NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

  *EPISODE Six*


    Murmushi Hajja Fatu ta ƙirƙiro cikin tsananin ruɗewa da son ɓoye halin da take ciki tace, "am..uhmm babu, auhm Ni da wata ƙawata ce da taci amana ta". Taƙarishe maganar tana sake sakin murmushi

Ɗahira kuwa kallon ta kawai take yi, domin kuwa duk abinda ta faɗa ta riga taji, sai dai tayi tsananin mamaki da al’ajabin abinda Hajja Fatu take faɗa akan Mahaifiyar ta da ita kanta. ita ma ɗin nuna mata tayi kamar bata ji maganar nata ba illa sakin murmushi da tayi tace, “But Hajja, why don’t you forgive her? I don’t see the point in keeping a person in mind.”

Wani irin ajiyan zuciya Hajja Fatu ta saki jin cewa ta yarda da abinda ta faɗa mata, hakan na nufin bata ji maganar da tayi ba kenan, murmushi ta sake ƙirƙirowa tace, “ƴata baza ki gane zafin cin amana ba, amma tunda kin ce in yafe ai Ni me iya yafe mata ne, nima sai yanzu na gane hakan be da wani amfani muyi ta sa’insa akan abinda be kai ya kawo ba”.

Sai kuma ta sauya akalan maganar da tambayarta “ina zaki je kika yo nan?”

Ɗahira said, “I will reply to Mamana’s message,”

Gyaɗa kanta Hajja Fatu tayi tace, “ok”.

Sannan ta juya ta tafi batare da ta sake furta komi ba

Ɗahira kuwa bin bayan ta tayi da kallo har sanda ta ƙule wa ganin ta, maganganun Hajjan ne suka dawo mata

“What does that mean?” Tafaɗa aranta tana sake zurfafa a tunani

Tabbas ta san akwai abinda Hajja ke shiryawa akan Mahaifiyar ta, sai dai kuma duk yanda za’a yi baza ta taɓa bari taci nasara ba, tun farko dama tasan Hajja Fatu ba ta ƙaunar Mahaifiyar ta, Kasancewar ita A’isha wato Aunty Amarya Asalin ta ƴar Soba ce a ƙaramar hukuman Zaria, karatu ya kawo ta Kaduna tana zaune wajen auntyn ta, to anan ne Mijinta Al’ameen ya ganta har ya’aure ta, tun sanda aka kawo ta gidan Hajja Fatu ta nuna ba ta ƙaunarta kuma take son nuna ita ɗin bare ce acikin su, sabida alokacin ƙanwarta dama ta daɗe tana ƙaunar Al’ameen wato Abbu, to hakan ya saka ta ɗau alwashin sai ta fid da Aunty Amarya a cikin gidan ko ta halin ƙaƙa, don a cewarta tunda ƙanwarta bata same shi ba duk a dalilinta, to, itama sai ta rasa shi

Numfashi Ɗahira ta sauke tana ɗauke kanta daga kallon Hanyan da Hajja Fatu tabi, ko kaɗan baza ta so ta faɗa wa Mahaifiyarta wannan maganar ba, domin ta san hankalin ta zai tashi matuƙa, sai dai zata dage da taya ta da addu’a duk wani wanda ke binta da sharri ya koma masa

takawa tayi ta shige Parlour’n Hajiya da sallama

Hajiya da har yanzu take zaune tana tunanin maganar Hajja Fatu, ta ɗago kanta tana bin Ɗahira da kallo, fuska babu walwala ta’amsa mata sallaman

Ita kuwa Ɗahira ƙarisowa tayi ta zauna a kujera tana kallon Hajiya tace, “Hajiya sannu da hutawa”.

“Yauwa”. Hajiya ta’amsa ataƙaice tana sake tamke fuska

Sosai Ɗahira tayi mamakin halin da Hajiya ta nuna mata, domin ta san ta mace ce me fara’a, kuma suna ɗasawa da ita ainun, tayi mamaki da ganin sauyawar fuskarta amma kuma sai ta dangana hakan da ko wani abun ne ke damunta, don ko kaɗan bata yi tunanin abinda ya faru ɗazu ba

“Hajiya dama Mama ce tace inzo in amsar mata saƙo”.

Miƙe wa Hajiya tayi batare da ta tanka mata ba ta shige ɗaki, sai gata ta fito da leda ta miƙa mata

Amsa Ɗahira tayi cike da girmamawa ta tashi ta fice

Ita kuwa Hajiya rakata tayi da harara tana jan tsaki

Ɗahira da har ta fice sai da tajiyo sautin tsakin, hakan yasaka taja ta tsaya tana kallon ƙofar, nan take kuwa abinda ya faru ɗazu ya dawo mata kwanya “kenan Hajiya tana fushi da ita ne saboda abinda ya faru ɗazu?” Ta tambayi zuciyarta cike da mamaki, taɓe bakin ta kawai tayi tajuya tayi tafiyar ta, Part ɗin Hajja Fatu ta shige, babu kowa a parlour sai ta nufi ɗakin Shakira kanta tsaye, tana isa ta tura ƙofar ta shiga da sallama a bakin ta

Shakira dake zaune gaban mirror tana gyara kayan kwalliyan ta ta ɗago da kanta tana kallon ta, sai kuma ta saki murmushi tana cewa, “ƴan mata adon gari me aka kawo min ne?”

