NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

sai da yaja lokaci a zaune a wajen be yi abinda ya kawo sa ba kafin daga bisani daƙyar ya buɗe baki yace,”I’m leaving”.

Kallon sa tayi batare da ta gane me yake nufi ba

hakan ya saka ya kawar da kai yana ɗan motsa bakin sa

“Ina zaka je?” Ta tambaye sa don ita bata gane inda za shi ba

In a calm and proud voice he said, “Turkey”.

Hajiya tace, “kamar ya zaka koma kai da kace sai kayi kwana biyu?”

Shiru yayi

“Are you talking quietly?”

“I have a job there.”

Shiru tayi tana kallon sa, shi kuwa ya kau da kai don be san ma su haɗa idanu

“Shikenan amma ka bari sai gobe sai ka tafi, yau dai ka haƙura”.

Be ce komi ba ya miƙe ya nufi ɗakin sa, yayinda ita kuma taraka sa da kallo tana mamakin irin halin sa

Shi kuwa yana shiga keey ɗin mota ya ɗauka ya fito ya zo ya wuce Hajiya still tana bin sa da kallo

parcking space ya nufa ya ɗau motar sa ya bar gidan.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

        WASHE GARI

     Wajen ƙarfe 05:30pm. Na yamma Ɗahira na zaune saman gadon ta tana karatun Novel *(JARUMAI na Jikar Lawal Goma).*

Fadil ne ya shigo ɗakin kamar an hankaɗo shi ko sallama, wajen ta ya nufa yana dariya yace, “Aunty, are you still here?”

Kallon sa kawai take yi batare da ta furta komi ba

sai ya sake sakin dariya yana cewa, “Yaya Usman ne ya bani saƙo in baki shi ne naje ɗakin Kaka neman ki ashe kina nan kina faman karatun Novel, Wai me kuke karantawa aciki ne?” Yaƙarike maganar yana kai hannun sa kan littafin

Buge hannun sa tayi tana hararan sa tace, “kai ba na son iskanci; Yi abun da ya kawo ka ka ware”.

Miƙa mata Leda yayi tare da wayan ta da aka farfasa yace, “ga kwaraɓaɓɓiyan wayan ki inji Kaka”.

Bata ce komi ba ta’amsa tana ajiye wa taci gaba da karatun ta

shi kuma Fadil tsayawa yayi yaƙi tafiya yana kallon ta

Ɗago kyawawan idanuwan ta tayi ta maida kansa, “What’s stopping me?”

“Aunty Ɗahira ki bani wannan wayan mana tunda kin ga kin samu wata”.

“What are you talking about now?”  Ɗahira ta tambaye sa still tana kallon sa

Ɗan turo baki yayi yace, “ai gaskiya na faɗa ba kwaraɓaɓɓiyan ba ce?”

Hannu tasa da ninyan riƙo sa yayi saurin matsawa ya nufi ƙofa yana mata dariya

“Idan na kama ka Fadil..” Sai tayi shiru tana ƙwafa sannan taci gaba da karatun ta

Fadil yace, “to inzo in amsa Aunty?”

Bata kula sa ba Amma kuma sosai ya’ishe ta; don ita ba ta son hayaniya da yawan surutu, shi kuma Fadil ya san ba ta so shiyasaka yaƙi tafiya sai magana yake mata yana son ya ƙule ta, ko kuma taji haushi ta ba shi wayan ya tafi, sai da ya gaji don kan shi sannan ya fice batare da ta sake kula sa ba

Yana fita ta’ajiye Littafin don tunda ya fara surutun sa ta dena fahimtar Book ɗin, ledan ta buɗe ta ciro wayan dake cikin kwali, sai da ta gama jujjuya ta ahaka kafin ta taɓe baki tana buɗe wayan, the same irin wayan ta ne, Simcard ɗin ta ta cire ta saka a ciki sannan ta kunna tare da gyara zaman ta tana murmushi ta soma latsa wayan.

Plz kuyi
Vote and shared
[5/23, 8:53 AM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTORS
????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT????????‍

بسم الله الرحمن الرحيم

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION????

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A✍️*

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattpad: UmmuDahirah????

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

Wannan shafin naku ne My Fans kuji daɗin ku, Allah yabar ƙauna.

 *EPISODE Eight*


       *MONDAY*

    Ɗahira ce tsaye gaban mirror ta buɗe locker ta ɗau ɗan siririn glass ɗin ta tasanya a idanuwan ta sannan ta juya ta ɗau jakan ta ta fice, Direct ɗakin Maman ta ta nufa, tana shiga ita kuma tana fitowa daga Toilet

Kallon ta tayi tace, “Ke har yanzu ashe baki tafi ba?”

Ɗahira tace, “Eh Mama ban gama shiryawa bane yanzu zan tafi”.

