SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“What!”

Murmushin yaƙe yai tareda sa hannun sa a haɓarsa ya furzar da iska a hankali ya ce ” duk abinda ki ke tunanin samu a wajena ba za ki samu ba, nonetheless, i’m going to buy your shares. Now leave my office”

Murmushi ta yi ta ce ” I’m going to fight for us Noory”

Tana tashi za ta fita ita kuma Farida ta shigo. Kallon-kallon su ka tsaya yiwa junan su. Kafin Sabreen ta janye kallon ta hanyar saka baƙin glass ɗinta ta fice daga office ɗin.

Farida ta ce “kurwata kur mayya”

Ƙarasawa wajen Najeeb ta yi wanda ke waya da Anas yana surfa ma sa masifa, dama tunda ya zo ba su haɗu ba. Yana ajiye wayan Farida ta ce “Sir Najeeb, wannan list ɗin da ka ce na yi akwai sunayen da ba su yi dai-dai da na cikin database ɗin ba ya za ayi?”

“Just do it anyhow?” Ya daka ma ta tsawa.

Jikinta ne yai sanyi, Najeeb ɗin da ta sani ba zai yi tsawa dan ɗan wannan abin ba.

“Sir Najeeb saboda Sabreen shine za ka min tsawa” ta faɗa a hankali

“Get out Mrs Jibo”

Wannan karan da ƙarfinta ta ce ” Ba zan fita ba, ba zan fita ɗin ba. Ka gaya min matsayina? yanzu da wannan karuwar ta ka ta dawo, miye matsayina?”

Ɗago ido yai ya kalleta amma baice komai ba.

“Banda matsayi ko?, banda matsayin da ya wuce matsayin Sakatariyar ka ko?”

“Wanni matsayin ki ke so bayan wannan?” Ya maida ma ta martani.

“Amm…” sai kuma ta fasa maganar da za ta yi ta ce “na gode”
Juyawar da za ta yi ta ga Anas yana tsaye a wajen. Sauri ta yi ta bar office ɗin.

“Kai wanni irin mutum ne Najeeb, Farida matar ka ce fa yanzu”

“Sabreen ita ke da kamfanin SABNAJ”

“Wanni Sabnaj ɗin?”

“Kasan sarai abinda na ke nufi, also Sabreen wants to work here”

“shegiyar kuma ta nan ta biyo?”

” ba na son ganin Sabreen Anas”

“Its simple, ka siye shares ɗinta”

“Ta ƙi”

“Ka bar batun wannan, Najeeb yadda na sameku da Farida kwata-kwata bai dace ba. Kar ka manta matar ka ce fa”

“Matar da Dad ya sa dole na aura ba”

Anas ya harareshi ya ce “Matar da ka rusa shirin aurenta ba. I know you love her Najeeb, kar ka yi wasa da damar ka”

“Stop this nonsense Anas, ka san har yanzu ban yafe ma ka abinda ka yi ranan saturday ba”

“Ni dai na gaya ma ka” daga haka ya fita.

Samun Farida yai ta kwantar da kan ta a kan table tana hawaye.

“Farida” ya kira sunan ta a hankali.
Ta yi saurin ɗagowa tana goge hawayen.

“Dan Allah ki yi haƙuri”

Murmushin yaƙe ta yi ta ce ” ba komai Ya Anas, ni dai abu ɗaya na ke buƙata a wajen ka”

Zama yai a kujera dan ya saurareta da kyau.

“Sharrin da aka min a wannan kamfani har ya sa Sir Najeeb ya ke ganin baƙina, ina so na wanke kai na ko ta halin ƙaƙa. After that, zan bar aiki a nan”

“I’m sorry ‘yar uwa na ce zan sake bin bahasin case ɗin, abubuwa su ka shamin kai ban yi ba. But Insha Allah zan yi”

“Na gode”

“Farida” ya sake kiran sunan ta a hankali. Ta ɗago ta kalleshi.

“Najeeb na son ki farida, idan ki na son shi, ko da kaɗan ne, fight for him. Kar ki ga wai Sabreen ta dawo ki shiga ruɗu ko ki ɗauka shikenan ba ki da chance a wajen Najeeb. Ke ne ki ke da damar samun sa, har ki juyashi yadda ki ke so. But only idan ki ka cire shakka ko wani tsoro”

Maganganun Anas sun ba ta mamaki sosai, ta daure ta ce “Najeeb ba ya so na Ya Anas, ba zan iya ƙwallafa rai na a kan sa ba”

“Shikenan, ki zauna, ki zuba ido har Sabreen ta ci galaba akan ki. Idan hakan ta faru ina tabbatar mi ki da cewa ƙeyar Najeeb sai ya miki wuyar kallo”

Daga haka ya tashi ya fita.

Tunanin maganganun Anas ta shiga yi. Tana kokonton maganar amma wani ɓangare na zuciyarta na son gaskata hakan…

Ranan ba su dawo tareba saboda ta rigashi tafiya, ta barshi suna tattaunawa da Anas, ta san ba zai wuce akan fara aiki da Sabreen ta ce za ta yi da su bane.

A gajiye ta shiga gidan sai taga Sabreen da Mom su na hira a falo. Mom kawai ta gaisar ta wuce sama bayan ta aikawa Sabreen harara.

