SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣5️⃣0️⃣

Tun daga wannan rana Naomi ta risina, tsoron Farida ta ke sosai. Ko office ɗin ta ta shiga za ta ma ta wani aiki ko za ta ba ta saƙo haka za ka ga jikin ta na rawa. Farida kam tana lura da yanayin Naomin sosai dan ta ga alama kaman tana yiwa Najeeb kallon so. Sai dai ganin ta dena shigar banza da kuma rawar ƙafa idan tana office ɗin sa ya sa ta ɗan ɗaga ma ta ƙafa. Ita ba dan tausayin Mrs Comfort da ta ke yi ba da tuni ta kori Naomi…

Tana zaune a falon ƙasa su na hira da Faruƙ wanda yazo hutu sai ga Najeeb ya sauko. Yau weekend ba su je aiki ba, sai da ya mannawa matar sa kiss a kumatu kafin ya mu su sallama akan zai je ya gaida Daddy wanda ke fama da ciwon ƙafa. Farida ta tashi ta raka Najeeb zuwa wajen mota.
Tana rungume jikin sa ta ce “za mu je gida anjima ni da Faruƙ”

“Kar ku daɗe plz kin san nima ba zan jima ba zan dawo”

Ta manna ma sa light kiss a lips ɗin sa. Shi kuwa ya rankwafo ya kissing cikin ta yana faɗin “baby, Daddy zai je gaida granny dont disturb your mom”

Farida ta yi dariya…

Kamar kowani zuwanta, yau ma maganar auren Ummi ta kuma yi wa Baffa Musa, wannan karan hatta Faruƙ sai da ya sa baki, shima ya nuna goyon bayan sa ɗari bisa ɗari.

“Baba idan ba ka amince ba Allah zan je Toro na ɗauko Abdul da Hamza su zo mu taru mu yi ta ma ka kuka har sai ka amince”

Baffa Musa yai murmushi ya ce “kin zama babbar banza kenan tunda yara na karatu za ki je ki ɗauko su”

Ta ɗan shagwaɓe fiska ta ce “Baba to ai duk cikin so ne”

Tafiyar su Farida ya sa Baffa Musa dogon tunani. Amina ta sha wahala da yaranta tun bayan rasuwan mijinta na ƙarshe. Da tana tareda iyayenta ne to yanzu kuma dukkan su biyu sun rasu, ita ɗaya za ta yi rayuwarta sai dai zama da yayyenta da matan yayyen. Yaranta ma ba sa kusa. Farida na nan Kano, Faruƙ na Kaduna. Sauran biyun suna boarding school a Toro sai hutu su ke zuwa gida.
Zai taimaka ma ta wajen haɗa kan yaran idan ya aureta. Kuma hankalinta zai kwanta idan tana kusa da ‘ya’yan ta. Da wannan tunani ya yanke shawaran tuntuɓar Aminan ya ji mi za ta ce.

Ranan Asabat ya je yai aski, ya zauna aka ma sa gyaran fiska. Ɗan tsoho mai shekara hamsin da takwas ya fito fes da shi. Ranan Lahdi da sassafe ya ɗau hanyar Jos. Yana tuƙi yana jin wani nishaɗi. Sabon kaya ya saka wanda cikin ɗinkin shi na sallah ne da bai sa ba. Shadda ce ash da ta sha aikin hannu mai kyau, ya ɗaura hular Zanna a kan sa wanda ya shiga da kayan…

Da ke Ummi ba ta san da zuwan sa ba, ta ma fita barkan suna chan ƙasan layin su lokacin da ya zo, Aliyu babban yayan su wanda shima ke zaune da iyalin sa a gidan ya kirata akan ga Baffan Farida ya zo. Sai da ta ji wani jim a ranta, ta dai amsa ma sa da cewa tana zuwa yanzu.

Baffa Musa kam tuni ya bayyanawa Aliyu buƙatar sa na son auren Amina. Yaya Aliyu ya nuna ba su da matsala da wannan infact su na murna da wannan haɗin. Kawai dai ita Aminan ne sai a hankali dan tun rasuwan Alhaji Kabiru ta ƙi aure fau-fau bayan kuma har yanzu da sauran ƙuruciyar ta…

Ummi ta shiga falon Yaya Aliyu da sallama wanda anan ne aka sauki Baffa Musa. Atamfa ce ajikin ta ɗinkin doguwar riga sai babban gyalen Khashka da ta yafa, hannunta ƙunshe da jan lalle.

Ta samu kujera ta zauna tana gaida shi a ɗan kunyace. Ta rasa dalili tun lokacin da su ka yi maganar aurensa da Farida sai ta ke jin kunyar sa.

“Amina” ya kira sunan ta ahankali.
Ta ɗan ɗago ido ta kalleshi kafin ta sauke.

“Lallen hannun ki yai kyau”

Ta maida hannunta cikin gyale tana wata munafukar murmushi ƙasa-ƙasa.

