NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

“Haka ne! To bari inje, yanzu ina da aiki da yawa”.

“Ok”.

     Da fitan Ayush ta shige Office ɗin ta, jikin ta na rawa ta soma sintiri a Office ɗin, ko kaɗan ta kasa yin tunanin da zai kai ta ga mafita, duk wata hanya da zata bi domin magana da Usman abun ya faskara, ta jima tana bibiyan sa a facebook amma har yanzu bata samu yayi mata reply ba, kusan kullum sai ta tura masa saƙon soyayya amma a banza

Tsaki ta ja tana zama akan kujeran ta, wayan ta ta sake ɗauka ta shiga facebook ta hau yin masa text, ga dai shi yana online amma bata samu reply ba. Ayush kamar tayi kuka ta ajiye wayan tana buga tagumi

Jin ƙaran shigowar text, tayi tunanin shi ne tayi saurin ɗaukan wayan, sai dai wata best friend ɗin ta ne tayi mata magana, dogon tsaki taja kafin ta yi mata reply, charting suka soma yi, anan take faɗa mata halin da take ci, kasancewar ita ƙawarta Safra ta tambaye ta “kwana biyu ina ta shige?” Shi ne ta soma bata labari aiki ne ya riƙe ta, har suka gangaro kan matsalan ta

Nan Safra tayi mata alƙawarin taimaka mata, ta yanda zata samu Usman a hannu, nan ta sanar mata nan da kwana biyu zata shigo Kadunan, kasancewar ita tana Zaria ne tana karatu

To a nan ne dai hankalin Ayush ya kwanta, duk da bata san Safra sosai ba, kasancewar a Facebook suka haɗu, amma ta yaba da wayewar ta, tasan zata iya taimakon ta, tunda tafi ta sanin kan duniyar.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

    Ƙarfe 01:30pm. Yau Ɗahira ta tashi daga aiki, tana komawa gida ta shiga ɗakin mahaifiyar ta

Aunty Amarya looked at her in surprise and said, “ah a yau kuma da wuri kika dawo?”

Murmushi Ɗahira tayi tace, “yes Mama”.

“Are you all right?”

Still Murmushi Ɗahiran tayi tace, “akwai baƙon da zan yi ne anjima Mama, shi ne na dawo tun yanzu”.

Aunty Amarya smiled and said, “Masha Allah! May Allah bring him peace”.

“Ameen Mama”. Ɗahira ta amsa mata, sannan ta fice tayi ɗakin su

Kwanciya tayi don ta huta, zuwa anjima sai ta tashi ta shirya.

    Bata fi mintuna goma da kwanciyar ba, Fadil ya shigo ya sanar mata Aunty Amarya na kiran ta

Koda taje kiran, Aunty Amarya kallon ta tayi tace, “in ce dai kin shirya abinda zaki tarbi baƙon naki?”

“A’a Mama”.

“To haka ake yi ne? Ki je ki shirya masa wani abun, koda yake ki buɗe Fridge ɗina zaki ga markaɗaɗɗen kayan miya dana saka, anjima zan yi amfani dashi, sai ke kiyi amfani dashi ɗin kiyi masa miya zai fi”.

“To Mama”. Ɗahira ta amsa mata tana yin wajen Fridge ɗin

Da kallo Aunty Amarya tabi ta dashi har ta fice, sai ta saki murmushi kawai, a ranta tana ma ɗiyarta fatan dacewa da Miji na gari.

    Ɗahira da fitar ta kichen ta nufa takai kayan miyan ta ajiye, sannan sai ta koma kan dainning taci abinci, tana gamawa ta koma kichen ta soma haɗa abincin baƙon ta, shinkafa da miya tayi masa, sannan ta haɗa Juice Kala biyu, sai tayi masa farfesun kifi, kasancewar shi suke dashi, dayake Abbu yafi son kifi shiyasa ba sa rabo dashi a koda yaushe, za su iya rasa Nama na kwanaki a gidan amma ban da kifi.

