SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Na ji mi ta ce fa, cewa ta yi mu je mu biyu”

“Ni ba inda zan je. A gaida marar lafiya daga nan a kai goro”

Sai da yai dariya mai isar sa kafin ya kai bakin sa zai kissing ɗin ta ta juyar da kai. Ɗan cizon kunnen ta yai ya ce “wannan kishin haka, kin san ke kaɗaice sakatariyar zuciya ta”

Ta ɗau hannu za ta kai ma sa duka ya riƙe hannun ya jawota jikin sa yana dariya…

Karfe biyar saura na yamma su ka isa asibitin. Lokacin Sabreen ta farfaɗo amma ba ta magana ko na ce ta ƙi magana da kowa. Jininta ne ya hau kuma likita ya ce idan ta cigaba da sa damuwa a ranta za ta iya samun heart attack. Magana ma ƙarin damuwa ne a gareta shiyasa ta ƙi magana. Noory kawai ta ke son gani.

Za su ɗakin da aka kwantar da Sabreen su ka haɗu da Dr Lukman. Najeeb yanata wani shan ƙanshi lokacin da Lukman ya miƙa ma sa hannu. Hannun sa sarƙe cikin na Farida ya ciro hannun sa da ƙyar ya miƙa ma sa su ka gaisa…
Farida ne ta iya ce ma sa sun zo duba mara lafiya ne. Amma Najeeb bayan gaisawa bai iya furta komai ba…
Bin bayan su yai da kallo yana ganin yadda Farida ke tafiya ya ji wani abu ya ɗarsu a zuciyar sa…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣4️⃣8️⃣

Da sallama su ka shiga ɗakin. Sabreen na kwance an ɗaura ma ta ruwa. Mouna kawai su ka gani a ɗakin. Tunda ta ji sallamar su ta juyo ta kafawa Najeeb ido hawaye na bin fiskarta.

“Sabreen” ya faɗa yana kallon yadda kwana ɗaya ta lalace.

“Forgive me Noory, forgive ne please”

Hannunta ya riƙo yana faɗin “na jima da yafe mi ki Sabreen. After all ke ƙanwata ce”

“Really?”
Najeeb ya ɗaga ma ta kai.

Farida na gefe ta cika ta yi fam. A wani dalilin zai riƙe ma ta hannu abin da zuciyarta ke raya ma ta kenan.

Ko me Najeeb ya faɗa ma ta oho ta dai ga maimakon hawaye da ta ke da sai ma bugewa ta yi da dariya, Najeeb ya sa hannu yana goge ma ta hawaye. Farida ta zaro ido waje. Ganin hirar ta su ta ƙi ƙarewa ya sa ra fara gyaran murya kaman wata mai mura.

Sai da ya ga ta sake ranta kafin ya ma ta sallama akan zai tafi gobe zai zo ya dubata. Juyawar da zai yi sai ya ga babu Farida a ɗakin. Mouna ta ce ai ta fita tuntuni.

Ya fito daga ɗakin yana mai kiran numbar Farida amma ba ta ɗauka ba. Yana ta dube-dube ko zai gan ta amma shiru. Kusan sau biyar ya kira amma ba’a ɗauka ƙarshe kuma idan ya kira sai ayi rejecting. Tsaki yai sannan ya kira numbar Abdullahi ya tambayeshi ko Farida tana mota Abdullahi ya ce ma sa e.

Cikin sauri ya fita daga asibitin dan ya san Farida fushi ta yi…

Yana shiga motar ya gan ta zaune fiskar nan a kumbure tamau.

“My Queen shi ne za ki tafi ki bar ni ni ɗaya”

Farida ta juyar da kai gefe ba ta ce komai ba.

Ya kamo hannunta ya riƙe. Ta fara kici-kici ɗin ƙwacewa tana faɗin
“Ni ka sake ni, kar ka taɓani da hannun da ka taɓa wata ƙatuwa har ka ke goge ma ta hawaye da shi”

“My love Sabreen Is sick and…”

“She’s sick ai, shine aka buge da taɗin soyayya, dan munafurci ma maimakon ayi da turanci yadda kowa zai ji sai aka fara larabci ana wani bubbuɗa hanci irin tsohuwar zuma ba lafiya ɗin nan. Mu je kawai ka biya sadaki sai…”

Tunda ta fara magana ya ke kallon ta, irin kishi haka tun ba’aje ko’ina ba. Lallai Aysherh. Ganin maganar na ta ba ƙarewa zai yi ba ya sa ya jawota ya haɗe bakin su. Ƙoƙarin ƙwacewa ta ke yi tana buga kafaɗun sa da duka hannun ta biyu amma bai ba ta dama ba. A hankali kiss ɗin ya fara shigarta, maimakon dukan kafaɗunsa da ta ke sai ya zama ta ƙara jawoshi jikinta sosai tana shafa wuyan sa zuwa gashin kan sa.

Sun jima a haka kafin su ka rabu kowa na maida numfashi saboda daɗewa da su ka yi su na kiss ɗin har numfashin su ya sarƙe ya gauraye ya zama ɗaya.

