NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

     Ɗahira motan ta kawai take ja tana tunani, ko kaɗan ta kasa gane takamaiman abinda ke damun ta

Tsaki kawai ta ja ganin tana son damun kanta da tunanin banza, ƙara Speed ɗin motan tayi tana kallon agogon hannun ta

Dai-dai ta isa kusa da Hospital ɗin, tana shirin shan kwana ta shiga, bata kula sosai ba, Ashe wata mota babba na ɗan gote ta dumfaro. shi kuma can ɗaya side ɗin me machine ya dumfaro da gudu yana shirin gilma motan, sai motan tayi ciki da shi, Wanda machine ɗin da me machine ɗin tuni sun yi hanyar su daban, inda machine ɗin ta zo kan motan Ɗahira da har ta kusa tura kan hancin motan ta cikin Hospital ɗin, sai ji kake yi motar nata tayi ƙuuuuuuu.. saboda wani wawan burki da taja kasancewar buguwan da machine ɗin tayi a kan motan ta, yayi matuƙar tsorata ta har ta rasa nutsuwar ta gaba ɗaya taja burki a take tana salati

Can kuwa wajen babban motan nan tuni tayi ciki da wasu motan da suka dumfaro ta,  nan da nan motoci da mashina suka harhaɗe aka haɗa babban hatsari, jini ya soma ambaliya a titin, machine ɗin nan na saman motan Ɗahira, inda wata motan kuma ta bugi motan nata tuni tayi ratsa-ratsa.

Kankace me mutane sun soma zuwa ceton rai, nan da nan wajen ya hargitse da hayaniya. Allah yasa kusa da asibiti ne, nan akai ta zaro mutane ana nufan asibiti da su.
[6/7, 8:19 AM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL.

SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT????????‍

بسم الله الرحمن الرحيم

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION????

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A✍️*

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

        
SADAUKARWA
???????? ???????????????????????????????? ???????? ???????????????????????? ???????? ???????????????? ɗ????????????. ????????????????’???? ????????????????????????.

       _Wannan shafin naku ne Masoyana, kar ku ce ban gaishe ku ba????, to ku shaƙata da wannan na ku ne kyauta, ina ƙaunar ku nima, har da waɗanda suka ɓoye kansu, Ni *JIKAR LAWALI* ina matuƙar jin daɗin nuna soyayyar ku gare Ni, idan baku Fans to babu Ni ce._

        EPISODE Twenty Eight

        Su Abbu na cikin Office ɗin Big Dady, inda suke meeting a kan shigo da magani da za’a yi musu, da sauran abubuwan da asibitin yake buƙata. A lokacin ne labarin mummunan hatsarin da ya afku a wajen Hospital ya iso gare su, ai tuni sun fito don zuwa su ba da agajin gaggawa

Sai da suka sauka downstairs ne, labari ya riske su da Ɗahira hatsarin ya ritsa. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un tashin hankalin da suka shiga baki ma bazai iya bayyana shi ba, kankace me sun ruɗe gaba ɗaya kowan su sai sharce gumi yake yi, musamman da suka ga yanda ake shiga da masu hatsarin rai a hannun Allah. Nan su ma suka bi ayari fannin emergency rooms

     Su Baffa da Fadila basu fito gida ba ma, labari ya kai musu, tunda shi Baffa dama be yi ninyan shiga ba yau, sai yamma, amma tuni sun ruɗe da su Aunty Amarya sun taho asibitin, sai dai an kasa sanar wa Kaka tunda ba’a san halin da take ciki ba yanzu.

     Lokacin da suka iso asibitin, a reception suka tarar da su Aunty Zainab da Yusra da Shakira, tunda su ba fannin su bane, su Big Dady kuma na ciki.

   Haka DOCTORS da staff’s suke ta sintiri suna ba da taimakon gaggawa

Baffa wuce su yayi ya bar su nan, shima ya nufi emergency rooms ɗin, duka tagumi suka yi har Hajja Fatu, domin itama taƙi shiga tunda itama ba fannin ta bane. Aunty Amarya ne kaɗai a wajen take share hawaye, sai Fadila da tayi zugum tana tunanin ƴar uwan ta a ranta, har bata san sanda ƙwalla ya zubo mata ba, babu abinda take tuna wa sai fitowar ta gida yanzu da abinda ya faru, dayake ta side ɗin windown ɗakin su suka tsaya, shiyasa tana kallon draman da suka yi da su Sa’adatu daga saman bene. haka Allah ke lamarin sa, da mutuwa ne sai a aiko musu a ce ta mutu.

