayi itama tana kai hannun ta kan hancin nata

“To ki nuna min shi ko a hoto ne mana”.

Zaro idanu tayi tace, “kaiii Kaka is so expensive, wannan dalilin ya saka na hana sa yin hoto kar ma wata ta mallaki hoton a rashin sani, don shi ɗin yafi ƙarfin ko wace mace idan ba Ni ba, but idan kana son in ɓurɓusa maka wani abu daga cikin labarin sa nima sai ka bani labari me daɗi ta yanda zanji daɗin baka labarin shi”.

“To shikenan yanzu bari in Baki labarin Matata abar alfahari na”.

Murmusawa Ɗahira tayi ta gyara zaman ta da kyau har da buga tagumi tace, “to ina ji bani nasha”.

Sai da yayi dariya kafin yace, “to tashi ki buɗe drowern can ki ɗauko min jakan ciki, ga ɗan mukullin acikin locker”.

Yayi mata nuni da Lockern dressing mirror

Ɗahira da har ta tashi tsaye tanufi wajen ta buɗe ta ɗauko keeys ta kawo masa, shi ya cire mata na drowern ta’amsa taje ta buɗe ta ɗauko masa jakan ta dawo

Zuge jakan yayi hotuna ne da yawa aciki, ya zaro ɗaya daga ciki ya nuna mata

“You see this”.

Amsa tayi tana kallo, shi ne tare da Baby a manne da juna, ga duk kan alamu anyi hoton ne lokacin da ake party, murmusawa tayi tana shafa hoton ta ɗago kai tana kallon sa tace, “Wow Kaka gaskiya kun yi kyau sanda kuke Matasa”.

Murmushi yayi yace, “ke ma kin faɗa ai, mun yi hoton nan ne lokacin da ake Dinnern bikin mu, hmm bazan taɓa manta wannan lokacin ba, Matata har yanzu na kasa manta ta har yanzu kuma ƙaunar ta na nan daram cikin raina batare da ko ɗigo ya fita ba duk da kuwa ba ta a raye, kin san kowa da irin ƙaddaran da Allah yake jarabtan bawan sa dashi, to Ni soyayyarta shine ƙaddara ta, na so ta matuƙa fiye da tunanin mutum, haka zalika taso Ni fiye da tunanin me tunani, Allah Sarki Baby”.

Sai ya saki murmushi yana komar da hawayen idon sa

“I will never forget her in my life. har yanzu zanen halin ta na nan daram cikin raina”.

Murmushi kawai Ɗahira take yi tana kallon Kakan nata, sai da ya dasa aya a maganar nasa sannan tace, “Grandpa tell me about the day you first met her”.

Sai ko Kaka ya saki dariya me sauti, ga duk kan alamu ya tuna wani abu ne, cikin murmusawa yake cewa, , “This is the day I will never forget in my life, ranan da na haɗu da Babyna matata abar ƙauna ta, lokacin da naje Hospital ɗin da nake aiki, a bakin Hospital ɗin na kusa bige ta da motata, hakan ya saka ta tsorata har ta faɗi taji ciwo a hannu sannan kuma nayi mata asaran shinkafan da take siyarwa”.

Ƙwalalo idanu Ɗahira tayi tace, “Kaakaa Talla?”

Dariya yayi yace, “eh Talla, ai talla naga take yi lokacin da muka fara haɗuwa, Hmm my Baby taga rayuwa duk da kasancewar ta ƴar gata don mahaifin ta me kuɗin gaske ne..”

“To amma Kaka ya akayi ta koma yin talla?” Ɗahira ta katse sa da tambayan nan

“Ƙaddara, ko ince canjin rayuwa”.

“To Kaka ya kuka ƙare da ita kuma wani kalma ta soma shiga tsakanin ku? And kuma lokacin ne ka soma sonta?” ta sake tambayan sa cike da zumuɗi da son jin labarin

Murmushi Kaka yayi yana lumshe idanun sa, sai ya buɗe a kanta yace, “kalman da ta soma fitowa a baki na shine haƙuri na bata, sannan ne ta ɗago ta kalle ni, tabbas kallon farko da nayi mata na kamu da matsananciyar ƙaunar ta, kuma sai na nemi alfarman tabi ni inyi mata dressing hannun, da farko bata da ninyan bi na but mutanen da suka taru wajen ne suka saka ta taje, kalman da na soma ji a bakin ta har ta tafi sunan ta kaɗai ta faɗa min”.

“Kaka kasan me?”

