NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT ????????‍

بسم الله الرحمن الرحيم

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION????

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A✍️*

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

        
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

        EPISODE 29 & 30

         Idanu Ɗahira ta zuba mata tana jiran taji me zata faɗa

Fadila tace, “na lura a gidan nan Hajja ba ta ƙaunar ki, kuma ba ita kaɗai ba har ta da Shakira, domin tasha sanar dani abu game dake domin ta haɗa mu faɗa, ban taɓa biye mata ba, sabida narigada nasan abinda ke cikin ranta. A kwanaki biyu da suka wuce na ji su suna zancen ki, maganar rashin samun tsayayye ne da baki dashi, suna faɗin hakan yayi musu daɗi, har suna cewa Allah yasa ma ki dauwama a haka baza ki taɓa aure ba, sannan Hajja take cewa koda ma kin samu, ita tayi alƙawari baza ta taɓa barin ki ki zauna da mijin ki lafiya ba, duk yanda za’a yi sai tayi don raba ki da Mijin, sai ta mayar dake ƙaramar bazawara idan kin yi aure, idan kuma baki yi ba, zata bi duk hanyan da taga zata iya wajen hana ki aure”.

Tun soma maganar nata Ɗahira take tsiyayar hawaye, sosai zuciyar ta ke suya da zancen nan, “wai dama tsanar da Hajja take mata har ya kai haka ne?”

Bata san cewa a fili tayi tambayar ba, sai jin muryan Fadila tayi tana cewa, “yafi haka ma, baza ki san haka ba sai nan gaba kaɗan idan kin san wani sirrin. Sister Ni abinda nake roƙon ki dashi har na sanar miki da zancen nan, saboda ki san maƙiyan ki ne, ki san yanda zaki zauna da su, sannan ki san hanyar da zaki ɓullo wa al’amarin, ki riƙe addu’a domin baki san ta ina za su biyo miki ba, don Allah ina sake roƙon ki, duk wanda zaki aura Sister, ki kasance me mishi biyayya, ki zauna da mijin ki lafiya ko don ki ba ma Maƙiya kunya, Ni ƙanwar ki ce, but I beg you by God, ki tuna magana ta ko bayan ba na nan”.

Sosai a wannan lokacin Ɗahira take hawaye, har da shashsheƙan kuka

Itama Fadila tuni nata hawayen sun zubo, cikin rawan murya tace, “”I miss you Sister, please .. please ki nemi kariyan Allah domin ki guje wa afkuwar wani abu, ba na son wani abu ya same ki ta silan maƙiya..”

“Keee Fadila meye haka? Me kuke yi haka? Kukan meye?” Ƙanwar Umma da suke kiran ta Inna Sailuba take faɗar hakan, shigowar da tayi

A tare suka bi ta da kallo, sai dai babu wanda ya tanka mata, illa ƙoƙarin share hawayen da suke yi

Tsaki taja tana bin su da kallo itama tace, “tashi dalla kin zauna ta saka ki gaba tana kukan muna-furci, idan ba ta son rabuwa dake ne itama tayi auren mana, in ba hassada kuma take miki ba. Ki tashi nace ga Naja’atu can ta dawo ku je gidan me lallin”.

Kamar yanda basu ce mata komi ba ɗazu ɗin, haka yanzu ma babu wanda ya tanka mata, sai dai Fadila ta miƙe tsaye ta wuce zuwa waje. Itama Inna Sailuba ɗin sai bin bayan ta tayi tana sababi har da kumfan baki, “wai Fadila ta raina ta, tana faɗa mata gaskiya amma Ɗahira ta fi ta a wajen ta”. Duk da kuwa tasan cewa halin Fadilan ce ƙyaliya da Miskilanci. Kankace me sauran jama’an da ke zaune a Parlour sun amshe zancen, nan suka soma aibata Ɗahira da ita da uwar ta tunda sun san ba ta nan, suna me zagin su da yin musu gori akan Ɗahiran.