Farida ta kwantar da kan ta kan kafaɗar sa ya fara shafa bayanta yana jin mugun sha’awarta na taso ma sa. Farida ma dai jikinta ne yai sanyi shiyasa ta kwanta laƙwas a jikin sa. duk da ta tsinci kan ta a wani hali hakan bai sa ta manta ɗankaren wahalan da ta ɗanɗana jiya ba.

Abdullahi dai dariyan masoyan ya ke yana fata inama ta shi matar tana son kiss kaman Farida, amma ita ba ta so sai ta ce abin na sa ta jin amai. Wani lokaci auren wayayyiya da daɗi. Loddo kam banda ya taho da ita birni ba ta taɓa fita daga ƙauyen su ba. Shekara huɗu da su ka yi tare ma duk wassu abubuwan shi ya koya ma ta. Wassu ta ɗauka wassu kuma har yanzu fama ya ke da ita…
Gidan su Daddy su ka wuce su ka yiwa su Daddy da Mom ban gajiyan biki da kuma ya mai jiki. Farida ta shiga ɗakin su ta ɗau wassu daga cikin kayanta su ka fito. Da za su tafi Mom ke cewa daga gobe Tasallah za ta koma yi ma ta aiki. Farida ta ma ta godiya…

Daren ranan dai Farida ta yi ta yiwa Najeeb tsiya akan Sabreen. Da taga yana ƙoƙarin yin abubuwa sai ta sa ma sa kuka. Shima yai hakan ne dan yai maganin bakin ta, amma yana so ya barta ta warke na kwana biyu tukunna a cigaba da abubuwa. Tana kwance jikinsa tana kukan sakalci har bacci ya tafi da ita. Ganin ta yi shiru ya leƙa fiskar ya ga bacci ta ke, cikin zuciyar sa ya ce “my crazy Aysherh kenan”

…………………………..

Washe gari ma sun je sun duba Sabreen kuma Alhamdulillah ta fara jin sauƙi. Wannan karan Najeeb bai yi gigin taɓa Sabreen ba dan sai da ya sha warning daga wajen Madam ɗin sa kafin su ka fito.

A asibitin ne ma Mouna ke nuna mu su videon Sabreen da aka yaɗa. Najeeb ya san za’a jima ana yawo da wannan video kuma hakan na nufin career ɗin Sabreen zai samu tangarɗa.

“I’m sorry Sabreen” ga faɗa lokacin da ya gama kallon Videon.
Sabreen da ke zaune a kan gado ta yi murmushi ta ce “i want to start a new life Noory, offscript”

Farida da ke gefe ta ce “daya fi miki kam”
Sabreen ta ɗago ido ta kalli Farida tana haɗiye duk wani kishinta da ke cin ta.

“Please take care of him Ayshah”…

Da su ka dawo gida wannan dare kam Najeeb bai iya haƙuri ba sai da su ka yi abubuwa. Wannan karan ma ta yi kuka sai dai ba kaman na ranan ba…

Satin su ɗaya suna cin amarcin su, ba su zuwa ko’ina suna manne da juna.

Ranan Monday Sabreen ta wuce London dan ta duba jikin mahaifinta. Ba wai ta gama warkewa ba ne ita ne dai ta nemi a sallameta…

………………………..

Tana zaune a gaban mirror Najeeb na tsaye yana riƙe da hand dryer yana busar wa Farida gashin ta. Yanzu su ka gama wanka saboda abubuwa da su ka yi.

“My Champ yaushe za mu koma office, an koma aiki tun Monday fah. Ga Ya Anas ma ya fara fita”

“Who owns the Company?”

Ta marairaice murya ta ce “idan ba mu fita aiki zai wa ya Anas yawa”

“Sai mun dawo daga tafiya tukunna”

“Ina za mu je?”

“Surprise, ki dai shirya kaya dan tafiyar jibi ne”

Mintsinin sa ta yi a ciki wanda ke buɗe saboda towel kaɗai ne ɗaure a jikin sa.

“Shi ne ba za ka gayamin da wuri ba na yi sallama da jama’a na”

“Then it wont be surprise ai”

“Nikam nikam nikam” ta faɗa cikin sakalci. Ta manta hannun ta na jan towel ɗin sa. Sai ga towel ɗin ya faɗo ƙasa.

Kashe hand dryer ɗin yai ya ce ” da alama kina son sabon wanka”

“Ah Ah Ahhhh….”

……………………….

Da ke tafiyar su ta zo ma ta ba zata shiyasa a rana ɗaya ta shirya zuwa sallama gidan su tareda gidan su Najeeb. Gidan su Najeeb su ka fara zuwa da safe kafin ta wuce gidan su.

Ta kwana biyu ba ta je ba, ta ga gidan ya wani chanja ma ta. Sai a lokacin Baaba Sabuwa ke ce ma ta Anty Hanne ba ta gidan, Baffa Musa ya saketa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button