Girgiza mata kai yayi yana kallon ta

Murmushi tayi da ya bayyana ƙananun haƙoran ta tace, “abinda yake bani mamaki da burgewa yanda ka auri Mata har uku masu suna ɗaya, ko a Film da littafai ban taɓa ganin hakan ba, kuma har kayi rayuwa dasu alokaci ɗaya”.

Shima murmushin yayi yace, “Allah kenan shi ya ƙaddara hakan, gashi ke kuma kin zo a ta huɗu”.

She laughed and said, “Show me the other pictures, ka ga har yanzu bansan sauran matan naka ba ko a hoto ka ƙi ka nuna mana, wancan ƴar uwan taka da tayi aure a ƙauye kawai nasan zan iya tunawa, tunda nasan ta muna yara kafin ta rasu”.

Jakan ya buɗe ya kuma zaro wani hoton ya miƙa mata

Hoton ta’amsa tana kallon matashiyar da aƙalla zata kai shekara 19 zuwa 20, fara ce sol kyakykyawar bafulatana, da sauri Ɗahira ta ɗago kai tana kallon Kaka tace, “Laa Kaka wlh wannan sak Big Dady, ba su da maraba kamar tayi kaki ta ajiye”.

Murmushi yayi yace, “Matata ta farko kenan UMMEE NAFEESA, Mace ƴar aljanna me tsananin haƙuri, dattako da sanin ya kamata, bazan iya fasalta miki kyawawan halayyan ta ba, wannan hoton anyi sa ne gab da zata rasu, Ni na ɗauke ta a waya shine na ba da aka wanko min, Allah Sarki ta rasu da ƙuruciyarta, ta rasu lokacin da nake matuƙar buƙatar ta, ta rasu sanda ta gama naƙudan Noor (Big Dady) batare da ta ganshi ba ta koma ga Allah. Allah ya jiƙan ki da rahma Ummeeta”. Kaka ya ƙarike maganar tasa yana share hawaye

Itama Ɗahira har sai da tayi nata hawayen sabida tausayi sannan tace, “ameen Kaka, may Allah have mercy on them all”.

Amsan hoton yayi ya maida a jaka, yana shirin rufewa Ɗahira ta saka hannu ta zaro wasu hotunan biyu tana cewa, “Kaka ka bari mana ka gama min bayani, wannan kuma yaron me tsananin kama da kai wanene?”

Ta nuna masa hoton ɗan ƙaramin yaro dake wasa da kayan wasan da aka zube masa da yawa a gaban sa

“Yarona na farko kenan sunan sa Arif, Sunan Kakana yaci Khabeer, amma tun yana ƙarami ya rasu”.

Ɗahira tace, “laa Kaka ashe ban da Big Dady dama kayi wani yaron? Wacece maman shi?”

Hoton hannun ta ya nuna mata

“Ga Maman shi nan cikin hoton nan”.

Shafa hoton Ɗahira tayi da hannun ta tana murmushi, hoton KAKA ne da Ƙannin sa biyu Baseera da Ihsan sai kuma Nafeesa mahaifiyar Arif”.

“Kaka kuna tsananin kama sosai duk kan ku kowa ya gan ku ya san ƴan uwan juna ne”.

Murmushi kaɗai yayi ya miƙa hannu ya’amsa hoton sannan yace, “kawo in mayar zanyi sallah”.

“So what about the story Kaka?”

“Ki bari duk sanda na sami lokaci zan tara ku gaba ɗaya in baku cikakken labarin aurena dasu”.

“Yauwa Kakus ɗin mu, Allah yakai mu to”.

Bayan ya zuba hotunan ya bata jakan ta mayar, ita ta tura sa har Toilet ta zuba masa ruwa yayi alwala sannan ta tafi part ɗin su bayan ta bar sa nan cikin ɗaki yana Sallah.

      Tana zuwa Parlour'n su da Fadil taci karo yayi ɗai-ɗai yana kallo

“Yauwa Aunty Ɗahira kin bar wayan ki ana ta kira”.

Bata ce komi ba ta wuce cikin ɗakin nasu, ƙarar zuban ruwa tajiyo a Toilet ta san Fadila ce, zama tayi ta ɗau wayan tana duba missed calls ɗin da akayi mata, Baffa ne ya kira ta, itama kiran sa tayi but be ɗauka ba, sai ta’ajiye wayan ta ɗau Novel ɗin da take karantawa JARUMAI ta gyara zamanta ta soma karanta wa kafin Fadila ta fito daga Toilet tayi alwala.
[5/23, 4:03 PM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
             FAMILY DOCTORS
                         ????
????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button