NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

            ⚫⚫⚫

     Baffa kuwa sosai ya shiga damuwa a wannan ranan, har kuka sai da ya sha ya ƙoshi, ya kuma gode wa Allah, ga shi yana ji yana gani zai bar zaɓin shi babu yanda ya iya, yana kallon wacce yake ƙauna bata da wanda zata iya gabatar wa face shi, amma kuma Mahaifiyar shi tayi masa iyaka da ita.

      Ya tuna sanda ya je har ɗakin ta yana kuka ya sake mata maganar “ta amince ya auri Ɗahira, in yaso duk wacce take so ya aura, shi wlh zai aure ta, koda kuwa mata huɗu zata haɗa masa, idan har da Ɗahira to ya amince”.

Amma sai buɗan bakin Hajja tace, “kai Al’ameen ka ji Ni da kyau, Ni Ɗahiran ce ba na so ka aura, bazan taɓa haɗa tsatso da A’ishah ba, domin kuwa na tsane ta a raina, ban taɓa faɗa maka hakan ba, amma yanzu sabida maganar nan ka saka ina bayyana maka sirrin dake raina, to wlh idan har ka kuma sake tayar da maganar nan ma, ban yafe maka ba”.

Kuka sosai Baffa ya fashe da shi, be iya furta komi ba sabida tsaban tashin hankali, wai yau Mahaifiyar sa ce take furta masa kalmar nan duk a sabida wani dalili nata mara tushe, ko a mafarki be taɓa tunanin akwai abinda zai iya bayyana wa mahaifiyar sa yana so ba, ta kasa mishi, sabida ya san tana ƙaunar sa, duk abinda yake so to itama tana so, hakan be taɓa faruwa ba, shiyasa yake ganin abun tamkar almara. ranan ya sha kuka kamar babu gobe, har zazzaɓi ya kwana da shi a ranan. Allah ya ɗaura masa ƙaunar Ɗahira kamar ransa, amma ga shi a lokaci ɗaya ya rasa ta, abinda be taɓa tunani ba ko da a mafarki, ya rigada ya saka wa ransa ita ɗin tashi ce, tunda be taɓa tunanin akwai wata matsalar da zai shiga tsakani ba, ko da ma akwai, to, sai dai a wajen Ɗahira, ita ma kuma be taɓa tunanin zata iya cewa ba ta son sa ba, tunda ya san girman son da take mishi, ya san Ɗahira a kansa zata iya yin komi sabida farin cikin sa, shaƙuwar su ya wuce misali, babu ɓoye-ɓoye a tsakanin su.
[6/5, 9:22 PM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL.

SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT????????‍

بسم الله الرحمن الرحيم

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION????

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A✍️*

???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️

????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????

        
????????????????????????????????????????
???????? ???????????????????????????????? ???????? ???????????????????????? ???????? ???????????????? ɗ????????????. ????????????????’???? ????????????????????????.

        EPISODE Twenty Seven

     “Dakata da Allah Ayush! Wani taimako kike so in miki ban da wanda nayi miki? Kin tambaye Ni Numban sa na baki wannan kuma ya rage naki, in yaso ki je ki same shi da soyayyar ki, in kuma kin kasa Wannan kuma damuwar ki ne, amma kar ki ƙara zuwa min da banzan maganar nan taki akan Ni ce zan sanar mishi, ina ruwana a ciki?” Shakira take maganar cikin fusata

Ayush dake zaune a gaban table ɗin ta, idanun ta sun cika da ƙwalla, hannu ta saka ta share tana kallon ta tace, “fine naji, sabida na gama miki amfani shiyasa kike son watsa min ƙasa a ido, don kawai na nemi taimakon ki akan nawa soyayyar? Babu damuwa”. Ta ƙarishe maganar tana miƙe wa zata bar Office ɗin

Da tsaki Shakira ta raka ta, bata ce komi ba ta mayar da hankalin ta kan wayan ta, sai yanzu ma take dana sanin amince wa tayi ƙawance da local irin wannan, don da farko a tunanin ta ƴar masu kuɗi ne irin su, shiyasa tayi saurin amince mata, amma yanzu gaba ɗaya dana-sanin yin ƙawance take yi da ita, ta bar ta ne kawai saboda tana mata aiki a kan Baffa da Ɗahira, amma kuma yanzu tunda komi ya ƙare a tsakanin su baza ta iya juran raini wajen ta ba…

Tsakin ta kuma ja cike da takaici.