      Lumshe idanu Ɗahira tayi tana me sake jin zafi sosai a ranta, sosai take kukan zuci babu me rarrashin ta. Ganin baƙin cikin su zai iya kashe ta, sabida ita bata saba jure irin waɗannan ƙananun maganganun ba, sosai suke damun ta a zuciya, sai damuwar kuma ya haifar mata da ciwo, shiyasa ta tashi tafito ta nufi cikin gidan, kasancewar yamma ta soma shiyasa babu wasu mutane sosai a waje, ta inda tasan ma baza ta same su ɗin ba ta nan tabi ta wuce sashin Hajja

Akwai mutane sosai a parlour’n suna zazzaune suna aiki, kasancewar parlour’n akwai duhun magriba har ta wuce ɗakin Baffa babu wanda ya kula da ita, bare ma a shaida ta, bare kuma gidan biki kowa sha’anin gaban sa yake yi.

      Keey ta saka ta buɗe ƙofan bayan ta taɓa taji a rufe yake, ta tura ta shiga sannan ta mayar ta rufe, Direct Kan gadon sa ta nufa ta faɗa ta soma rusa kuka, kawai so take yi ta fitar da duk wani ƙuncin da ke damun ta, domin kuwa muddin bata fitar ba, dole ne tayi ciwo. Sosai tayi kukan babu me rarrashin ta, sai da ta gama ta miƙe zaune ta buga tagumi tana me ci gaba da tunanin zuci

“Ita bata ga makusa a jikin ta ba, duk inda mace me ji da class, me ji da kyawu da tsafta, gami da ilmi ta kai, to meyasa har yanzu ta rasa masoya? Meyasaka har yanzu ta rasa wanda zai ce mata zai aure ta? Ta san tana da farin jinin jama’a, kama daga mazan har matan, babu wanda ba ta harka da su, amma kuma babu wanda ya taɓa buɗe baki yace mata ya zo gare ta ne don soyayya, wanda kuma zai kai su ga aure, sai dai su zo a matsayin tana burge su, tunda tana burge su why baza su sanar mata suna ƙaunar ta ba? Ko kuma dama tana da makusa ne wanda be dace ta samu mijin aure ba?”

Runtse idanuwan ta tayi hawaye na sake silalo mata, cikin muryan ta da ya dishe sosai sabida kukan da tasha tace, “Allah gani gare ka, kai kace a roƙe ka zaka amsa, har yanzu bazan gajiya ba, kuma na san cewa kana ji na. Allah ka zaɓa min abinda yafi alkhairi a rayuwa ta, idan har auren nan ne alkhairi a gare Ni, ya Allah ka zaɓa min miji na gari, idan kuma babu alkhairi a tare da Ni, ya Allah zan rayu ina me gode maka, saboda haka ka tsara min rayuwa ta. Zaɓin ka kaɗai nake nema ya Allah, a duk sanda kaso ikon ka a kaina, a lokacin Ni kuma zan amsa ina me godiya a gare ka ya Allah, Allah na tuba ka yafe min”. Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan

Ta jima tana yi kafin ta tsakaita tana me miƙe wa, sai hannun ta ya bigi drowan gadon wani abu ya faɗo, kasancewar ɗakin da duhu sai ta saka hannu zata laluba, hakan yasa ta kama wayan da tayar hannun ta na latsa wa a rashin sani, take a nan hasken ta ta kawo

Ƴar ƙaramar waya ce Nokia, wayan tabi da kallo, kamar ta ajiye sai kuma zuciyar ta ta bata umarnin latsa wa, take a nan ta danna ta ta cire ta a keey, nan ya bayyana wajen Text message, kasancewar daga wajen ne ba’a fita ba ta shiga keey

Rawa jikin ta ya soma saboda ganin text ɗin da ake turo mata, take ta koma ta zauna tana ci gaba da karanta wa, tabbas gaba ɗaya text ɗin da ake turo mata ne anan

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un… Kar dai ace Ya Baffa shi ne Masoyin ta na ɓoye?” Tayi maganar a fili tana ɗaura hannun ta ɗaya dake rawa a baki

“Ya Allah…” Ta sake faɗa tana kai idanun ta dake tsiyayar da hawaye kan wayan, ci gaba da karanta text ɗin tayi, sai kuma ta koma ta shiga ta duba Numban, take a nan taga Numban nata ne

Lumshe idanu tayi tana jin wani irin raɗaɗi a ranta, babu abinda ya faɗo mata a rai sai text ɗin sa na ƙarshe

“Hajja..!” Ta furta a laɓɓan ta tana me buɗe idanun ta

“Why Hajja? Me nayi miki? Dama ke ce kika hana Ni aure a wannan gaɓar? Ke kika raba ni da Masoyi na na haƙiƙa? Me nayi miki da zafi haka?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button