NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

Babu musu ta matsa mishi yazo ya soma duba mata, shima ya daɗe yana taɓe-taɓen sa kafin yace mata, “wake up the car”.

Shiga tayi tayi ma motar keey amma har yanzu ya ƙi tashi

“Ina ga dai motar ki sai ta ga bakanike coz myb wani matsalan ne babba wanda baza mu iya gane wa ba”. Yayi maganar bayan ya rufe mata garejin

“To Nagode”. Tace dashi tana ciro jakarta kafin ta rufe motan da keey

“In ba damuwa muje in rage miki hanya mana”.

Ta tsinkayi muryan sa da har ta juya baya zata tafi

Jimmm tayi tana tunani domin ita mutumin ko kaɗan be mata ba, coz ta kula kallon tsiya ne dashi tun ganin sa na farko

Murmushi yayi yana takowa wajen ta yace, “don’t worry. Ni ba siyar da kanki zanyi ba, ai kin san a nan nake aiki balle kice Ni ɗin baƙo ne, so ni ba baƙo bane babu wanda be San ni ba, My name is Dr. Sa’id Khan”.

Kallon sa ta ɗan yi sai kuma tayi guntun murmushi tace, “ba damuwa mu je”.

“Yauwa ko ke fa”. Yafaɗa yana yin gaba wajen motar sa

Shi ya buɗe mata murfin motan da zumman ta shiga

Sai kawai ta ga abun yayi mata wani iri domin ita idan har ba Baffa ba basu taɓa hakan da wani ba, hakan ko kaɗan be burge ta ba, amma babu yanda zata yi ta shige ta zauna ya rufe mata

Shiga shima yayi yaja motar suka bar asibitin

A cikin motan ma babu wanda yayi magana cikin su, sai da suka ɗan yi tafiya kafin ya soma jan ta da Surutu duk a kan aikin nasu

Ko kaɗan ba ta jindaɗin surutun nasa

Shi kansa ya gane ba ta ƙaunar hiran sa; yanda take amsa masa maganar kamar baza tayi ba, don haka yaja bakin sa yayi shiru yana mamakin yarinyan, shi tunda ya ganta yaji ta burge sa matuƙa kuma yana son ƙulla alaƙa da ita, sai dai ya ga alamun hakan ba me yiwuwa bane duba da yanda take ɗin, da alamun tana da girman kai kuma zata yi wuyan sha’ani, a yanda ya fahimce ta kenan

Har suka kai ƙofar gidan su kafin ya tsai da motan

Kallon sa Ɗahira tayi cikin siririyan muryanta me kamar tana yanga tace,”Thank you, Dr.”

He smiled and looked at her and said, “It’s all right.”

Buɗe motan tayi ta fito

Dai-dai lokacin su Baffa da Usman suka ƙariso wajen sun dawo sallan magriba

Gaba ɗaya kallon ta suke yi, yayinda Usman ya ɗauke kansa time ɗin da ta juyo zata sauke idanun ta a kansu, cikin gidan ya wuce batare da yayi wa Baffa magana ba

Shi kuma Baffan sai ya nufo ta fuskarsa duk babu walwala yana bin motan Dr. Sa’id da kallo da har ya ja ya tafi

Itama ganin ya taho ɗin ne yasa ta tsaya tana masa murmushi

Yana ƙari so wa idanun sa a kanta yace, “wannan kuma wane ne? ina Motar taki?”

Sai da ta kalli hanyar da Dr. Sa’id yabi kafin ta dawo da ganin ta kanshi tace, “Yaya Motata taƙi tashi ne wlh ban san kuma me ya faru ba, shi ne yace in zo ya rage min hanya”.

Gaba ɗaya zuciyar Baffa ba ta mishi daɗi, tsananin kishi ne yake nuƙurƙusan sa a ransa, daƙyar ya”iya saisaita kansa ya sake jeho mata tambaya

“Aina Motar taki ta tsaya da har kuka haɗu dashi?”.

“A cikin Hospital ɗin ne fa, kuma shima Dr. Ne cikin asibitin shiyasa ma na yarda na hau, but da farko ban yi ninyan hawa ba”.

Murmushi Baffa ya kirƙiro yace, “let’s go then”.

