NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

Fadila ce ta shigo ɗakin idanunta ya sauka akanta, sai ta taɓe baki tana ƙarisawa wajen ta tace, “Are you all right?”

Sai a lokacin Ɗahira ta ɗago kanta tana kallon ta, sai kuma takau da kan tare da faɗin “me kika gani?”

Fadila bata ce komi ba ta juya ta tafi, dama wayan ta tazo ɗauka, tana ɗauka ta fice a ɗakin, wannan shi ne halin su su duk ka biyun basu cika kula juna ba duk da duk kan su suna da ƙyaliya, But kasancewar Iyayen su suna kishi shiyasaka su ma suke taya su a junan su, ga dai shi ɗaki ɗaya suke kwana amma sai su wuni su hantse ba wacce zata kula ƴar uwanta, ba me shiga harkar ɗaya sai sun ga dama, ita dama Ɗahira ƴar ba ruwanta ne, bata cika shiga shirgin da ba nata ba, bata da son hayaniya amma tana da fara’a da kirki, komi tana yin abinta ne cikin class, sai dai alokaci ɗaya baza ka taɓa fahimtar halin ta ba sai ka zauna da ita, Fadila ma haka sai dai wani lokacin tana da yawan wulaƙanci a ɗabi’a, domin miskilancin ta yayi yawa don in bata ga dama ba ko kai uban waye baza ta kula ka ba sai taga dama.

    Ɗahira cire tagumin tayi ta soma shafe Baby face ɗin ta da kayan makeup, ita gwanar son gayu ne duk sanda zaka ganta bata rabo da kwalliya, Light makeup tayi wanda ya ɗau fuskarta sosai ya ƙara fito da zallan kyawunta, ba maganar wasa ba Ɗahira tana ɗaya daga cikin kyawawan gidan, duk a cikin ƴan matan gidan zan iya cewa tafi su kyau duk da suna matuƙar kama, sai dai ita yanayinta da komi nata ya banbanta da nasu

Buɗe Lockern tayi ta ciro Glass ɗin ta tasanya Wanda ya zame mata ɗabi’a ko yaushe idan zaka ganta tana tare dashi, sai ta miƙe ta nufi gaban gadon ta taɗau wayan ta ƙirar IPhone 11+, takalmin ta kawai ta sanya ta fito batare da ta yafa komi ajikin ta ba baya ga ɗankwali da ta sanya ta rufe tulin gashinta, tana fitowa parlor ta hangi Fadila zaune har yanzu, sai dai wannan lokacin wayan ta take dubawa, ɗakin Mahaifiyar ta tawuce, tana shiga babu kowa hakan yasa ta fito ta doshi cikin gidan, sai da ta wuce wani dogon corridor kafin ta buɗe wani ƙofa ta shige, ahankali ta soma taka Step tana sauko wa sai gata cikin wani kyakkyawan parlour ƙarami, sai tabi ta wani ƙofan ta fito babban parlor’n gidan da ya kasance cike da mutane kowa sai harkan gaban sa yake yi, tana isa ta gaishe dasu sannan ta wuce wajen ƴan matan dake can gefe zaune, zama tayi gefen Shakira da Salma (ƴa ga Hajiya LAILA)

Shakira CE ta soma cewa, “Now I ask Aunty Amarya where are you? She told me kina Sashin ku ai”.

Ɗahira She smiled and said,  “na tsaya wanka ne”.

Fiddausi da ta kasance ƙanwar Salma tace, “to ya Naga hannayen  ki rabbana suna dukan cinya, ina tsaraban tamu?”.

Kallon ta Ɗahira tayi tace, “What are you eating na baka na zuba? Let me rest for a while, sai ki zo ki taya ni kwance jakan”.

Gaba ɗaya wajen su kayi dariya ban da Yusra dake faman latsa wayan ta ko ɗago kai bata yi ba

Shakira tace, “kin ji ƙyale wannan yarinyan bata da hankali, ke da akaje Duba marar lafiya kike zancen tsaraba?”

Ɗage gira Fiddausi tayi tace, “to kuma akace idan anje baza’a yi tsaraba ba? Nasan da cewa waɗannan tsofaffin baza su barta haka ba sai sun haɗo ta da abin lasawa”.

Shamsiyya (ƴa ga Hajiya Ikram) tace, “ƙwarai kuwa Fido sai dai idan mu baza’a bamu ba, don naga tunda ta shigo Shakira take ƙifƙifta mata idanu”.

Salati Shakira ta saki tana rufe bakin ta tare da zaro idanu, sai suka saki dariya suna shewa, wasu suce “eh su ma sun gani” wasu kuma suce “kai Shamsiyya banda ƙarya”.