Shiru ne ya biyo bayan abinda ya ce kafin daga baya ya katse shirun da cewa “Amina na zo da ƙoƙon bara ne. Ina fata dai ba za a barni da ƙishirwa ba. Haƙiƙa ke mace ce ta gari, kin yi goggormaya da rayuwa kuma kin sha fama da jarrabawa kala-kala. A hakan kin nuna jarumta da bajinta mai ban mamaki. Ina neman alfarma da ki kasance cikin rayuwata. Mu haɗu mu rufawa juna asiri har iya ƙarshen rayuwar mu”…

Bayan ya gama bayanan sa Ummi ta ce ya bata lokaci ta yi tunani duk abinda ta yanke zai ji a wajen Yaya Aliyu…

Sati ɗaya da zuwan Baffa Musa Jos Yaya Aliyu ya kirashi akan Ummi ta amince za ta aureshi. Murna a wajen Baffa Musa ba a magana. Da ke abu ne da an riga an san juna sai abin bai ɗau lokaci ba. Bayan Baffa Musa ya tura magabatan sa. Yaya Aliyu ya sa biki nan da sati biyu…

……………………..

“My Champ kana ganin kuɗin nan bai yi kaɗan ba” Farida ta faɗa tana miƙawa Najeeb check ɗin da ke hannun ta.

“Make it 20” Abinda ya faɗa kenan.

Farida ta ƙarɓi check ɗin ta yaga ta ciro wanni ta sake cikawa, maimakon 15million da ta sa ɗazu sai ta mai da shi 20million.

Yau ta ke so ta je gidan Baffa Musa dan ta kai mishi.
Wayar ta ne ya fara ringing. Tana dubawa ta ga sunan Ummi. Ta katse kiran kafin ta sake kira.

“Farida wanni shirmen ne wannan. Ba ki da kunya ko”

Farida ta yi dariya ta ce “Ummi to za ki yi aure ba gyaran jiki ne?”

“Ungo na ki da gyaran jiki” ta faɗa tana kashe kiran.

Farida kam sai dariya ta ke. Matar da ta musu gyaran jiki ne ita da Najdah ta tura ma ta maƙudan kuɗi akan ta je ta yiwa Ummi gyaran jiki…

Yammacin ranan Farida ta je gida. Baffa Musa bai dawo daga kasuwa ba sai bayan Maghrib. Ta tsaya ta naɗi tuwon shinkafa miyan bushashshen kuɓewa da Baaba Sabuwa ta yi, dama wannan cikin mahaukacin kwaɗayi ya ke sata.
Bayan sallan Isha ta samu gamawa da Baban na ta.

Su ja gaisa ana ɗan raha sannan ta miƙa ma sa check ɗin kuɗin wanda ke cikin ƙaramin envelop.

Baffa Musa ya zaro ido ganin maƙudan kuɗin da ke jiki.

“Farida! Wannan yai yawa. A’a Farida” ya maida check ɗin cikin envelop ya miƙa ma ta.

Maimakon ta yi magana sai ta fashe da kuka.
“Farida lafiya?” Ya faɗa da ɗan damuwa.

“Baba sai ka ce wanda na baka kuɗin jini za ka maida min. Baba ba za ka samin albarka ba kenan? Mijina ya mallaka min kaso 25 na kamfanin sa, duk wata inada kuɗaɗe dayawa da ke shiga account ɗina. Idan ban kyautata ma ka ba ya zan yi da su? Ban taɓa ganin Baba na ba sai a hoto. Kai na sani a matsayin Uba, dan Allah ka sa min albarka”

Baffa Musa ya maida check ɗin cinyar sa yana sa ma ta albarka.

Bayan ya gama Farida ta ƙara ba shi wani abin mamakin ta hanyar gaya ma sa cewa mijin ta ya biya mishi Hajjin bana, ba shi kaɗai ba harda Baaba Sabuwa da Ummi. Ita Anty Wasilah da ke tana da tsohon ciki sai wata shekarar.

Baffa Musa ya ɗaga hannu sama yana kwararo addu’a wa marigayi ɗan uwansa, yanayi yana hawaye.
Faridan ma sai da ta yi kuka. Ba ta rayu ta ga wannan Bawan Allah ba amma duk wanda ya san shi har yau labarin kirkin sa ake ba ta. Tana fata su haɗu a Aljannah ta ganshi ya ganta…

Bayan sati biyu aka ɗaura auren Baffa Musa da Ummi bisa sadaki dubu Hamsin. Ba ta tare a lokacin ba sai bayan sati ɗaya…

Daren ranan Baffa Musa ya shigo ɗakin amarya wanda ya sha tsadaddun furnitures da Farida ta yiwa Ummin ta.
Ledar kazarta ya ajiye a centre table sannan su ka gaisa da amarya. Bayan sun yi sallan godiya anci kaza sannan su ka shiga raya dare. Baffa Musa round uku yai a wannan dare. Yai biyu a jere na ukun kuma ƙarfe huɗun asuba su ka yi shi. Amina ta na nan matse ga shi ta sha gyara. Ba ƙaramin daɗi ya kwasa ba. Itama Ummin ta ji daɗi sosai, shekaru takwas kenan rabonta da namiji. Ashe dai har yanzu tana buƙatar namiji dan sai ta ke jin duk wassu ƙofofin jikinta sun buɗe suna karɓan wannan ni’ima…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button