       Allah ya taƙaita, Ɗahira bata wani ji rauni sosai ba, sai dai suman da tayi ne har yanzu bata farka ba, ta samu buguwa a kanta har da ciwo, sai kuma gwiwar ƙafafuwan ta da suka ƙuƙƙurje. Alhmadulillah gaba ɗaya ahalin sun samu kwanciyar hankali musamman da suka shiga suka duba ta, time ɗin tana barci tunda an yi mata alluran barci, ba’a haɗa ta da kowa ba a ɗakin da take, sauran suna can rooms ɗin, sun daɗe wajen ta, inda suka je ɗaki-ɗaki suka duba sauran mara su lafiyan.

    Sai da ta farka kafin su Aunty Amarya suka bar asibitin, tare da masu aiki suka koma tunda sun kawo musu abinci.

     Ɗahira tana samun kulawa sosai wajen su Abbu, barin ma kar ace Doc. Sa’id, domin kasancewar fannin sa ne, shi yayi ruwa yayi tsaki yana kula da ita, abu kaɗan ya matso kusa da ita yana tambayan ta abinda ke damun ta, sai hakan ya faranta ran iyalan gidan, musamman su Abba, don a tunanin su akwai wani abu a tsakanin su, tunda itama Ɗahira sosai ta saki jikin ta dashi, ta yanda ma ta nuna sanayya a gare sa.

     Hakan ko kaɗan be ma Baffa daɗi ba, shiyasa be wani zauna ba ya bar wajen, domin bazai iya zama yana kallon wani banza yana hira da ita ba, da kuma bata kula wa sosai.

      Usman kam koda ya san abinda ke faruwa, ko leƙowa be yi ba, yana Office ɗin sa, sai da Big Dady ya kira sa yayi masa faɗa, sannan ne ya zo ya duba ta, kuma komi be ce mata ba, kamar yadda itama bata ko kalli inda yake ba. Haka ya juya yabar ɗakin yana taɓe baki.

    Babu wanda ya sanar wa Kaka, har sanda su Abbu suka dawo gida, sannan ne suka sanar masa cikin nutsuwa, amma duk da haka sosai ya ɗaga hankalin sa, cewa yayi “dole sai an kai sa ya duba ta”. Ga shi lokacin dare ne. Dole haka suka fito gaba ɗayan su, Big Dady Abba da Abbu suka nufi asibitin.

      Umma ce da ɗaya daga cikin ƴan aikin su za su kwana da ita, bisa umarnin Abbu. time ɗin ma tayi barci sanda suka zo

Sai a nan hankalin Kaka ya samu sukuni tunda ya ganta a kyakykyawar yanayi. Sun jima kafin suka baro asibitin.

    Washe gari da safe ma ya saka aka sake kawo shi

Lokacin Ɗahira na zaune tana shan tea da aka haɗa mata suka shigo, taji daɗin ganin su, nan tabi su ɗaya bayan ɗaya tana gaishe su

Kowan su na amsa mata cike da kula wa, tare da tambayan ta ya jiki?

Murmushi tayi tace, “it’s so easy”.

Big Daddy yace, “Are You sure my daughter babu abinda ke damun ki?”

Gyaɗa kanta tayi tana sake tabbatar masa da cewa, “Yes my Dady”.

Murmushin farin ciki gaba ɗaya suka yi

Kaka yace, “ai gaba ɗaya kin ɗaga min hankali Matata, a jiya kasa barci nayi, ban ma karya ba na taho duba ki, ashe ke ga shi har kin samu saka abinci a cikin ki, kin bar Mijin ki cikin tashin hankali”.

Ɗahira murmushi ta sakar masa, tana langaɓe kai tace, “eyya Miji na, ban sani bane ai, ka ga da ban ci komi ba nima kamar kai, na tausaya maka matuƙa tsoho na”.

Dariya gaba ɗaya suka yi har Kaka da ke faɗin, “Ja’ira”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button