NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

        EPISODE Twenty Six

             SUNDAY
        Gaba ɗaya sun taru a General Parlour kamar yanda al’adan gidan yake, sai da suka gama raha da nishaɗin su, sannan Kaka ya soma magana da cewa, “Kai Fadil ki rawo Fodio tunda ya ƙi zuwa”.

“To Kaka”. Fadil ya amsa mishi da sauri yana tashi ya fita

Babu jima wa sai ga Fadil ya dawo, ya isar da saƙon zuwan Usman

Kamar mintuna biyar da shigowar sa ne, Usman ya shigo yana ciccin magani, fuskar nan ko alamun fara’a babu, babu wanda yayi masa magana sai Big Dady dake faman hararan sa, sai dai shi ɗin be ma san yana yi ba, tunda be kalli kowa ba, ya samu wuri ya zauna gefen Baffa, sannan ya gaishe su yana latsa wayan sa

Kowa ya amsa, banda Big Dady da hakan ya ƙular da shi, a fusace ya ce, “kai Usman wannan wani irin ɗabi’ar banza ce? Ina ce gaishe mu kake yi amma kanka a waya?”

Sai a lokacin Usman ya ɗago kansa, sai dai be ce komi ba, illa jikin sa da yayi sanyi ya zame hannayen sa daga wayan ya bar sa a saman cinyan sa

Zai sake magana Big Dady, sai Kaka ya tare shi da faɗin, “bar wannan maganar Noor, mu Yi abunda ya tara mu, kasan halin wannan yaron meyasa kake son ɗaukan zafi da shi ne?”

“Baba wlh abun Usman sake gaba yake yi ba baya ba, kamar shi har sai an zauna ana faɗa mishi dai-dai da wanda ba dai-dai ba? Nan ya bar mu muna zaman jiran sa tsawon lokaci, duk sabida shi aka ƙi cewa komi, amma kuma ya zo yana wani sabga daban bayan yasan da cewa magana me muhimmanci ne ya tara mu”.

“Well enough to stop talking, ban san ka da wannan halin ba Noor Kar ka soma ka ji ko?” Kaka ya sake faɗa idanun sa kan Big Dady

Gyaɗa kansa yayi, kana yace, “to Baba Allah ya huci zuciyar ka”.

Murmushi Kaka yayi, yayinda su Abba da Abbu suka amsa da “Ameen, sai haƙuri ai”.

Kaka ya ce, “to ina jin ku, ya muka kwana a maganar yaran nan ne? tunda yau dama na ce zamu sake zama akan maganar”.

Abba ne ya ce, “ai Baba duk na tambaye su kuma na ce su turo mun su, kuma sun zo mun yi musu tambayoyi da Yaya (Yana nufin Big Dady) sannan na bincika duk na gano inda yaran suke, har na saka ayi min bincike a kansu. Uwata kuma da Usman har yanzu ba su ce komi ba akan maganar, shi kuma Baffa ɗazu Mahaifiyar tashi take faɗa min Sa’adatu ta wurin ƙanwar ta Hajiya Amina yake so”.

Kaka yace, “to Masha Allah Baba na”. Sai ya mayar da kallon sa ga Ɗahira da ke gefen sa ya ce, “Matata har yanzu abokin takaran nawa be shirya bane da baki gabatar da shi wajen Iyayen naki ba?”

Shiru Ɗahira tayi kanta a ƙasa

Sai da Big Dady yace, “Daughter you’re talking, are you okay? No problem?”

Bata ɗago kai ba tace, “Daddy, I don’t have anyone to introduce me to.”

“Baki da wanda zaki gabatar kuma?” Cewar Big Dady da Abba da suka haɗa maganar a tare

Sai kuma Big Dady ya ƙara da faɗin, “ko dai kin tsaya ruwan ido my Daughter? Amma maganar babu wanda zaki gabatar ai be taso ba”.

Jikin ta a sanyaye tace ,”Daddy wlh da gaske nake yi, wanda muke soyyayya da shi ya ce “ya fasa aure na, sabida Mahaifiyar sa ta zaɓa mishi wacce zai aura”.

Daga Aunty Amarya har Abbu da su Big Dady sai da jikin su yayi sanyi, haka zalika Kaka da yayi zugum yana kallon ta ya kasa furta komi

“Yanzu Uwata babu kuma wanda zaki iya gabatar wa ne?” Cewar Abba da yayi maganar a sanyaye

Gyaɗa kanta tayi, don haka kawai taji hawaye ya cika mata ido, a ganin ta abun da kunya a tara su a gaban jama’an gidan ace ta kawo zaɓin ta, amma kuma bata da shi, babu wanda zata iya nuna wa a matsayin gwanin ta, kamar ta ƙatuwar budurwa da ita, a ƙalla yanzu kaɗan ya rage ta cika 26 cif-cif…

Muryan Kaka ya katse mata tunanin ta, sai ta saka hannu tana share hawayen da ya zubo mata tana ci gaba da sauraron shi

Tambayan Usman yayi kamar yanda yayi mata

Usman ɗago kai yayi yana kallon kakan, fuska babu walwala a daƙile ya ce, “Babu”.

