SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

………………….

Ana zaune ana duba kayan da su Faridan su ka siyo Maijiddah ta shigo tsakar gidan da sallama, dawowarta kenan daga yiwa Hajiya Yelwa kitso. Kai tsaye ɗaki ta nufa bayan ta gaishe su.
“Ke Jiddah zo nan” Farida ta kirata.
Ba mu su ta dawo ta tsugunna gefen Faridan ta ce “gani Anty”

“Kina gani kowa yana duba kaya yana sa albarka ke za ki tsallake ki shige ciki”

“Lah Anty zan cire hijabi ne na wanke hannuna sai na fito”

Zainab ta ce ” ba wani, baƙin ciki ta ke ba nata kayan bane”

Farida ta wurga mata wani awarwaro wanda ya doki hancinta maimakon bakinta da Faridan ta yi niyya.

“Zan ci Ubanki agidan nan, sa’arki ce da zaki dinga yaɓa ma ta magana son ran ki. Na ce sa’arki ce!” Ta daka ma ta tsawa.

Anty Hanne wanda ita ce ta biyu a matan Baffa Musa kuma Umman Zainab ta ce ” Yo ba gaskiya ta faɗa ba. Anyi auren ƙannenta biyu yanzu za a sake wasu biyun. Ai abin kunya ne ace ko mashinshini ba ta da shi”

“Da kyau, dama Zainab ai daga nono ta sha. To barin gaya mu ku, tafi ƙarfin tayi baƙin ciki da bikin ƙannenta saboda duk cikin su ba wanda yake auren mijinta. Na ta mijin na nan zuwa, za ku ganshi handsome gentleman da shi”

Hajara ta ce ” waya ga handsome mijin shortie” gaba ɗaya sai aka sa dariya banda ‘yan ɗakin su Maijiddan wanda su ke tausayinta. Maijiddah ta fashe da kuka ta tashi za ta bar wajen Farida ta riƙe hannunta ta ce ” ba inda za ki je. Ki tsaya ki kalli kowacce ido cikin ido ki maida mata martani daidai da ita”

“Anty Farida gaskiya su ka faɗa, na yi kwantai”

“Ji mim shirme, inba dan ke da su ɗin duk ‘yan ƙauye bane dan kina 20yrs ba ki yi aure ba shine kin yi kwantai. Tukunnama ke za ki aurar da kan ki ne? Ko mijin ya zo kin ce bakya so”

Ta kalli Hajara da ke dariya ta ce ” ke kuma fantsararriya, za ai aurenki at 16yrs ba abinda ki ke hangowa sai kwanciyar aure saboda abinda ki ka sani kenan. Gaya min me ki ka iya? Wacce sana’ar ki ka iya? Jakar banza kawai, yanzu haka wankar tsarki mai kyau ba ki iyaba, tun tasowar ki ke daƙiƙiya ce, shiyasa ko jarrabawar WAEC ma ki ka ce ba za ki rubuta ba. Har mijin da za ki aura abin alfahari ne, ina shi ma wani tunkuzan ne kamar ki, ba ilimin Arabi bare boko”

“A hakan dai auren za ta yi, ta fi wasu da maneman ma ba ta da su” Anty Hanne ta faɗi tana hararan Farida

“Wallahi Jiddah ta fi ƙarfin ta auri miji kaman Haladu, mi za tai da irin su Haladu ai shi kam sai jaka irin Hajara. Mijin Jiddah ɗan gayu kuma mai ilimi ne Insha Allah”

Tuni wajen ya kaure da hayaniya, Baaba Sabuwa dama tuni ta shige ɗaki saboda takaici, ita ɗin kanta ba daɗin ganin Maijiddah ta ke agidan ba. Anyi auren ƙanwarta Murja duk da kuwa tsakaninta da Murjan shekara ɗaya ne to yanzu ga Salima ma za ayi na ta amma ita shiru. Tana jin hayaniyar su amma ko leƙowa ba ta yi ba.
Farida kam duk ta inda aka ɓullo kare Maijiddah ta ke ta hanata tafiya kuma ta hanata kuka. Ƙarshe dai sai gajiya su ka yi su ka barta dan indai wajen ɗasa magana ne to Farida ta kere su…

Da dare da za su kwanta Farida ta sa Maijiddah a gaba da masifa.

“Ke sai ana magana ki fara kuka, ba dole su raina ki ba. Ai su na magana ki na magana, wanda ya gaji ya bari. Tukunna ma ke idan za ki fita sai ki dinga saka dogin hijabai kamar matan Malam, a haka kam ai ko mutum zai tsaida ke a hanya ma zai ɗauka ke matar aure ce ya fasa”

” Lah na saba ne ai”

“A wannan zafin, to kul, kisa ɗan dai-dai amma banda dogin nan, idan ba haka ba zan sa almakashi na rage mi ki tsayin su”

“Kai Anty”

“I’m serious”
Maijiddah ta sa dariya…

Washe gari da sassafe Farida ta shirya za ta bi Yakubu wajen aiki saboda interview da ya ce za a ma ta yau. Sai da za ta fito daga ɗaki taga Maijiddah na shiryawa itama da alama fitan za tai,

” ‘Yan mata ina zuwa da sassafe haka”

” Hajiya Yelwa ce ta kirani wai dan Allah na zo na yiwa jikokinta kitso yau za su tafi”

“Ba za dai ki gyara ba ko”

“Mi na yi Anty?”