      Time ɗin da ta gama komi ƙarfe 02:40pm. Tayi, da sauri-sauri ta zuba a cikin coolars masu kyau, sannan ta wuce ɗaki tayi wanka, tana fitowa ta shirya cikin riga da skert na atamfa me ruwan silver, sai ratsin fari kaɗan-kaɗan, sai tayi make-up tayi ɗaurin ɗankwali me kyau da ya ƙara fito da kyawun ta

Zama tayi gefen gado tana kallon agogon ɗakin, har ƙarfe uku tayi ta wuce ma, wayan ta ta ɗauka tana kallo ko zata ga message ɗin sa, but babu, dole tayi zaman jiran sa.
[6/3, 9:25 AM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL.

SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT????????‍

بسم الله الرحمن الرحيم

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION????

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A✍️*

???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️

????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????

        
????????????????????????????????????????
???????? ???????????????????????????????? ???????? ???????????????????????? ???????? ???????????????? ɗ????????????. ????????????????’???? ????????????????????????.

        EPISODE Twenty Four

       Har ƙarfe 04:30pm. Ɗahira tana zaune jiran masoyin ta, amma babu shi, kuma babu text ɗin sa, ta ɗauki wayan ta tana ajiye wa yafi sau a ƙirga, daga ƙarshe ta tura masa message, but babu reply, dole ta haƙura ta tashi tayi sallan Asar, sannan taci gaba da zaman jiran sa, ji kawai take yi tamkar ta ɓarke da kuka, amma haka ta daure, a ranta tana ba shi uzuri; Maybe wani abu ne ya hana sa zuwa

Har aka kira magriba Ɗahira na zaune bakin gadon ta, ta zuba tagumi tana ta tunani. Tashi tayi ta gabatar da sallan tukun ta koma ta zauna.

      Aunty Amarya aiko Fadil tayi yazo ya kira ta, koda taje sai Aunty Amarya ta tambaye ta “ko bazai zo bane?”

“I don’t know either. Mama, I still keep quiet, and at three o’clock we made it come.”

Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta saki, tana kallon Ɗiyarta ta da damuwa ya nuna a fuskarta kafin tace, “to kiyi masa uzuri,
maybe there is something stopping him from coming, Allah yasa dai lafiya”.

“Ameen”. Ɗahira ta amsa tana ficewa

Ɗaki ta koma ta kwanta tana lumshe idanun ta, jin ƙarar shigowar text, da sauri ta tashi zaune tana ɗaukan wayan ta, nan da nan murmushi ya suɓuce mata ganin Masoyin ta ne, buɗe wa tayi jikin ta na rawa ta soma karanta wa

      “Ban san da bakin da zan baki haƙuri ba Ɗahira, tabbas nasan zaki fahimce ni sabida ke me yiwa kowa uzuri ne, kuma na san kina da kirki da sanin Ya kamata. yau na so in bayyana a gaban ki, in nuna miki tsantsan ƙaunar da nake miki, sai dai kuma abu mafi girma ya shigo rayuwar mu, bazan ɓoye miki sirri na ba Ɗahira, na zaɓi faɗa miki ne kar ki ga laifi na, wanda na san zaki fahimce ni kiyi min uzuri. Mahaifiya ta ta haramta min zuwa gare ki, domin ta ce “idan har na aure ki bata yafe min ba,” ta rigada ta zaɓa min matar da zan aura, don Allah! Kiyi haƙuri domin ba’a son Raina zan bar ki ba, sai don bin umarnin mahaifiya ta, amma ki sani ina matuƙar ƙaunar ki, har in koma ga mahalicci na bazan taɓa dena son ki ba.”

       A.A.A. Masoyin ki.✍️

      Lumshe idanuwan ta tayi, hawayen dake tsiyaya akan kuncin ta tun soma karanta text ɗin; suka ci gaba da kwaranya, wani irin ƙunci ne ya tokare mata maƙogwaro, wanda daƙyar take iya haɗiye yawu

Dauriya dai me dauriya sai da ta gwada yin shi, amma ta gaza, dole ta zube kan gadon ta hau rusa kuka, kuka take yi sosai zuciyarta na mata zafi tamkar zai faso ƙirjin ta

Taya ma zata iya jure wannan halin da take ciki, meyasa zai mata haka? Meyasa zai tafi ya bar ta a lokacin da take buƙatar sa cikin rayuwan ta? Ya tafi ba tare da ta gansa ba, ya tafi ba tare da tasan sunan sa ba, dama ashe ba son ta yake yi ba? Meyasa to ya koya mata ƙaunar sa?…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button