SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

………………….

Wacece Aisha Farida Salihu?

Malam Salihu ɗan ƙaramar hukumar Wase ne da ke jahar Plateau. Sai dai tun yana ɗan shekara sha takwas da ya ƙare sakandare ya dawo cikin Jos da zama. Sana’ar sai da kayan gwari ya fara kuma Alhamdulillah yana samu. Su biyar ne a wajen mahaifin su wanda ya jima da rasuwa tun yana shekara bakwai a duniya, shi ne na huɗu a gidan kuma su biyu ne maza. Babban yayansu Musa shi yana Kano inda yake kasuwancin sa acan sai yayun sa mata Halimah, Asma’u da ƙanwar sa Fatima, wanda a lokacin duka sun yi aure Shekarar sa biyar a Jos yai aure.

Aminah ‘yar Jos ce domin iyayen ta anan su ke da zama tun shekara da shekaru sai dai asalin su Fulanin Dukku ne da ke Jihar Gombe.
Shekarar Aminah shabiyar aka yi auren wanda a lokacin JSCE kawai ta kammala. Suna zaune da Salihu lafiya cikin so da ƙauna har wata takwas kafin mummunan ala’amari ya faru. Tana zaune ta shirya abincin rana ta tsara kwalliya tana jiran sa, saboda ko yaushe Salihu a gida ya ke cin abincin rana, taji sallamar mutane daga waje. Ta sa mayafi ta fita inda taga Alhaji Nuhu ne wanda su ke haya a gidan sa da kuma Yusufu wanda rumfar sa ke kusa da na Salihu a kasuwa. Yanayin su kaɗai ya tabbatar ma ta akwai matsala. A hankali Alhaji Nuhu ya sanar ma ta Salihu ke asibiti ya yi hatsari. Cike da tashin hankali ta bisu asibitin inda Salihu ke kwance rai a hannun Allah. Da asuba Salihu ya cika wanda sanadiyyar haka ya sa Aminah suma. Da ta farfaɗo ma dai rikicewa ta yi wanda da ƙyar Nanna wato mahaifiyar Aminan ta shawo kan ta. Sai da aka yi bakwai ɗin Salihu Nanna ta fahimci Amina ciki gareta wanda ko Aminan ba ta san da shi ba. A hankali Aminah ta dinga renon cikin ta wanda Inna mahaifiyar Salihu ta ke matuƙar farin ciki da cikin. Tsakar daren ranan Alhamis Amina ta tashi da naƙuda,aka kira wata nurse da ta ke ƙasan layin su, zuwa asuba ta haihu, ta samu ɗiya mace. Aisha Farida aka sa ma ta saboda sunan da Salihu ke cewa zai sawa ‘yar sa ta fari kenan saboda sunan innar sa Aisha ya ce zai haɗa da inkiyar Faridah.

Amina ta cigaba da renon Aisha Farida a gidan su. Tana son ɗiyar ta sosai, ko kaɗan ba ta ma ta karan ‘ya’yan fari irin na fulani. Shekarar Aisha Farida biyu da rabi Baba ya fara yiwa Amina maganar aure saboda a lokacin akwai manema dayawa da suke son ta. Duk ciki ba ta da zaɓi dan ita tun Salihu ba ta kuma sa soyayyar wani namiji a ranta ba. Cikin maneman ta Baba ya zaɓa ma ta Malam Haruna wanda shima mutumin Dukku ne yana ɗin ki a Terminos. Matar sa ɗaya da yara shida. Lokacin da Amina za ta tare Inna ta so a bar ma ta takwarar ta sai dai Amina ta nuna batason hakan dan a ganinta Farida ta yi ƙaranci a raba ta da uwarta. Ba laifi Haruna na ƙoƙarin nuna adalci tsakanin matansa sai dai Laraba sam ba ta da haƙuri kullum cikin tsangwaman Amina da ‘yarta ta ke yi. Amina za ta lamunci komai amma idan akan Farida ce to ba za ta bari ba. Watarana Amina ta dawo daga unguwa lokacin watan ta takwas a gidan ta samu Laraba na dukan Farida tsabar wahala sai da yarinyar ta suma amma haka Laraba ta cigaba da jibgar ta. Da gudu Amina ta yi kan ‘yar ta tana ihu. Daga asibiti dai Amina gidan su ta wuce ta yi yaji. A ranan Haruna ya zo biko sai dai ta nuna ma sa matuƙar za ta zauna da shi to dole ne ya raba mu su gida. Yai-yai da ita ta ƙi chanja ra’ayinta, daga baya ya yarda da hakan. Har ya kama ma ta haya ɗaki ɗaya a wani gidan haya a tudun Fera. Ana saura kwana ɗaya tak ta tare saboda har an je an jera ma ta kayanta sai ga Haruna ya zo neman ta da yamma, ta fita ta sameshi a ƙofar gida. Bai amsa gaisuwarta ba ya damƙa ma ta takardar saki ɗaya. Ba dalili ba komai. Ƙarshe dai yadda aka je aka jera kayanta haka aka dawo da su gida. Ta ƙare iddar ta ta cigaba da zaman gida. Da tanada hali ma makaranta za ta koma sai dai iyayenta ma su ƙaramin ƙarfi ne. Kuɗin makarantar Farida. Baffanta Musa ke aikowa tareda kuɗin buƙatunta duk wata, ya so ya ɗauketa sai dai Amina ta ƙi musamman da ya maida Inna zuwa gidan sa a Kano.
Ganin zaman gidan shiru ya sa ta fara yin su kunun zaƙi da zoɓo tana siyarwa. Shekararta ɗaya tana zawarci Ibrahim ya fito neman ta shima dai yanada mata, ba ta bashi dama ba sai dai ganin Haruna ya dawo yana son maida auren su ya sa ta yi saurin amincewa da Ibrahim. Haruna yai nadamar sakin ta acewar sa bai san ya akayi ya saketa ba.

