SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Bayan an fita da shi Farida ta sake tambayar su ko da mai ja, wannan karan ba wanda yai ƙwaƙwƙwaran motsi balle magana.

“Good, now what’s next?”

Anas yai gyaran murya ya gabatar da matsalar da ke gaban su a yanzu. Maganan French investors ɗin su da ke son siyan kaso arba’in na kamfanin yai tareda neman minene mafita.

Farida ta bada dama a kawo shawara. A wajen kashi saba’in sun ba da shawaran a sayar da 40% ɗin sauran kashi talatin ɗin kuma su ka bada shawaran a kan kada a siyar a bari su janye 11% ɗin su. Duk da kuwa kamfanin za ta shiga wani yanayi amma idan aka jure aka kuma bi matakai masu tsauri za a farfaɗo daga faɗuwan da kamfani za ta yi. Cikin wanda su ka ba da shawaran a bari su cire hannun jari har da Anas. Bayan Mrs Najeeb Jibo ta gama sauraron su sannan ta ce
“11+40?”
Kallon kallon aka farayi dan ba a gane me ta ke nufi ba. Ganin ba ta kuma cewa komai ba ya sa wani ya ce “its 51”

“Exactly 51” ta faɗa tana buga table.

“Taya 51% zai kasance shares ɗin wassu turawa, mun amince mu sallama mu su kamfani kenan?. Ta ya za mu bar wa wassu turawa kaso mafi tsoka cikin wannan kamfani, bayan shekaru bakwai kenan ku na yiwa wannan kamfani hidima ace kun kasa riƙeta har sai wassu baƙin haure sun zo sun mu ku jagoranci. Miji na baya nan hakan bai sa komai zai tsaya ba, dukkan mu mu na da hakki akan wannan kamfani. Maganar ma a saida mu su shares ba ta taso ba. We will fight, we will fight with everything we’ve got. Tsoro ba na mu ba ne, the moment mu ka sa tsoro to mun faɗi, we will all fight this together”

Gaba ɗaya wajen aka sa tafi.

Anas yai murmushi tareda ma ta thumbs up…

A hankali ta buɗe ƙofar office ɗin, office ɗin na nan yadda ta san shi. Ba wani chanji illa kawai mai office ɗin da baya nan. Ta ƙurawa kujeran sa ido tana ganin kaman Najeeb na zaune a wajen sai dai wannan karan maimakon yadda fiskan sa ke tsume koyaushe to yanzu murmushi ya ke ma ta.

“Sir Najeeb” ta faɗa a hankali.

“Aysherh” ta ga ya faɗa ma ta yana ma ta thumbs up.

“Farida” muryan Anas ya dawo da ita daga tunanin da ta ke.

Ta juyo tana kallon sa.
“Gaskiya kin yi ƙoƙari, sai dai da sauran aiki saboda jibi za su zo kuma ba mu shirya komai a kai ba”

“Ya Anas su zo ma na, su ɗin mala’ikun mutuwa ne da za mu ji tsoronsu?”

Anas ya girgiza kai.

“Wancan Mr Ogonnan ka sa a rubuta ma sa suspension na sati biyu. Ba ma son ɓata gari irin sa”

“Amma Farida ba kya ganin this is extreme”.

Farida ta zauna akan kujera tana mai faɗin Bismillah a zuciyar ta.

“Lokacin da na ce ba zan karɓi aikin nan ba mi ka ce min?”

Anas yai ajiyar zuciya sannan ya ce “Shikenan Farida, zan yi yadda ki ka ce”

” na gode Yaya na” fita yai daga office ɗin yana mai fatan zuwan Farida zai yi gyara ne ba lalata lamura ba.

Ta san dole za a samu matsala dama, shi ya sa tun farko ta ce ma sa ba za ta yi ba, saboda za su samu matsala da shi. Za ta iya bada umurnin da bai ma sa ba yai magana. A lokacin ya ma ta alkawarin duk abinda ta ce zai bi matuƙar bawai a harkan zane-zane ba ne tunda ba ta da masaniya a kan wannan harka.

Tana juyi a kan kujeran tana tuna hiran su da Daddy shekaranjiya.

” ‘ya ta, Anas ya faɗa min ba za ki kula da kamfanin Najeeb ba, mi ya sa?”

Ta sunkunyar da kai ta ce “Daddy, aikin ya min girma kuma ban da ilimi a wannan harka”

Murmushi yai ya ce ” Kamar ba Aisha Mai Gwanjo ba”

Farida ta yi saurin ɗago ido ta kalle shi cike da mamaki

Ya cigaba “Aisha mai turare, Aisha mai takalma, Aisha mai jakukkuna, Aisha mai zoɓo roto one in town…. and the list goes on. Aisha Baffan ki ya gaya min yadda tun ki na yarinya ki ka fara siye da sayarwa. Ko ba ke ba ce kina shekara tara ki ka saro goruba da taura ki ka zo da shi hutu kano, Baffan ki ya hanaki sayar wa ki ka ce ai ba za ki yi asara ba sai dai ya siye ya biya ki kuɗin hajar ki”

Farida ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin rufe fiskar ta da gyale saboda kunya.

