SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Daga office maimakon ta wuce asibiti kaman yadda ta saba sai ta wuce gida. Tasallah ta samu a falo tana goge-goge ta tambayeta ko Daddy na gida ta ce ma ta yana nan. Kai tsaye sama ta haura ta wuce falon sa. Da sallama ta shiga falon ya amsa ma ta yana kora ruwa, da alama magani ya sha dan ga tulin magani a gaban sa.

Sai da ta gaishe shi sannan ta ma sa ya jiki. Ba ƙaramin zabgewa yai ba, to ba dole ba shalelen ɗan sa yana kwance a asibiti shi da mai mutuwa banbancin su kaɗan ne.

“Aisha ya aikin?” Ya katse shirun na su

“Alhamdulillah Daddy”

“Allah ya taya ki riƙo” ta amsa da amin.
“Ki na cin abinci kuwa? na ga kin rame”

“Ina ci tareda Sir Najeeb mu ke ci”

Daddy yai shiru bayan yai addu’an Allah ya bawa Najeeb lafiya.

“Aisha, Anas ya zo wajena ɗazu da rana kuma ya min wassu bayanai, na saurare shi kuma na fahimce shi. A wani ɓangaren kuma ke ma na fahimci inda ki ka dosa. Alhamdulillah dukkan ku manufar ku ɗaya ne, sai dai ra’ayin ku ne ya banbanta kan yadda za ku cimma wannan manufa”

“Daddy zan haƙura idan ka ce na haƙura amma gaskiya ba zan cigaba da zama a matsayina ba bayan hakan”

” ba zan ce ki haƙura ba amma ina da tambaya. Idan da ace Najeeb ne a wannan yanayi ki na ga zai shiga gasan nan ko ba zai shiga ba?”

“A sanin da na yiwa Sir Najeeb Wallahi zai shiga gasan nan”

Daddy ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ce ” ki je ki yi abinda ki ka ga Najeeb zai yi, Allah na tareda ke. Idan ki na buƙatan taimakona ko shawara kan wani abu feel free ki min magana yadda Najdah ta ke matsayin ‘ya ta haka na ɗauke ki”

Godiya ta ma sa sannan ta tashi ta shige ɗakin su. Ɗakin na nan yadda ya ke abu ɗaya ya rasa shine mazaunan ciki.

Tana tsaye gaban mirror ta rage kayan jikin ta tana kallon yadda ta rame ta yi baƙi.

“Aysherh ba na son ƙazan ta” ta ji muryan Najeeb a bayanta. Ta juyo ta ɗan harareshi ta ce “ni ba ƙazama ba ce”
Sunkuyo da kan sa yai ya shinshina gashin ta sannan ya ɗago yana fifita hanci yana faɗin ” kin san ba na son wari Aysherh”

Ta juyo a harzuƙe zata fara masifa ta ga wayam ba kowa. Dama idon ta ke ganin kamar Najeeb na wajen, abinda ke sa ta nishaɗi kenan saboda ganin Najeeb da ta ke yi a idon ta, koyaushe yana tare da ita.

Da sauri ta wuce banɗaki ta fara wanke gashin ta wanda rabon shi da ya ga proper wanki tun zuwan ta Jos. Ta shampooimg kanta tana dirje dattin gashin da na scalp ɗin ta. Da ta wanke kumfan sannan ta saka instant conditioner yai minti biyar kafin shima ta wanke, sai a sannan ta fara wanka da shower gel ɗin Najeeb mai shegen ƙamshi.
Lokacin da ta fito ita kan ta sai kan ya ma ta saƙayau. Bayan ta drying na shi da hand dryer sannan ta shafa ma sa leave in conditioner. Zama ta yi ta yiwa gashin twist manya guda takwas. Ta kalli kan ta a madubin ta ga ta yi kyau saboda rabon da gashin ya ga gyara tun tana Jos. Cikin ran ta tana faɗin ai dole Champ ya ce ba ya son wari, kan ta cikin wata biyu ban da ruwan alwala da kuma ruwan wankan tsarki bai ga ruwan wanki ba. Tana shiryawa Tasallah ta zo ta tambayeta ko ta kawo ma ta abinci ne yanzu. Ta ce ta haɗa ma ta za ta wuce da shi asibiti…

Lokacin da ta je asibitin ta samu likita na duba Najeeb.

“Ya jikin na shi?” Ta tambaya lokacin da ta ƙaraso.

Likitan ya amsa da sauƙi

Sai da Farida ta samu waje ta zauna sannan likitan ya juyo ya kalleta bayan ya gama duban na’uran da ke kula da Najeeb.

“Aisha, ki cigaba da addu’a amma halin da Najeeb ke ciki komai zai iya faruwa. Wassu kan ɗaukan shekaru ma su tsawo ba su farfaɗo ba wassu daga haka su ke mutuwa, wassu kuma idan sun farfaɗo ma za ka ga sun samu matsala da ƙwaƙwalwar su ko kuma ka ga sun…”

“Na sani likita, tunda Najeeb ya shiga wannan halin na fara karance-karance akan wanda su ka shiga hali irin na shi kuma na gane komai. Ina da yaƙinin cewa mijina zai tashi nan ba da jimawa ba. Zai tashi mu yi rayuwan aure mai cike da soyayya da ƙauna, zai tashi mu haifi ‘ya’ya kyawawa kaman sa, zai tashi ya kirani Mrs Jibo, zai tashi na nuna ma sa yadda na ke tsananin son sa” hawaye ya ƙwace ma ta.

