SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Cikin zuciyar sa ya ke jimami sai dai bai bayyana ba ya ce ” ke mi ya hanaki auren? Karatu ki ke?”

Shiru ta yi ta juyar da kanta wajen glashi tana kallon waje.

Bai sake tambayarta ba yana dai sake karantar yanayinta. Sai da su ka iso ƙofar gidan su sannan ya miƙa ma ta wayarsa ya ce ” sa min numbar ki anan”

Kwarjininsa da girmansa shi ya hana ta mishi musu. Ta ƙarɓa wayar ta saka nambobin ta.

Miƙa ma ta kuɗi yai ta ƙi ƙarɓa.

“Kuɗin ƙitson da ki ka yiwa su Baby ne”

“Hajiya ta bani ai”

“Hajiya daban ni daban. Ki ƙarɓa ko na sa a kawo kyanwar gidanmu na ɗaure mi ki ita a ƙafa”

Ta ƙarɓi kuɗin ta ce ” na gode Allah ya saka da alkhairi” ya amsa da amin. Sai da za ta fita ya ce ” a samu a addu’a, Insha Allah anjima zamu hau hanya”

“Allah ya kaiku lafiya ya tsare mu ku hanya”

“Amin”

………………………

Su Faridah ba su dawo ba sai yamma lis, da su ka dawonma hidimar gida ya sa ba su zanta da mutuniyarta ba. Sai da ƙarfe goma ta gota na dare bayan ta gama goge doguwar rigar da za ta saka gobe sannan Maijiddah ta fara ma ta bayani.

“Anty Farida barin nuna mi ki wani abu”

Ta miƙa ma ta wayarta. Farida ta amsa wayar tana faɗin ” wannan tsohuwar wayar ta ki ma ya kamata ki chanja ta”

Alhamdulillah! ni da yara na mun sauka lafiya. Na gode da addu’arki gare ni
AbdulWahab Bello Hassan

“Weeeeeehuhu. Waye wannan dan Allah? ki ce addu’ar mu ta kusa karɓuwa”

“Kayya Anty, ɗan Hajiya Yelwa ne fa”

“Sai aka yi me. Abeg gist me, ya akayi ya samu numbar ki?”

Maijiddah ta labarta ma ta duk abinda ya faru.

“Ai Insha Allah mun sameshi ‘yar uwa ki dai cigaba da tashin dare da kikeyi. Allah ya kusa amsar addu’ar mu. Tukunna ke da me ki ka ma sa reply?”

“Ban ma sa ba”

” amma anyi ‘yar ƙauye anan”

“To Anty mi zan rubuta?”

“Mtsssw, give me the phone jooor”…

…………………….

Doguwar riga ta atamfa ta saka kalar atamfar ja ce da ratsin fari dan haka ta saka ƙaramin gyale fari. ‘Yar powder ta murza sannan ta goga jan janbaki kaɗan wanda ya ke ƙara haska fiskanta.

A karo na biyu Yakubu ya aiko ta fito shi zai tafi.

“Jiddah wannan yayan na kun ko”

Maijiddah dai sai dariya ta ke ma ta…

Su na tafiya Yakubu na ta yiwa Farida faɗa akan indai haka za ta dinga makarar da su to zai dena tafiya da ita kowa yai hanyar sa. “Haba Ɗan Musa, sai kace wanda mu ke aikin asibiti. Ban isa na fito ban karya ba, Allah na gani”

“Lallai kuwa, Sir Najeeb zai samu dalilin koran ki cikin sauƙi kenan”

“Ba Sir Najeeb ba Allah ya sa Sir Salihu ne”…

Office ɗin Anas ta fara zuwa dan ta gaishe shi ta samu cleaner tana shara.
Ta juya za ta fita sai ga Anas ɗin ma ya shigo.

“A’a ƙanwar mu ce da wurwuri haka, ashe da dai ba za kuyi faɗan latti da Ogan ki ba”

“Ina kwana Ya Anas”

“Lafiya Aisha Farida”

Bayan sun gaisa sannan ta wuce na ta office ɗin.
Nan ma ɗin ana kan gogewa ne hakan ya tabbatar ma ta Ogan na ta bai ƙaraso ba, ta zauna tana danna wayarta…

Cikin takunsa na ƙasaita wanda ke ƙara ma sa kyau da kwarjini ya shigo kamfanin na sa. Duk inda ya wuce gaishe shi ake yi sai dai fuskarsar nan mur ta ke balle ma asa ran zai amsa gaisuwar. Dama idan da sabo to sun saba. Sir Najeeb ba ya amsa gaisuwa.

Yana shiga lifter ya danna 3rd floor wanda nan ne za ta sada shi da office ɗin sa.

Ya ma manta batun yau sabuwar sakatariyar sa za ta fara aiki dan haka kai tsaye ya shiga office ɗin, sai dai tundaga bakin ƙofa muryarta ya fara dokan kunnensa.

“No it cant be her” ya faɗi lokacin da ya tako cikin office ɗin. Sai dai itan ɗin ce dai ya gani, ba ta san ya shigo ba saboda hankalinta na kan wayar da ta ke yi.
Ƙanshin turarensa da ya cikata ne ya sa ta ɗago da idon ta.