                 ⚫⚫⚫

    Ayush kuma na fita ta tsaya bakin ƙofar ta gama share hawayen ta, a fili ta furta, “wlh wlh sai kin yi nadamar sani na a duniya Shakira, yanda ban yi farin ciki ba kema baza ki taɓa yi ba, idan har kin ga kin samu kwanciyar hankali wajen mijin da zaki aura, to, tabbas nima na samu abinda nake so ne, amma mu zuba dani dake, ba a Shana a zauna lafiya”.
Tana gama faɗar hakan tayi hanyar Lefter don zuwa office ɗin Usman, so take yi yau ayi ta ta ƙare, baza ta iya barin soyayyar sa a zuciyarta ba, tana shan wahala ko da yaushe be ma san tana yi ba, dole yau zata bayyana mishi soyayyar ta, ko da zata samu sukunin zuciya, ga shi duk shawaran da Rumanatu take ba ta be yin tasiri, ita kuma Safra da tace zata taimake ta har yanzu bata sake jin ta ba, ko a waya ma Numban ta ya dena shiga, wannan dalilin ne yasa ta nemi taimakon Shakira, Amma kuma ta watsa mata ƙasa a ido, ita a ganin ta Shakira tana da hanyar da zata taimake ta domin mallakar Usman, shiyasa kai tsaye ta je da ƙoƙon baran ta..

     Sanda ta isa bakin Office ɗin, tsaya wa tayi tana gyara zaman Labcoat ɗin ta, sai da ta gyara fuskar ta sannan tayi Nocking, sai dai babu answer, haka ta sake yin wani, sai da ta ɓata time a wajen kafin ya ba ta iznin shigo wa, buɗe ƙofan tayi ta shiga

Yana zaune ne kansa a saman table, ga duk kan alamu barci ne ya so ɗaukar sa sai yaji Nocking ɗin ta, amma kuma duk da haka be ɗago ba yana jiran yaji abinda ke tafe da ko ma wane ne

Ɗan numfashi taja kana cikin ƙarfin hali tace, “Doctor wajen ka na zo, can I sit?”

Sai a time ɗin ya ɗago kansa ya bi ta da kallo, ganin ta da Labcoat ya tabbatar masa da itama ma’aikaciya ce a Hospital ɗin, sai dai be iya ce mata komi ba illa sake haɗe rai da yayi yana kau da kansa daga kallon ta, tare da gyara zaman sa yana jingina bayan sa kan kujeran, har da ɗaga kansa sama yayi ya sake mayar da idanun sa ya rufe ruf

Ayush dai na tsaye tana kallon sa, sosai take jinjina halin miskilanci irin na bawan Allan nan, tabbas idan har ji da kai ne da taƙama, gami da izza, idan har ka zo wajen sa to ka gama samu, ko kai uban waye ne sai ya nuna maka wannan halin nasa, abun a jinin sa yake, sai dai in ka zage sa amma dole ne sai ka kwashi haushi a zaman ka da shi

Sai da ta ɗan ja wasu sakwanni tana tsaye ko zata ji yayi mata iznin zama kamar yanda ta buƙata, amma be ce komi ba, kuma ga duk kan alamu ba shi da ninyan cewa ɗin, don haka ta ja ƙafafun ta ta nemi wuri ta zauna jiki a sanyaye, shiru tayi don bata san ta ina zata fara ba, a tunanin ta abinda ta ɗauka ɗin sauƙi ne da shi, amma kuma sai da ta bayyana gaban sa ta gane hakan ba me yiwuwa bane ta sauƙi a gare ta, tabbas kwarjinin sa da tsantsan cika idanun sa bazai bar ta ta samu sukuni har ta faɗi abinda take so ba. haka ta shafe tsawon mintoci tana zaune ta kasa yanda za’a yi ta sanar masa da abinda ke ranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button