“Lokacin da Najdah ke shekara tara ba abinda ta sani sai sakalci. “Lets go for ice cream Dad” ko “are we going to Disney this summer?” ” Dad i want a pink teddy not brown” yai murmushin yaƙe sannan ya cigaba.
“Allah ya ba ki baiwa Aisha ki gode ma sa bisa wannan ni’ima. Ba zan takura mi ki ba amma ni akaran kai na ina so ki jagoranci kamfanin Najeeb, Allah kuma zai taimake ki a kan hakan”…

“Allah ka taimake ni bisa wannan jagoranci, ka bani ikon sauke nauyin da ya rataya a kai na, ka ba ni ikon yin gaskiya da adalci, Amin” abinda ta faɗa kenan kafin ta fara buɗe tarin files da ke gabanta.

………………………..

Ƙarfe biyar da rabi ta isa asibitin, bayan an tashi sai da ta tsaya su ka tattauna da Anas kafin ta taho.
Tana shigowa ta samu Najma da Najdah a ɗakin.

“Sannun Anty, barka da yammaci” ta faɗa tana ajiye jakarta a kan ƙaramin fridge da ke ɗakin.

” an samu abinda ake so ko? Shi ne yanzu ba za a iya zama da shi ba” Najma ta faɗa tana mata wani kallo.

“Big sis ai dama kukan munafurci ne, neman attention ta ke yi kuma ta samu shine ta guje shi. I cant believe wai Daddy ne ya ce ta zama CEO ko mi ta sani oho”
Ta rasa cikin yayar Najeeb da ƙanwar sa wanne cikin su ta fi tsanarta. Mom da Daddy du ka sun karɓeta hannu bibbiyu kuma ba su da girman kai amma Najma da Najdah kam sai a hankali, ƙiri-ƙiri su ka nuna ma ta ba sa yinta, ba kamar Najdan ma.

Farida ba ta ce ƙala ba, ta ƙarasa bakin gadon da Najeeb ya ke kwance kamar mai bacci. Ta manna ma sa kiss a goshin sa ta ce ” My Champ, ka ga na jima ko? Aiki ne ya min yawa. Ka san sai yanzu na gane ba ƙaramin wahala ka ke sha ba a office ɗin nan. Da ni kullum gani na ke kana zaune kan kujera mai laushi ga AC ba ka da wata matsala, ashe abin ba sauƙi. Yau har irin zamanka na yi dan kawai na ba su tsoro, na nuna mu su cewa kana tareda ni. Kuma Wallahi sun tsorata. Ka san yanzu kai ni ne, ni ma kuma kai ne”

Najdah ta ja doguwar tsaki Najma kam ido da baki ta sake tana kallon ta. Ba su sha mamaki ba ma sai da ta ce “dan Allah tunda kun riga kun gaisa da shi ku bamu ware, miji da mata su na son keɓewa da junan su”

“Heeeee wonders shall never end, shegiya ke a suwa ki koremu a wajen ɗan uwan mu”

“Ni ɗin ce dai matar Najeeb”

Najdah ta kalli Najma ta ce ” Big sis ki ji abinda ta ke faɗa fa, wai mu fita a ɗakin Big B”

Najma ta tashi ta ɗau jakar ta ta ce ” ba laifin ta ba ne Najdah. Laifin Daddy ne da ya je ya kakaɓo wata ‘yar ƙauye ya haɗata da Najeeb, har ta ke ganin matsayin ta yana dai-dai da namu”

Har su ka fita ko kallon su ba ta yi ba. Ba ta da lokacin su, idan fitina su ke nema su jira Najeeb ya warke su ga ikon Allah.
Ta zauna ta sa kanta a gefen sa ta na shafa hannun sa. Bai jima ba bacci ya ɗauketa a haka…

Da dare su Daddy su ka zo anan Mom ke ma ta sallama akan jibi za ta wuce za ta je Umurah ta yi wa Najeeb addu’a. Farida ta yi farin ciki da hakan tareda addu’an Allah ya kai ta lafiya ya dawo da ita lafiya.
Fitan su ke da wuya tana zaune ta zubawa Najeeb ido, ta kai hannu za ta kama hannun sa sai ta ga ya motsa yatsun sa biyu. Wani ihu ta ƙwalla tana kiran sunan Daddy.

“My champ da gaske kai ka motsa yatsun ka? Da gaske yatsun ka ne su ka motsa?”

Ganin ba wani reaction da ya sake yi ya sa ta fita da gudu tana kiran su Daddy.

Sun yi nisa da ɗakin dan sun kusa fita a asibitin kafin ta taro su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button