A Saminaka Ibrahim ya ke da zama da shi da matarsa da yaran su uku. Watannin farko an tafi lafiya-lafiya sai daga baya Matar sa Kubura ta fara nuna halin muguntar ta, ƙarshe sai raba mu su gida Ibrahim yai Lokacin Amina na laulayin ciki. Sai da su ka raba zama Amina ta samu sakewa ita da ‘yar ta. Da cikin ya cika wata tara Amina ta haifi ɗa namiji. Hakan ya farantawa Ibrahim rai saboda yaran Kubura duka mata ne. Wannan haihuwar ya jawo Kubura ta sake jin tsanar Amina. Da daɗi dai ba daɗi su na zaune har Faruƙ ya shekara biyu. Kasancewa abubuwa sun fara ja baya wa Ibrahim ya sa su ka bar gidan haya su ka koma gidan sa. Zama tareda Kubura dai sai ma abin da ya ƙaru.

Watarana Farida da Safiya ‘yar Kubura su ka yi faɗa. Kubura na kitchen ta ji kukan Safiya aikuwa ta fito da gudu, ba tareda bin bahasi ba ta kama jibgar Farida daga ƙarshe ta kaita kitchen ta sa wuƙa a cikin wuta sai da ta yi jaa sannan ta cire ta manna a bayan Farida. Farida ta calla ihu wanda Amina da akewa kitso a makwabta sai da ta ji kukan ‘yarta. Da gudu ta sa hijab ta taho gida inda ta samu har lokacin Kubura ba ta cire wuƙan da ya ke kwance a bayan Farida ba har wajen yai rami, tsabar wuya tuni Faridan ta suma. Amina ta yi kan Kubura ta kama ta da faɗa wanda a sanadiyyar kokawa da sukayi Amina ta rasa cikin ta. Wannan ya sa Amina ta nemi saki a wajen Ibrahim. Duk wani magiya da roƙo ya yi amma ta ƙi yarda ƙarshe cewa ta yi idan bai saketa ba da shi da matar sa za ta shigar da su ƙara a kotu na zubewar cikin ta da kuma ƙunar da Kubura ta yiwa Farida. Dole haka Ibrahim ya saketa ba tareda ya so ba. Ba ta bar ma sa Umar Faruƙ ba ta ce idan ya cika shekara uku za ta bawa ƙanwar sa Sadiya da ba ta jima da aure ba. Hakan kuwa aka yi dan Amina da kanta ta kai Faruƙ wajen Sadiya da ke aure a Kaduna. Ta ce ma ta madamar Ibrahim yana tareda Kubura bata yarda ta mayar da Faruƙ Saminaka ba.

Aikin cleaner Amina ta fara a wata private school da ke anguwar su. Inda anan ta saka Farida. Dalilin Farida ta haɗa Amina da Alhaji Kabir mai makarantar. Wata rana ta yiwa wata ‘yar ajin su duka iyayen yarinyar su ka kawo complain makaranta. Da komai ya lafa Alhaji KB ya kira Amina ya fara ma ta faɗa akan rashin ƙwaɓar Farida da ta ke wanda hakan ya jawo Farida ta zama ba ta jin magana. Amina ta sa kuka tareda cewa tunda kallon da ake yiwa ‘yarta kenan za ta cire Farida a makarantar. Alhaji KB da ya ke da tausayi ya fara bata haƙuri. Daga ranan su ka fara mutunci, watarana da ya ji tarihin rayuwarta ya ce ma ta mi zai hana ta koma makaranta. Ta ce za ta so hakan amma yanzu kam ba hali sai dai gaba. Alhaji KB ya ce ma ta idan ta samu mai taimaka ma ta zata koma? Amsar da ta bashi ya sa zuwa sati biyu ya samo ma ta form ɗin SS1 a wani makarantar gomnati. Da farko ta ƙi sai dai daga baya data yi shawara ta amince. Ta dena aikin cleaning ta koma makaranta. Bayan shekara biyu lokacin tana SS2 Alhaji KB ya bayyana manufar sa. Da farko ta ƙi shi daga baya ta amince amma da sharaɗin ba za ta zauna da matarsa ba. Sai a lokacin ya tabbatar ma ta shekara huɗu da rasuwar matar sa kuma basu taɓa haihuwa da Ita ba har ta rasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button