Aunty Amarya tace, “to ki kula sosai abinda ya kai ki shi za kiyi, Allah ya tsare”.

Murmushi Ɗahira tayi tace, “Ameen Mama na tafi bye”.

Ta juya ta fice, a parlour ta tarar da Umma tana zaune

“Umma sai mun dawo”.

Umma kallon ta tayi sannan tace, “to adawo lafiya”.

Amsa mata kawai tayi ta fice cikin sauri, parcking space ta nufa ta buɗe motan ta da ta kasance ash colour ta shige tabar gidan

Mintuna 15 ya ɗauke ta kafin takai Babban Hospital ɗin wato AL’AMEEN FAMILY HOSPITAL tana shiga tayi parcking motan sannan ta ɗau jakan ta tare da rigan aikin ta tafito, rufe motan tayi kafin ta juya ta doshi cikin Asibitin cikin tafiyan ta na yanga, Lifter ta hau yakai ta hawa na uku kasancewar anan ne Office ɗin ta yake, ko wani Doctors akwai sunan sa agaban office ɗin sa, itama haka an saka Dr. Ɗahira Al’ameen Al’ameen, sai da ta kalli sunan nata tasaki kyakykyawar murmushin ta kafin ta buɗe tashiga ciki, ahankali ta taka har ta’isa kan kujera ta zauna tana ajiye jakan ta tare da rigan aikin ta, files ɗin da ta gani azube akan table ta soma buɗe wa tana dubawa, sai kuma ta miƙe tsaye da nufin fita taji anyi nocking

“Yes come in”. Tafaɗa tana kallon ƙofan

Baffa ne ya shigo hannun sa riƙe da wasu files, murmushi suka sakarwa juna kafin ya’iso ciki ya zauna, itama ɗin komawa tayi ta zauna tana cewa

“yayana Barka da safiya”.

“Yauwa my sweet sister, hope dai kina enjoyed aikin?”

Murmushi tasaki cike da farin ciki tace, “Yes sai dai ban fara ba zuwana kenan”.

Shima murmushin yasaki cike da ƙaunarta a ran sa yace, “Ok ga wasu files ɗin; su ne waɗanda zaki duba anjima da ƙarfe 10:00am, waɗannan kuma na gaban ki na petiens ɗin ki ne Big Dady ya kawo miki, idan kin shirya sai muje in nuna miki Rooms ɗin da suke”.

Ɗahira kallon sa tayi har alokacin da murmushi a face ɗin ta tace, “Tom muje”.

Miƙewa yayi itama ta miƙe tana ɗaukan farar rigan aikin ta tasaka, sosai rigan yayi mata matuƙar kyau fiye da tunanin me karatu, eyeglasess ɗin ta tagyara tana me bin bayan sa

bayan sun fito atare suka jera suna tafiya suna hira sai zuba murmushi duk kan su suke yi.

              ⚫⚫⚫

   .   Buɗe ƙofan tayi ta shigo bayan da Shakira ta bata umarnin shigowa, ahankali ta ƙariso ciki tana karairaya cike da son burgewa ta samu waje ta zauna tana kallon Shakira da itama ta zuba mata idanu tana kallon ta, murmushi ne kwance a face ɗin ta tace

“Suna na Dr. Ayush Abdulkarim, Ni ce office ɗina ke kusa da naki kuma nima ɗin ina cikin wanda Hospital ɗin nan suka ɗauke ni aiki ranan Waliman ku, am.. shine nace bari na shigo mu gaisa”.

Sai alokacin Shakira tasaki fuskarta tace, “ok Ni kuma Dr. Shakira Abubakar Al’ameen”.

Murmushi Ayush tayi tace, “idan babu damuwa zan so mu zama Friends coz tun alokacin Walima naga kin burge ni”.

“Why not”. Shakira tafaɗa tana ɗage kafaɗa

“Thank you, bari inje zan sake dawowa idan na gama aiki”.

Murmushi Shakira tayi mata tace, “ok babu damuwa”.

Tashi Ayush tayi ta fice tana me rufo mata ƙofar, murmushi ta saki tana cije leɓe afili ta furta

“Da sannu Burina zai cika, da sannu mafarki na zai zama gaske, tabbas sai na cika burin zuciyata”.

Juyawa tayi ta shige office ɗin ta dake kusa da na Shakira.

                 ⚫⚫⚫

       Ɗahira bayan ta gama duba petiens ɗin ta ne ta juyo ta nufi office ɗin ta, ta zo karya kwana kenan su kayi karo da wata matashiyar budurwa har files ɗin hannunta suka zube, cikin sauri atare suka ce

“Sorry”.

Sai kuma su kayi murmushi sannan Ɗahira tariga ta cewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button