SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Yana cikin wannan bulayin Sabreen ta buɗe ƙofa ta shigo. Ƙaran tafiyar ta ya ji ya gane ita ce.

“What do you want?”

“Noory i’m sorry”

Wani dariyan takaici yai ya ce ma ta ” in 8yrs 2 months 11days ba abinda za ki ce sai I’m sorry? For kin maida ni mahaukaci ko”

“Noory” ta faɗa tana matsowa kusa da shi

“Go back to Hollywood” ya faɗa da ƙarfi

“I’m here to stay Noory, for you, for us”

“You’re Crazy Sabreen”

Kuka ta fara mi shi tana faɗin cewa tana son shi har yanzu kuma ba ta taɓa dena son shi ba. Rasa ma mi zai ce ma ta yai ya fice daga ɗakin ya barta. Ba zai iya tsayawa a gidan ba, not after all that happened.

Ranan dai wannan dinner ta zama wani iri, an dai ƙarasa da ƙyar, wanda su ka kawo gifts wa amarya da ango sun miƙa. Daddy da su Uncle Sulaiman sun jima suna tattaunawa gameda zuwan Sabreen kafin daga baya kowa ya watse.
Da ƙyar Farida ta kai kan ta ɗaki dan gaba ɗaya ta shiga wani yanayi na ruɗu. Sabreen ta dawo, macen da Sir Najeeb yai dakon rashinta har shekara takwas, macen da Anas ya ce ma ta ita Najeeb ya fara so kuma ya so ta so mai tsanani. Idan Sabreen ta dawo miye amfanin zamanta tareda Najeeb tabbas nan ba da jimawa ba zai sallameta ya auri Sabreen. Ta jima tana zaune akan gado tana tufka da warwara kafin daga baya ta tashi ta shiga banɗaki dan ta watsa ruwa…

Daddy yai ta kiran Najeeb amma ba ya shiga. Ya na son ma sa magana akan zuwan Sabreen dan ya san halin ɗan na sa. Daddy ba zai iya ƙin karɓan baƙuncin Sabreen ba saboda kamar ‘ya ta ke a wajen matar sa.

Najeeb gidan sa ya je ya kashe wayoyin sa ya kwanta, ba wai bacci ya ke ba, ya kwanta ne yana tuno abubuwa dayawa da su ka faru musamman soyayyar sa da Sabreen. He gave her all his heart, he loved her with every beat of his heart. Ya ma ta alƙawarin samun rayuwa mai kama da aljannar duniya idan su ka yi aure amma…

Ranan bai koma gida ba dan ba ya son sake ganin Sabreen saboda yadda ya ke ji a zuciyar sa. Farida kam bacci ƙaurace ma ta yai. Makomarta ta ke nema a wannan lamari, idan tana ganin za ta iya samun soyayyar Najeeb to yanzu kam chances ɗin ta ya bouncing back to zero.
Sabreen ta maimaita sunan a karo na ba adadi…

……………..

Washegari Lahdi Farida ba ta tako ko ƙofar ɗaki ba, a ɗaki ta wuni Adama ce ta ke kawo ma ta abinci har ɗaki, wanda abincin ɗan tsakura kawai ta ke iya yi. Rashin kwanan Najeeb a gida ya tabbatar ma ta nata zancen ya kaɗe domin ta san yana chan yana kitsa yadda zai yi aure na gani na faɗa shi da Sabreen.

Ga mamakin ta ƙarfe tara na dare sai ga shi ya shigo ɗakin, bai ce ma ta komai ba ya je yai wanka ya shirya cikin ɓakin pyjamas na shi ya kwanta.

Daga inda ta ke zaune ta ce “Sir Najeeb miye matsayi na yanzu?”

Bai kulata ba, shi idan ba dan Daddy ya ce lallai ya dawo gida ba da bai san ranan da zai dawo nan ba. He feels empty.

“Sir Najeeb magana na ke”

“Oh please Aysherh” ya faɗa ba tareda ya realising da sunan ta ya kira ta ba

Jin sunan ta for the first time a bakin sa sai ta tsaya ta na jin yadda sunan ke ringing a ƙwaƙwalwarta Aysherh Aysherh Aysherh

Ringing ɗin wayar ta ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, ta yi saurin zuwa ta ɗauki wayan sai ta ga Sister Munibat. Ta ɗauki wayan su ka gaisa, jin muryan ta kaman tana kuka ya sa ta tambaya ko lafiya. Sister Munibat ta sanar da ita mahaifinta ne ya rasu ta gayawa Sir Najeeb ba za ta zo aiki ba ta ɗau hutun sati ɗaya.

“Allah ya jiƙan sa, kar ki damu Sister zan faɗa ma sa. Daga satin nan ma za a shiga hutun ƙarshen shekara so kar ki damu. Allah ya ma sa rahama”

Da ta gama wayar ta fara gayawa Najeeb ko ya ji ta ko bai jita ba oho, dan bai amsa ba.