“Jiya mi na gaya mi ki?”

“Kayya Anty”

Farida ta je ta binciko ma ta wani hijabi cikin kayanta wanda bai da tsayi ta miƙa ma ta. “Sa ka wannan”

“Anty da kin barshi, skirt ɗin da na sa fa ya ɗan kama ni”

“Saka!”

Ba mu su ta amsa hijabin ta saka, da ke ita ɗin guntuwa ce ya kusa kai ma ta gwiwa.

Haka su ka jero su ka fito, ɗakin Baaba Sabuwa kawai su ka shiga su ka gaisheta sannan su ka fita…

…………………………

A office ɗin su Yakubu ta zauna wanda shi da colleage ɗin sa Engr Mathew su ke sharing. Tun a office ɗin ta dinga sa Mathew dariya da surutunta. Ƙarfe tara da rabi Yakubu ya dawo office ɗin ya ce Farida ta biyoshi. Kai tsaye office ɗin Anas su ka je. Da sallama su ka shiga office ɗin lokacin Anas na duba wasu takardu. Ɗagowar da zai yi ya ga yarinyar ranan, ta ke murmushi ya suɓuce ma sa cikin ransa yana ayyana abubuwa dayawa.

“Bismillah zauna” ya faɗi yana nuna ma ta kujera.

Yakubu ya ce ” sir ni zan wuce office”

” Ok Yaks”
Sai da Yakubu ya fita sannan ya kalli Farida ya ce ” Aisha Farida Salihu right?”

“No” ta faɗi tana kallon cikin idon sa.

“No kuma, ba sunan ki kenan ba” ya faɗi da mamaki

“To yallaɓai ka ga takarduna ka ga sunan da ke jiki kuma sai ka sake tambaya”

“Hmmm. Well na ga takardun ki kuma ba laifi i’m impressed. Sai dai aikin da za ki yi babban aiki ne kuma aiki ne da sai kin yi haƙuri sosai”

“Rayuwar duniya kanta sai da hakuri, balle aiki a ƙarƙashin wani” ta amsa tana kallon laptop ɗin da ke gaban Anas

“Da alama dai Yaks bai yi ƙarya ba gameda yarinyar nan, tabbas za a sha kallo tsakaninta da Najeeb” abinda Anas ya faɗi a zuciyarsa kenan. A fili kuma ya ce

“Malama Aisha, kasancewa muna buƙatan Secretary da sauri so gobe za ki fara aiki. Kafin nan zamuje ki ga office ɗin ki sannan zan nuna mi ki yadda za ki dinga gudanar da ayyukan ki”

“Abin da sauri-sauri haka?” Ta tambaya

“Ko ba za ki iya ba ne?”

“Kana ganin Ogan ka zai iya korana ne? Dan ance mini abu ƙiris mutum zai yi ya koreshi”

” I see, ashe kinada labarin wanda za ki yi aiki a ƙarƙashinsa. Kin san ba ya ɗaukan raini, Malama Aisha”

Farida ta ɗan yi murmushi ta ce “ni kuma banda mutunci ba, ga rashin haƙuri kamar zawo”

Anas yai murmushi sannan ya miƙe ya ce ” welcome to Najeeb constructions miss Aisha Farida”

“Thank you” ta faɗi tareda miƙewa itama…

Ta yi mamakin ganin girman wajen da aka nuna ma ta a matsayin office ɗinta, cikin ranta tana ayyana irin shagalin da za ta yi a wannan waje, ga ƙaramar fridge ga AC, kai aiki cikin jin daɗi haka.

“Ehmm, Ogan ki bai ƙaraso ba tukunna so zuwa gobe idan kin fito za ki ganshi. Ba sai an nuna mi ki shi ba kina ganin sa za ki ganeshi” maganar Anas ya dawo da ita daga tunanin da takeyi.

“Ba matsala Sir Anas”

Anas ya ce ” Kira ni da Anas ɗin kawai ai ke ƙanwar mu ce”

“Rufa min asiri, rashin kunyata ba ta kai nan ba. Kai fa sa’an Yaya Faruƙ ɗin mu ne”

“To kirani da Yaya kawai kinga dama ba ni da ƙanwa mace”

“Na gode Ya Anas”…

Ba su shiga office ɗin Najeeb ba haka su ka fito. Ya ƙara ma ta wasu bayanai gameda aikin, sannan ya ba ta takardar shaidar ɗaukanta aiki. Sai da ta biya office ɗin Yakubu sannan ta wuce gida.

Anas kuwa Farida na fita daga office ɗin sa ya ɗau waya ya kira Najeeb. A take ya sanar ma sa an samu sakatariya kuma gobe za ta fara aiki.

“she better be good” abinda Najeeb ya faɗa kenan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button