SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

” da kin rufawa kan ki asiri kin bar aikin nan da zai fi mi ki, dan ni Khalidah sai na sa Najeeb ya kore ki daga aiki”

“haba Anty! daga zuwa na. Ba ga ruwa balle ya hanya?” Farida ta faɗi tana farfari da ido.

Khalidah tai tsaki ta tafi…

“Sir Najeeb Ina kwana” ta faɗi lokacin da ta shigo office ɗin sa. Bai ce komai ba bai kuma ɗago ba.

“Miss Salihu you are late”

” na san ba ka son latti Sir, a min afuwa na yau ne kawai”

Sai a lokacin ya ɗago idon sa ya kalleta.
Shigar riga kalar maroon ta yi sai wando kalar ash da jacket shima kalar ash, ta yi ɗaurin turban da ɗankwali kalar maroon.

“Sir Najeeb ka gama kallon da kyau. Duk haɗuwar da na yin nan gwanjo ne ajikina, grade one ma kuwa. Kuma akwai irin su-irin su da na saro ko da za ka ɗaukawa ƙanwar ka ko…”

“Miss Salihu, go back to your office” ya faɗi yana sauke idon sa

“Haba Sir, ba sannu, ba ya jiki, ba…”

Wani file ya miƙa ma ta ya ce ” ina son aikin nan cikin minti goma”

Ƙarɓan file ɗin ta yi a hannunsa tana kumbure-kumbure har ta fice daga office ɗin…

????SAKATARIYA TA????
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Free page

0️⃣1️⃣1️⃣

A kishingiɗe ta ke a kan kujerarta bacci ya sace ta. Tun ƙarfe goma da ta gama aiki ba abin da ta ke yi, chatting ta ke yi a waya baccin ya sace ta.

“Miss Salihu…Miss Salihu” ta yi firgigit ta farka. Kallon sa ta farayi tana murza ido.

“Biyo ni”

Kafin ta wartsake ta tattara office ɗin tuni ya fita.
A hawa na farko ta sameshi yana yiwa wasu bayani. Anas ne ya ce ma ta yana ƙasa, dan da ba ta san inda yai ba.

Tana tsaye tana ƙoƙarin saita kan ta saboda har lokacin ba ta gama wartsakewa ba ta ga yai hanyar parking lot na kamfanin. Da sauri ta bi bayan shi tana jiran ƙarin bayani amma bai ce komai ba. Sai da su ka iso wajen motar sa ta ce “Sir fita za mu yi ne?”

“Shiga mota” abinda ya iya cewa kenan. Sai da ta zauna da kyau sannan ta kalleshi ta ce “Sir da ka gayamin fita za mu yi ai da na ɗan gyara fiskata ko. Yanzu ko ɗan hodan nan ban ƙara tisawa fiskata ba, fiskata ta yi wani bauu”

” Miss Salihu ina so ki sa a ran ki cewa wannan kamfani ba fashion industry ba ne inda ake gudanar da fashion shows. This is a constructions comp….”

“Daɗina da kai Sir Najeeb akwai wasge mutum. Kuma dan ina aiki a kamfani irin wannan sai ba zan yi ado ba. Yanzu idan a yamutse na ke fitowa kai kan ka ba za ka ji daɗin aiki da ni ba, balle ma su zuwa wajenka kullum”

“Miss Salihu…” ya faɗa da ɗan ƙarfi

“Sir Najeeb ina neman alfarma dan Allah”

Ɗan juyowa yai ya kalleta na ɗan daƙiƙai sannan ya maida hankalin sa ga tuƙin da ya ke yi.

“Sir dan Allah ka dena kirana da Miss Salihun nan. Shi fa Salihun nan yana chan kwance cikin kabari amma ka dinga kirana da sunan sa. Ga Aisha ga Farida duk bai maka ba, sai ka kirani da Salihu” ta ɗan yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce “Salihun ma fa a hoto kawai na ganshi ban ganshi a zahiri ba, amma abi a dameni da Miss Salihu Miss Salihu”

Wannan karan muryarsa a kausashe ya ce ” our relationship is strickly formal Miss Salihu. So ba abinda zai sa na kira ki da first name na ki”

“Abin ai son kai ne. Ita sister Munibat ai Miss Munibat ka ke kiranta ba Miss AbdulHamid ba. Ga wancan ƙatuwar nan Khalidah, itama sunan ta ka ke kira. Sai ni ne za a raina a dinga wani yaɓa mani Miss Salihu kamar wata marar suna. Gaskiya Sir ka dinga kirana da suna na nima”

“Or what?” Ya faɗi yana kallon ta

“Sir ni dai ka gyara dan Allah”

Bai sake cewa komai ba har sai da su ka iso inda za su je. Ya ce ta fito kuma ta kimtsa kan ta baya son yawan surutu. Wani ɗakin taro ya shiga ya barta a reception wai ta jira shi.