………………..

Yau ma Mom ce ta kaita wajen aiki dan Najeeb tun ƙarfe shida ya fita. Su na tafiya tana ba ta haƙurin zuwan Sabreen tareda ma ta alkawarin duk yadda za ayi sai ta sa Sabreen ta koma inda ta fito.
Farida ta tambayeta ko miya sa ta ke supporting ɗin ta ba Sabreen ba. Mom ta ce “saboda Sabreen is his past, ke ce present and future ɗin sa” da wannan ya sa Farida ta ɗan ji sanyi a ranta…

Tana aiki a laptop Sabreen ta shigo office ɗin ta still cikin shiga mai ɗaukan hankali.

Cewa ta yi za ta ga Noory. Farida ta haɗe fuska tana jin haushin sunan da Sabreen ke kiran Najeeb da shi.

“Sabreen ki ke ko Siren ne?Najeeb zaujy, Ana Zaujy Najeeb” ta faɗa tana nuna kan ta.

Sabreen ta kwashe da dariya saboda shirmen larabcin da Farida ta yi. Ta san da zancen auren Najeeb kuma ta san wanda ya aura, but seeing Farida ya sa ta ƙara yarda Najeeb ba auren son ran sa yai ba, saboda Farida ba ta dace da irin matan da Najeeb zai so ba balle har yai tunanin yin rayuwa da su.

“Fuck off girl, i have his heart”

Tana faɗin haka ta shige office ɗin Najeeb.

“Shegiya karuwa” Farida ta faɗa tana tsaki…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣2️⃣8️⃣

a star is never perfect and the villain is not always that bad

Ya riga yai nisa cikin tunani lokacin da ta shigo sai da ta kira shi sannan ya ɗago ido ya kalleta. Farin idon sa ya koma ja saboda rashin bacci da damuwa.

“Noory” ta sake kira da murya mai jan hankali

“Leave” ya daka ma ta tsawa.

Ba ta damu da abinda ya ce ba, ta samu kujera ta zauna.

“I’m here to stay Noory” ta faɗa tana ƙanƙanta ido kamar za ta yi kuka.

A da wannan muryan yana raunata shi, a da wannan murya yana ratsa duk jikin sa ya bi kowanni jijiya na jikin sa, a da wannan murya yana sa shi jin wani farin ciki mai wuyar bayyanawa.

“Look, ban san mi ya dawo da ke ba, kuma ba na so na sani, ko ma minene ina so ki sani cewa you’re not welcome”

(Maganansu ingautsan Larabci da turanci su ke. And ni kuma????)

“Noory listen to me please, i love you, i still do”

“Get out”

“Noor…”

“Get out of here”

Ta san za a yi haka shi ya sa ta zo da shirin ta.

“Ba za ka iya korata ba”

Kallon mamaki ya ma ta at the same time sai maganan ta yai kama da abinda Farida za ta ce.

“Ina da 6% shares a kamfanin nan”

“6%” ya maimaita sannan ya sa dariya, tsayawa yai da dariyan lokacin da ta ce “SABNAJ Inc.”

Farkon buɗe kamfanin sa kafin ta gama zama da ƙafarta, ya saida kaso ashirin da biyar a matsayin hannun jari ciki kuwa har da Sabnaj inc. Ya tuna lokacin kamfanin ta so siyan kaso shabiyar ne amma ya ƙi, daga baya aka koma kaso goma har kuma daga ƙarshe aka tsaida matsaya akan kaso shida. Abinda ya sani shine Sabnaj inc wata kamfani ce a ƙasar America.

“Yes Najeeb, i owned sabnaj”

“SABNAJ” ya furta a hankali. Sunan da su ka shirya sa wa kamfanin sa kenan kafin komai ya wargaje tsakanin sa da Sabreen.

“Sab for Sabreen and Naj for Najeeb. Do you still remember?”

Ta ya bai yi wani ƙwaƙwƙwaran bincike ba a lokacin har ya sayar da shares ɗin kamfanin sa ga Sabreen. Ko lokacin da kamfanin Sabnaj ta zo neman saka hannun jari bai yi niyyar karɓan su ba saboda yadda sunan kamfanin ya ke. Anas shi ya convincing ɗin sa akan ya amince mu su.

“Ina son na yi aiki a nan Noory, ina so na yi aiki kusa da kai. Na ɗau hutun acting na shekara biyu just to be with you. Na san kamfanin ka ta samu koma baya cikin watannin nan, i’m here to help”

“Nawa za ki sayar da shares ɗin ki?” Ya faɗa with serious face

“Ba zan sayar ba, i want to be with you”

“Miss Sabreen. Welcome to Najeeb constructions then”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button