Dogon tsaki Yusra taja ta miƙe ta wuce abin ta, yayinda duk kan su suka bi ta da idanu kana Salma tace, “Oh, that juju girl, what’s wrong with her?”

Dawo da idanun ta Ɗahira tayi gare su tana murmusawa tace, “Ni kun ga tafiya na bari inje in miƙa gaisuwata ga Kaka tunda naga ban ganshi anan ba”.

Tafa hannu Fiddausi tayi tace, “ai Kaka yau sai dai yayi haƙuri mun hana sa fitowa, cewa yayi bazai iya da surutun mu ba ya shige ciki ya kwanta”.

Tashi Ɗahira tayi tana faɗin “ai gwara haka kar ku ƙara masa damuwa”.

Daga haka ta wuce batare da ta kula su da sukayi mata caaa ba.
[5/21, 9:54 PM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
             FAMILY DOCTORS
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
  NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT ????????‍

بسم الله الرحمن الرحيم

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION????

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A✍️*

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattpad: UmmuDahirah????
        

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

NATSUWA A SALLAH
      Sallah babbar matsala ce. Ganawa ce tsakanin Bawa da mahaliccin sa, Ubangiji maɗaukakin sarki. Saboda haka ana buƙatar cikakkiyar natsuwa, a tattara hankali wuri ɗaya domin wannan ganawa ta musamman.
     A cikin ayoyi biyun farko na suratul Mu’uminun ana faɗa mana cewa:
     “Lalle ne, muminai sun sami babban rabo, wanɗanda suke a cikin sallar su masu tawali’u ne.”
    Watau, Muminai wanɗanda idan sun tsaya yin Sallah sai gaɓoɓin su da zukatan su su natsu, babu wani abu mai shagaltar da su daga ambaton zatin Allah maɗaukakin sarki, to, irin su suke rabban ta. Natsuwa cikin sallah da ƙasƙan da kai ga Allah su ne alamun imani na gaskiya da Tauhidi tsantsa, don kuwa ko yaushe bawa yayi kusa da Ubangijin sa sai ya haɗa jin tsoron sa, musamman ma dai a sallah inda yake ganawa da shi, yake tunawa da girman sa.

    EPISODE Three

      A hankali ta sanya hannun ta ta soma jan gemun sa

Hakan yasaka ya buɗe idanuwan sa ya sauke a kan ta, murmushi yayi yana kallon ta yace, “Ni dama nasan babu wanda zai min haka sai ke, When did you come back?”

Murmusawa tayi tana janye hannun ta tace, “yanzu babu daɗewa”.

Tashi zaune yayi yana faɗin “To ya me jikin da fatan ya samu sauƙi?”

Sai da ta dawo kusa dashi kana tace, “Alhmadulillah Kakus suna gaishe ku kowa da kowa”.

“Mun gode muna amsawa”.

“My Kakus miss you so much”.

Murmushi Kaka yayi yana ɗaura hannun sa a kan ta yace, “nima haka Matata, You have left me alone I miss you, kin bar ni da waɗannan yaran mara su kunya masu ido a tsakar ka ko hiran basu taya ni”.

Dariyan ta me kyau ta saki tana jingina kanta jikin Kakan tace, “Kakana kenan! don’t worry, I’ll be back. hira har sai ka gaji daji, akwai labarin ma da na samo maka”.

“Well I hear you tell me”.

Ƙofar da aka turo ne ya sanya Ɗahira rufe bakin ta without saying a word. Big Dady ne tare da Abbu suka shigo da sallama, amsa musu su kayi yayinda Ɗahira ta tashi da sauri ta nufi Mahaifin nata ta rungume shi tana faɗin

“Abbu na”.

Murmushi yayi yana shafo kanta yace, “to ya kin dawo ko zaki fara?”

Dariya tayi tace, “I’m really missing you, Abbu.”

Sai kuma ta sake shi, Then she hugging Big Daddy and said, “Daddy, I’m the only one.”

Shafo kanta yayi shima yana smiled and said, “my daughter when did you come back?”

“Now Dady”.

“To ya me jikin yaji sauƙi dai ko?”

Gyaɗa masa kai tayi tana faɗin “Alhmadulillah”.

Big Dady yace, “madalla haka ake so”.

Sannan ya juya yana kallon Kaka yace, “Dad, we’re here to talk about new products da za’a shigo dasu.”

Kaka yace, “to shikenan”.

Abbu da ya samu wuri ya zauna yace, “Mamana bamu wuri za muyi magana”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button