Kusan awa ɗaya yai a wajen sannan ya fito. Tunda su ka bar wajen su ke tafiya tun tana shiru-shiru har dai ta kasa jurewa ta ce “Sir Najeeb wai garin za mu bari ne kam?” Bai kulata ba sai ma ƙara volume ɗin kiɗan da ke tashi a motar da yai.
Haka ta haƙura ta yi shiru har su ka isa wajen. Tana fitowa a mota ta fara miƙa tana cewa ” kai! yau na zaunu gaskiya. Irin wannan nisan waje haka”

Wani site ne da kamfanin su ke ginawa ya zo dubawa. Bayan zaunuwa to Farida ta taku domin kaf wajen sai da su ka zaga duk girman shi. Su kan tsaya da wasu ma’akata yai mu su tambayoyi da ‘yan bayanai. Anan ta ke ɗan rubuta wa su abubuwa kamar yadda ya buƙata.

Ƙarfe uku sai ga kiran Anas ya shigo wayar sa. Lokacin su na hanyar dawowa. Yana ajiye wayar ya kalli Farida da ta yi lanƙwas a motar ya fara faɗa.

“Miss Salihu are you nuts?”
(Miss Salihu kin yi hauka ne?”

“Kin fixing meeting da Mr Abraham ƙarfe uku ba tareda kin gayamin ba a wani dalilin?”

“Sir, ba ka ce min za ka fita ba ai. Kuma mantawa na yi”

“To hell with mantuwar ki. Miss Salihu, akwai dubban mutane da su ke neman aikin nan, idan ba za ki yi aiki da kyau ba zan kore ki”

Shi kan sa sai abin ya zamo ma sa banbaraƙwai wai ‘zan kore ki’ ba ma ‘na kore ki ba’ kamar yadda ya saba faɗi.

“Sir Najeeb dan Allah ka dena ɗaga min hankali, dududu yaushe na dawo aiki bayan wannan iftila’in da ya sa me mu. Irin wannan rashin godiyar ne ya sa wallahi aikin nan ke fita min a ka. Ga shi mutum duk ya fiffige saboda aiki amma ba ka gani. Ni mutum ce kuma ba abun aibi ba ne ace na yi mantuwa tunda yana kan kowa”

Yana son maida ma ta martani amma ya rasa me zai ce. Yawan maganarta shi ne abu na farko da ya ja hankalinsa ranan da ya fara ganinta a restaurant, haka nan har yau bakin nan na nan. A kowani lokaci tana da abin faɗi choichoichoi. Tunowa da yai da kama su da aka yi da irin surutun da ya sha, ya sa ya san wannan Aisha Faridan a ko ina sai ta yi magana ba ta iya yin shiru……

……………………….

Tana zaune tana typing memo Anas ya shigo office ɗin ta.
Sir Najeeb ya jima da fita kuma a yadda ya ce ya tashi kenan saboda zai daɗe. So ta ke ta ƙarasa abinda ta ke yi ta tafi itama duk da kuwa ƙarfe biyu ne saura. Ciwon cikin period ke damunta tun safe shiyasa ta ke nan laƙwas ba kuzari sosai duk da kuwa ta sha magani ya lafa ma ta kaɗan.

” ‘yar uwa yau ba zoɓo ne? Kin san i’m addicted to your zoɓo”

” Ya Anas ban yi ba yau. Ni zoɓon ma zan dena gaba ɗaya tunda Sir Najeeb ya nuna indai na cigaba da sana’a a office to cikin albashina”

“Ya Najeeb zai ma na haka kuma?”

“Hmm kaman ba ka san shi ba, watan da ya wuce da ya zare 40% ai har yau shiru ka ke ji. Wai jiya Halima tana duba gwanjo anan da ya shigo ya gani haka ya dinga faɗa har da cewa wai ya ƙara ganin na buɗe hajata a office zai cire 10% a cikin albashina. Kuma fa ya Anas lokacin break ne ba wai a lokacin aiki ba”

Anas yai murmushi ya ce ” kin fara gajiya da shi ne Farida? Ko za ki bar aikin?”

“Yaya kenan. Ni fa idan ka ga na ajiye aikin nan to aure na yi, na gano take-takensa ai, dama so ya ke na yi wani abu ya koreni. Mutum sai shegen taurin rai”

“Well, ni na ga alamun tun fara aikin ki da shi ya chanja, he’s becoming more tolerant now. Allah! Farida da Najeeb ɗin da ne da tuni kin bar aiki a nan”

“Hmm shi ya sani, wai ace mutum yai ta haɗe rai shi kaɗe ya ƙi shiga jama’a. Ai jama’a Rahama ne”

“Kowa da irin rayuwarsa ‘yar uwa”

Har zai fita ya ce ” ki ji har na manta. Akwai baƙin da za su zo gobe wajen Najeeb, ki scheduling lokacin meeting da su sannan ki sanarwa Najeeb on time kar ayi irin ta ranan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button