Babu musu tayi gaba yana bin ta a baya duk da ita bata fahimci musabbabin tambayan nasa ba, amma ta san cewa shi ɗin Yayanta ne yana da right ɗin tambayar ta

Sai da suka shiga ciki kafin suka jera cikin gidan, Part ɗin su Ɗahira suka wuce

Suna shiga da sallama, Aunty Amarya dake zaune ita da Fadil suka amsa musu

“Aaah maraba da Mijina”. Aunty Amarya tafaɗa tana yalwata fuskarta da fara’a

Baffa na faman shafa kansa yana murmushi ya ƙariso ya zauna a kan kujeran kafin ya gaishe ta

Ta’amsa masa cike da fara’a tana tambayar sa aiki

Itama Ɗahira sannu da gida tayi mata ta wuce ɗakin su ba tare da ta zauna ba

Su kuma suka ci gaba da hira suna kallo

Daga baya itama Umma ta fito aka ci gaba da hiran da ita

Baffa duk ya ƙosa Ɗahira ta fito amma tunda ta shiga bata sake fitowa ba, shi kuma ya zauna ne don ita amma tunda ta fito ta zuba abinci ta sake shige wa ɗaki, aiki take yi a ciki shiyasaka ta zauna nan ɗin tunda ba ta son hayaniya

Sai da aka kira sallan isha’i kafin Baffa ya miƙe tare da Fadil suka fito

Anan suka ci karo da Fadila itama dawowar ta kenan, gaishe da Baffa tayi

Ya’amsa yana faɗin, “Sarkin miskilanci sai yanzu aka dawo?”

Murmushi tayi tace, “Yaya kana son dai tsokana ta ko?”

Murmusawa yayi shima yana cewa, “ai gaskiya ne, kwana biyu ma gaba ɗaya kamar ba kya nan a gidan, rabon da in ganki na jima sai jiya a wajen meeting”.

Fadil dake tsaye yana sauraron su yace, “ai Yaya wlh duk wanda ya auri Aunty Fadila ya bani, shiyasa ma zan ba ma Yaya K.B shawara tun wuri ya sauya ta don baza tayi daɗin zama ba idan ya aure ta, yana ji yana gani zata mayar da waya abokin rayuwanta ta ƙyale shi yay ta surutun sa..”

Kawo masa duka tayi dole yayi shiru yana matsawa gefe da sauri

“Wlh zan ɓalla ka a nan wajen; Ni sa’ar wasan ka ne Fadil?” Tafaɗa tana hararan sa cike da haushi

Baffa dariya yayi yace, “mai da wuƙan don Allah wasa yake miki”.

Ƙwafa kawai tayi ta juya ta buɗe ƙofan Part ɗin nasu ta shige, tana jin Baffa yana faɗin

“Babu sallama kuma zaki tafi?”

Amma bata jiyo ta kalle sa ba bare ta tanka masa

Su ma wuce wa suka yi suka tafi, Baffa na shan dariyan Fadil da yaci gaba da maganar Fadilan.

             ⚫⚫⚫

             08:45pm.

         Suna zaune su huɗu a kan dainning suna cin abinci, babu me magana cikin su sai ƙaran cokula da Plate da ake ji

Kansa na ƙasa yana cakalan abincin kamar bazai ci ba, rabi kuma hankalin sa naga wayan sa yana kallon wani abu da aka tura masa, har kowa ya miƙe suka bar sa nan zaune be ma san sun tashi ɗin ba

Parlour suka koma sukai zaman su, Big Dady da Hajiya suna taɓa hira while Yusra kuma ta mayar da hankalin ta kacokan kan Film ɗin da ake yi a Bollywood, Film ɗin زوجة زوجي searese

A hankali ya miƙe ya taho cikin parlour’n yana shirin wuce wa ɗakin sa

Dady ya tsayar dashi yana faɗin, “Fodio come here we’ll talk”.

Juyowa yayi ba tare da yace komi ba ya taho ya zauna kan One sitter dake Facing ɗin nasu Dady

Ɗan gyaran murya yayi yana kallon sa kafin yace, “gobe ne zaka soma zuwa Hospital ɗin ko ya?”

Cikin ƙasa da murya kamar wanda yake tsoron yin maganan yace “No .. until Monday”.

Jinjina kai Dady yayi kafin yace, “to har yanzu baka shirya aure bane? Tunda ga shi yanzu ka dawo gida Ya kamata ace kun ajiye mata kai da Baffa amma shiru har yanzu baka ce komi ba, kuma idan ban manta ba naji Baba yayi muku magana akan maganar auren ku”.

Shiru Usman yayi be ce komi ba, sai ma sad da kansa ƙasa da yayi

Su kuma sun zubo masa ido daga shi har Hajiya suna sauraron abinda zai ce

Yusra dake kallo ma hankalin ta na wajen

Girgiza kansa Dady yayi don yasan halin ɗan nasa, don babu wanda be saba da miskilancin sa ba

“Ya kamata dai kusan kun girma tun kafin mu ce zamu nuna fushin mu a kan ku ku fito da mata, don baza mu zira muku idanu kuyi yanda kuke so ba, ka tashi kaje Allah yayi muku albarka”. Dady ya sake faɗan hakan

Miƙewa yayi yana ɗan motsa bakin sa kafin ya nufi hanyan ɗakin sa

Su kuma suka rakasa da kallo har sanda ya gifta ta gaban su ya wuce

Ajiyan zuciya Dady ya saki yana miƙewa ya kalli Hajiya yace, “Let me in. I have a job.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button