“And who are you?” Ya faɗi yana ƙare ma ta kallo.

” The new secretary” ta amsa ma sa

” This is bullshit” abinda ya iya faɗi kenan ya nufi hanyar office ɗin sa.

Tunaninta baƙon Oga ne dan haka ta yi saurin tsaida shi. Cikin bayanin da Anas ya ma ta. Bai kamata wani ya shiga office ɗin Oga ba tareda izininta ba.

” Mr Arab you cant enter the office, my boss is not around” ta faɗi da ƙarfi.

Tsayawa yai da buɗe ƙofar Office ɗin ya juyo ya kalleta, lokacin ta baro wajen kujeran ta ta nufo shi.

” you can seat and wait for him there” ta nuna ma sa kujeran da baƙi za su zauna Idan sun zo.

Ƙura ma ta ido yai, itama idon ta na cikin na sa. Hazel eyes na shi ta ke kallo wanda ya sa ta ji wani kasala nan da nan ta yi saurin ɗauke na ta idon. Ta yi gyaran murya sannan ta ce
” please go and wait for him”

Girgiza kai yai ya sa hannu zai buɗe ƙofar Farida ta yi saurin buge hannun sa ta shiga gaban sa ta stretching hannayenta tana tare ƙofar da su. “Dan Uban ka, dan kana balarabe sai ka ce ba za ka bi doka ba, to ba ka isa ba”
Idonsa ne su ka firfito lokacin da ya ji abinda ta faɗi.

Ta kalleshi ta ce ” you will not enter this office. Anta La adkul…..a’a ba haka bane, Anta La Tadkulul Bab…. mtsww, yau ga ranan zuwa Islamiyya nan, ni Aisha ɗan Larabcin ma ta gagareni”

Hannu ya sa a aljihu ya zaro waya ya kira wata number, ana ɗaga kiran ya ce da kakkausar murya “Come to my office now”

Mamaki ne ya mamaye fiskan Farida lokacin da taji abinda ya ce sai dai ta dake a wajen ba ta matsa ba.

Suna tsaye a haka Anas ya shigo. Ganin yadda Farida ta yi kane-kane a bakin ƙofar office ɗin Najeeb ya sa shi fashewa da dariya.

“Tell this crazy girl to get out of my way” Najeeb ya faɗi cikin tsawa.

Anas ya dubi Farida wanda jin abinda Najeeb ya ce ya sa jikinta yai sanyi, ta sauke hannayenta amma ba ta matsa a bakin ƙofar ba.
Ya ce ” Aisha ya ki ka hana Ogan na ki shiga office? ko salon na ki aikin kenan?”

“Ya Anas ni ban san shi bane ai. Akace sunan Oga na Najeeb Jibo, kuma na ga wannan balarabe ne. Suna Jibo kan ba na fulani ba ne?”

Anas ya fashe da dariya ya ce ” kuma da gaskiyan ki fa. Sai dai wannan bafulatanin ruwa biyu gareshi, ruwan fulani kuma ruwan larabawa”

“Ya Anas ina dai ba ya jin Hausa?”

“Hausa kai, hausa kamar Jakar Kano ma”

“Shikenan ni Aishatu, daga fara aiki har na tafka katoɓara”

“Fatan dai ba ki zage shi ba?”

A sanyaye ta ce ” sai dai gobe kar a ƙara”…

“Barin ji mi Ogan zai ce” Anas ya faɗi tareda shigewa office ɗin Najeeb. Dama tuni Najeeb ya shige ya barsu su.

Yana zaune kan kujerar sa ya na kallon ƙofa lokacin da Anas ya shigo.

” lokacin da na ce ka nemo min secretary, ban ce ka nemo mahaukaciya ba. She’s fired, find another one” abinda ya faɗi kenan lokacin da Anas ya ƙaraso wajen sa

Maimakon Anas ya bashi amsa sai ya sa dariya har da riƙe ciki.

“This not funny, da na yi aiki da wannan gara na dawo da Joseph”

Har lokacin Anas bai bar dariya ba, sai da yai mai isar sa sannan ya zauna ya kalli Najeeb da ya cika yai fam.

“First of all Aisha ba mahaukaciya ba ce, secondly, a iya sanina da Najeeb na san girman kan sa ba zai taɓa bari ya dawo da Joseph ba. Thirdly idan ka kori Aisha, kai za ka ɗau nauyin neman wata ko wani da kan ka. Aisha ƙanwar Architect Yakubu Musa Wase ne, and as far as i know Yakubu is like a brother to me dan haka ƙanwarsa ƙanwata ce”

“Wow! Ban san ka fara kalen dangi ba ai”

“Ni ma kuma ban san ka fara tsoron mata ba”

“What do you mean?” Najeeb ya faɗa a fusace

“Na san ka gane Aisha ita ce yarinyar da ta tada hayaniya a restaurant ranan. Shi ya sa ka ke tsoron aiki da ita”

“Tsoro?” Ya furzar da iska daga bakin shi sannan ya ce ” i’ll give her a chance, idan ba ta iya aiki ba zan koreta. And i dont care who’s sister she is”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button