Tana ɗan jin ciwon ciki amma ba wannan ba ne a gaban ta yanzu. Mafita ta ke nema wa kan ta, ko da ba za ta samu Najeeb ba amma ba za ta bari Sabreen ta sameshi ba, dan Najeeb bai dace da karuwa ba. Ko yaushe ta fara damuwa da Najeeb oho…

As usual sai dare ya dawo, tana kwance akan gadon ya shigo. Ba ta kulashi ba dan ta kanta ta ke, tun da magriba ciwon cikin ta yai tsanani kuma ta duba ba ta da magani.

Bayan ya shirya ya sa Najdah ta kawo ma sa lemon tea. Ya zauna yana aiki a laptop yana sipping tea ɗin.

Tun ɗazu ta ke juye-juye a kan gadon bai lura da ita ba. Ta tashi zaune, ta yi rub da ciki, ta yi gotso duk saboda yadda ciwon mara da ciki ke jijjigata. Ƙarshe dai ƙasan gado ta sauko ta yi kamar sujjada tana ɗan jijjiga jikinta.

Ya gama abinda zai yi ya hau gado sai ya ga bai gan ta ba. Ɗazu dai ya gan ta a kwance kuma bai ji ƙaran buɗe ƙofar banɗaki ba balle yai tunanin wajen ta shiga. Ya share zancen ƙila kaya ta je chanjawa. Bai yi 5seconds da sake zancen ba ya ji nishinta.
Fara dube-dube ya ke har ya mirgino zuwa gefenta ya leƙa ƙasa ya ganta.

“Are you Ok?”

Girgiza kai kawai ta yi.

“Mi ya sameki?”

“Ina ruwan ka da ni. Ka damu da ni ne?”

Juyawa yai ya ƙyaleta.

Ta ɗan jawo pillow ta danne cikin ta da shi ta cigaba da nishi. Bata ankara ba sai ta ga ya kashe wutan ɗakin. Wani tuƙuƙin baƙin ciki ya zo ma ta har wuya, wato da gaske bai damu da ita ba.

“Wayyo Ummina, Wayyo Allah gatan marainiya. Wayyo Ummi”

Kunna wutar ɗakin yai ya tashi ya zo ya ɗauketa ya maidata kan gadon. Ya ce “mi ya ke damun ki?”

Ba ta kulashi ba ta cigaba da murƙusu a kan gadon. Lokaci guda ya tashi kaman an tsikare shi ya fita daga ɗakin. Minti biyar sai gashi ya shigo ɗauke da mug.

“Tashi ki sha magani”

“Ni ka bar ni, ka san abinda ke damuna ne?”

“Get up” ya faɗa da ɗan ƙarfi.

Ibrufen tab ya miƙa ma ta tareda ruwan ɗumi, ta amsa ta sha.

Ya ce ” ki shanye ruwan”

Ta cigaba da shan ruwan ɗumin har ya ƙare. Ta miƙa ma sa mug ɗin ya karɓa ya ajiye a saman bedside drawer.

“Kwanta”

Kwantawa ta yi da bayan ta tana kallon idon sa. Rigan baccin da ta sa riga da wando ne masu laushi, wandon iya gwiwa ya ke.
Hannu ya sa ya kamo ƙafafuwanta biyu. Ta challa ƙara ” Sir Najeeb me ka ke shirin yi?”

Wanni kallo ya watsa ma ta ta yi shiru. Ƙafafuwanta ya kama sannan ya tanƙwasu ta yadda cinyoyinta sai da su ka taɓa cikinta gwiwan kuma na taɓa nonuwanta. Ya sake stretching ƙafafun sannan ya sake tanƙwasasu. Haka ya ke yi har sai da yai kaman sau goma sannan ya sauke ƙafafun, ya sake ɗaga ƙafa ɗaya ya tanƙwasashi gefe. Ƙafar ta yi kaman triangle, sannan ya tanƙwasa ta koma ɗaya ɓangaren haka yai ta yi har sau goma sannan yai wa ɗaya ƙafan ma haka. Hannu ya sa zai ɗaga hips ɗin ta sama Farida ta yi saurin cewa “Sir Najeeb ina abu fa, kuma ba a abu idan ana abu”

Ya gimtse dariyar da ta zo ma sa ya ce ” Bakin ki ne abu ai, ni ma ba na abu idan ba na so na yi abu musamman ma da wadda ba ta da abu”

Ya tallafo hips ɗinta ya ɗan ɗaga sama sannan ya mai da su ya sake ɗaga su a haka sai da yai sau goma.
Yana sake wani form of stretching ɗin ta yi saurin cewa ” Sir Najeeb ka yi a hankali wandona zai yage”

Tsayawa yai yana kallon ta. Sometimes yana mamakin wai yarinyar nan ta yi makaranta. Most at times tana yin wassu abubuwan kamar ‘yar ƙauye.

Sai da ya gama yi ma ta yoga dan ta samu relieve sannan ya kashe wuta ya kwanta.
A cikin duhun Farida ta dubi gefen sa ta ce “Sir Najeeb ya aka yi ka iya wannan abin, Allah na ji sauƙi sosai”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button