Ƙarisawa kusa da ita Ɗahira tayi tana jingina da bango tace, “a’a Ni babu abinda na kawo miki, amsa dai nazo yi, kin san yanzu wayata ta samu matsala shiyasa zaki haɗo min kan Littafaina in tafi dasu”.

Dariya Shakira tayi tace, “kai wlh Ƴanmata yau kin bala’in burge Ni, ashe zaki iya kai ƙaran Ya Usman? Shin wai ina tsoron da kike mishi ya tafi?”

Taɓe baki Ɗahira tayi kana tace, “ai dama ɗan hakin da ka raina wataran shi ke tsole maka ido, kema da kanki kin faɗa da ba yanzu ba, Ɗahiran Da; da na yanzu sun sha banban”.

Miƙe wa Shakira tayi tana sakin murmushi tace, “gaskiya ne ƴan mata, don yanzu ba lokacin Da damuke yara bane, yanzu mu ɗin DOCTORS ne manyan yara, kinga kuwa baza mu iya ɗaukan raini ba, wlh kin burge Ni amma Ni kam ba na tunanin zan iya fa”.

“Dama ai ke matsoraciya ce, Ni dai ɗauko min in tafi Mama jira na take yi”.

Drower Shakira ta buɗe ta soma kwaso mata Books ɗin tana cewa, “hmm baza ki gane bane, Ya Usman ya wuce gaban kwatance, wlh ko wacce mace idan har zata haɗu dashi sai dai ta kalle shi da idon soyayya amma ba faɗa ba, kwarjinin sa da kyawun sa tare da isa da izzar sa su kansu sun ishe ka, ina matuƙar shakkan Ya Usman kuma ba na son abinda zai haɗa ni dashi da har zai saka mu saka ƙafan wando ɗaya dashi, but ke kam nasan kashin ki ya bushe wlh don ba ƙyale ki zai yi ba, ya lafiyan Kura ma bare ace tayi hauka, uhmm ke dai kawai ki guji ranan haɗuwan ku”.

Ɗahira takowa tayi tazo gaban ta ta soma kwashe Littafan tana zubawa a leda, batare da tabi ta maganarta ba tace, “Ni kin ga tafiya na ba ni da lokacin ku daga ke har shi ɗin”.

Tajuya tayi ƙofa zata fice, dai-dai lokacin da Yusra ta turo ƙofan ta shigo suka kalli juna suka ɗauke kai sannan ko wacce ta wuce

ƙarisowa Yusra tayi kusa da Shakira dake zaune bakin gado; itama ta zauna gefen ta tana cewa, “wai ya maganar mu na zuwa shopping yaushe za mu je?”

Shakira tace, “ki bari a kawo mana Mota mana, kin ga sai muje aciki ko ya kika ce? Don Ni wlh bazan fita a tsohuwar mota ba, gwara muje muna tsole idanun Gayu”

Dariya Yusra tayi tana cewa, “shegiya inda ba’a ce za’a ba mu ba fa? ya za kiyi dole ki fita a ciki”.

“Uhm baza ki gane bane amma dai gwara mu bari sai ranan Sunday ɗin muje, kin san har gidan su Marcy za muje ranan wlh”.

Hannu Yusra ta bata suka kashe tana cewa, “gaskiya ne Tawan ai wlh yanzu ma kika tuna min da ita, ahh ai dole ne ma muje, kai wlh har kin sani na ƙosa ranan tazo, uhmm Allah ya kai mu har na hango irin wulaƙancin da zanyi”.

Sai suka kwashe da dariya suna sake tafawa

Shakira tace, “kin san yanzu muka gama hiran ki da mutumiyar taki?”

“Wace kenan?” Yusra ta tambaye ta cike da rashin fahimta

“Wace kika sani ban da Ɗahira, Ni na rasa meyasaka ba ta ƙaunar ki duk sanda zamu zauna sai tayi maganar ki, abun mamakin ma yanda tayi ta zagin Ya Usman anan wajen, uhmm duk wai akan waya”.

Ɗaure fuska Yusra tayi tace, “wlh yarinyan nan akwai ranan da zan cire mutunci mu goge raini, ni fa na gaji da kawo miñ ƙarar ta da kike yi a kaina tana zagi na, wlh zan je inji dalilin da ya saka take zagi na”. Tana ƙarike maganar ta miƙe da ninyar tafiya

Shakira tayi saurin riƙe ta tana cewa, “ke kuma meye haka? Yau ta soma zagin ki da zaki damu? Wlh idan baki iya kama ɓarawo ba sai ya kama ki, yanzu idan kika je sai kice mata mene? ki bari duk ranan da kika kama ta tana maganar naki sai ki ɗau mataki amma ba yanzu ba, kuma menene na damuwa tunda gani ina faɗa miki komi?”.

Yusra dake tsaye har yanzu kallon Shakira take yi har ta dire aya kana ta ɗaura da nata, “But wlh today I have to tell Hajiya everything, dama ina ɓoye mata ne ban son hankalin ta ya tashi”. Daga haka ta juya ta fice fuuu kamar ana tura ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button