“Meye kuma Babu?” Abba ya tambaye sa

“I mean har yanzu babu wacce nake so”.

Shiru gaba ɗaya parlour’n ya ɗauka, ana jiran aji wani yayi magana a kan hakan, amma babu wanda ya iya cewa komi, har Kaka kuwa, kowa juya maganar nasa yake yi a mizanin hankalin sa

Kaka kallon Abbu yayi ya ce, “Takwara kun yi maganar da Yayar taku?” (Hajiya Ikram, Yana nufin akan Khabeer da ke son Fadila)

“Eh Baba, Yaya yayi maganar da ita”.

Big Dady yace, “mun yi maganar, har mun tattauna da mijin ta, babu matsala tunda su ma a shirye suke, za’a haɗa gaba ɗaya dana Isma’il da Shamsiyya”. (Sauran yaran Hajiya Ikram, su uku kenan zata aurar itama, har da K.B)

Gyaɗa kansa Kaka yayi yace, “Masha Allah gaskiya nayi farin ciki matuƙa, Allah ya sanya albarka gaba ɗaya”.

“Ameen ameen”. Suka amsa gaba ɗaya

“Yanzu duk abinda kuka ga ya dace sai ayi, kun san dai idan za’a saka ranan nace muku kar ya wuce wata ɗaya? Sai ayi komi a tsanake zuwa watanni biyu, na ƙara lokaci, a lokacin idan Fodio da Matata sun kawo nasu sai a haɗa baki ɗaya, don baza ayi babu su ba. Kai kuma Fodio kayi ƙoƙarin samo mata tun kafin Ni in zaɓa maka kana ji ko?” Kaka yayi maganar ta sigan barkwanci

Be ce komi ba kamar yanda kuwa babu wanda yayi tunanin zai ce.

     Daga nan dai aka bar zancen aka kama wani, inda waɗanda suke da abun yi suka bar wajen.

    Ɗahira bata wani tada hankalin ta ba akan maganar, ta bar wa Allah zaɓi, a ganin ta idan ta saka damuwa kanta zata cuta, tunda dama bata iya saka damuwa a ranta ba, da zaran ta saka, to shikenan ta dinga ciwo kenan, duk idan ka ga tana ciwo to tabbas da akwai abinda ke damun ta ne, ba ta iya jure wa damuwa ko kaɗan a ranta, bata da dauriyan hakan, domin zuciyar ta ba ta iya ɗauka, shiyasa ba ta shiga sabgar kowa idan har be shafe ta ba, sabida ta san matsalar kanta.

      Aunty Amarya har ɗaki ta kira ta, tayi mata nasiha akan hakan

Amma sai Ɗahira ta nuna mata babu komi, har da fara’an ta

Hakan ya kwantar wa da Aunty Amarya hankali matuƙa, ko babu komi taji daɗi a yanzu, tunda ta san dole ɗiyar ta zata shiga wani hali na rashin masoyi, tabbas rashin Masoyi abu ne me ciwo ga duk macen da ta isa aure amma babu ma nemi, sai dai Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi.

          ⚫⚫⚫

     Fannin Usman ma, da dare Daddy ya Kira sa ya titsiye sa akan maganar, a cewar sa “ai wannan shirmen banza ne, shirmen hofi. Ta ya zai ce be da wacce yake so duk girman sa, shekara kusan 33 yana musu wasa da hankali”. Tsiya-tsiya sosai Big Dady yayi masa, kuma ya ba shi umarnin “lallai-lallai ya kawo mata zuwa nan da lokacin da Kaka ya ce, idan ba haka ba, zai ɗau mummunan mataki a kansa”

Hajiya na zaune tana jin su, sai dai bata ce komi ba, tunda itama ai tana ƙaunar ganin ɗan nata yayi aure, shi ne babban ɗa a gidan, amma har yanzu be yi aure ba, duk da a ganin ta ai ba wani shekaru ne masu yawa da shi ba, amma ta yanda za’a ganshi da girma, ƙannin sa su ƙara ganin girman sa, ai sai idan yana da mata, itama zata so ta ga jikokin ta ta wajen shi, ai abun kunya ne ma ace yanzu Yusra zata yi aure shi be yi ba, sannan ga ɗaya ƙanwar sa can a ɗakin miji har da ɗan ta, shi ƙaton banza ya zauna.

     Shi kuwa Usman ko a jikin sa, tunda a ganin sa dai babu wanda ya isa yayi masa auren dole, don haka be tashi yin aure ba yanzu sai sanda yayi niyya, duk a cikin mata har yanzu be ga wacce tayi dai-dai da ra’ayin sa ba, yana da burin ra’ayin auren mace zaɓin shi da koda yaushe zuciyar sa take raya masa, kuma har yanzu be dace da kalan ta ba, don haka sai sanda ya same ta sannan ne zai yi aure, mata yanzu ba sa gaban sa, shiyasa ya ɗauki maganar Kaka ba ta da wata muhimmanci, bare shi rayuwan boko ya saka wa kansa, har yanzu gani yake yi be kai matakin da har zai iya ajiye mata ba, ɗawainiya ya hau kansa tun da ƙuruciyar sa ya tsufa da wuri.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button