“Ki yi haƙuri Aisha, Allah ya na tareda ke. Akwai wani likita da ke zuwa visiting doctor a nan kwanan nan ya dawo Nigeria kuma gaskiya ana yabon ƙwazon sa. Yana aiki ma da Dr Sajid so inaga idan ya zo gobe zai duba mijin ki. Mu ji wanni shawarwari zai bayar”

“Na gode Doctor amma idan ya zo ka kirani, zan so na ji mi zai ce da kunne na”

“Insha Allah zan kiraki” daga haka likitan ya fita.

Farida ta taso ta ƙarasa gadon Najeeb. Ɗankwalin ta ta cire ta kai gashinta dai-dai hancin sa ta ce “my champ na wanke gashin baya wari yanzu, ka ji ƙanshin sa. Do you like it?”

Ta sumbaci idon sa da ke rufe ta ce “ko za ka mutu a haka ba zan gujeka ba, zan jira ka. Zan cigaba da jiran ka har iya ƙarshen rayuwa ta. I love you, I love you so much. Ka tashi ka ji, ka tashi mu yi abubuwa, saboda kanada abubuwa ma su saka abubuwa kuma nima inada abubuwan da za su saka yin abubuwa. Ka tashi ka kissing ɗi na irin na ranan, ka tashi kamin tafiyar ka mai ɗaukan hankali ɗin nan. Ka tashi ka min dariyan ka mai daɗi”…

…………………….

Washe gari ta zo ta tarar da abun mamaki, tana office Mrs Comfort ta shigo wai Anas yana kiran ta ana meeting a conference room.
Ba tareda ɓata lokaci ba ta wuce hall ɗin. Tana zuwa ta tadda an cika, duk wani mai babban matsayi yana wajen, abun takaicin ma har da Sabreen.

Anas ne ya raising motion kan ƙin amincewa da yai da shiga gasar da Farida ta sa.
Zaro ido tai lokacin da ya ce ko ta janye gasan nan ko kuma ya ajiye aikin sa.

“Ya Anas ya za ka min haka?” Ta faɗa idon ta ya ciko da hawaye. Ba ta ɗauka abin zai kai haka ba. Jiya sun rabu da Daddy akan zai yiwa Anas magana to mi kuma ya faru.

Sabreen ta ce Anas ba zai ajiye aiki ba idan ya ajiye kuma za ta cire shares ɗin ta. Ta sake cewa Farida ta ajiye aikin ko kuma dukkan ma’aikata su yi yaji.

“Its your lost Farida, dont destroy my Noory’s company”

Sunkuyar da kai ta yi tanajin maganganun su. Ta jima a haka kafin ta ɗago, ga mamakin ta sai ta ga Najeeb yana kallon ta yana murmushi.

“Its not easy ko?, haka nima na ke fama da su, but you have to be strong, you have to stand by what you believe. Kin san ya akayi na gina wannan kamfani cikin shekara bakwai ta zama haka?”
Farida ta girgiza ma sa kai

“Saboda idan na sa abu a raina sai na ga na cimmaci na ke ajiyewa. Na gaya miki mi za su yi idan ki ka janye gasar nan?”
Ta ɗaga ma sa kai

“They will consider you weak and incompetence. Za su ce ki sauka daga matsayin ki za su ce ba abinda ki ka iya. Anas is good amma yana da tsoro da rauni. But you” ya nunata da yatsa “My Miss Salihu My Mrs Jibo My Aysherh ba ki da tsoro ba ki da rauni”

Firgigit ta yi lokacin da Anas ya ce ” muna sauraren ki Aysherh”

Tashi tsaye ta yi tana shanye duk wani damuwa da ke ranta.

“Ya Anas za ka iya ajiye takardar a wajen sakatariya ta, za ta shigo min da shi office. Sauran da za su shiga yajin aiki kuma Bismillah sai na ji ku. Ma su son bin bayan ya Anas kuma takardan ajiye aikin ku duk ku ajiye wa sakatariya ta”

Ta maida kallon ta ga Sabreen ta ce “ke kuma zan fi kowa farin ciki idan ki ka cire shares ɗin ki a wannan kamfani”

“Ga wanda ya goya min baya wajen ayi gasa kuma. Zan sa a ajiye box a ƙasa kowa ya jefa ƙuri’ar sa ciki. Ba suna za ka saka ba ko matsayi, kawai ka ɗau takarda ka rubuta i support ka jefa ciki. Na barku lafiya”
Daga haka ta ɗau wayar ta ta fita. Anas dai mutuwar tsaye yai a wajen. Hall ɗin ya kaure da kace na ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button