SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Alhaji yai waya ya ce maza Nazir ya maida yaran Lagos. Kasancewa Aneesa ta fita wajen aiki sannan Mama ma ta fita ya sa ya ɗau yaran ba tareda wanni cikin su ya hanashi ba. Ya na samun tiketin jirgi sai Lagos. Baby da Alizah sai murna dan dama sun ƙagu su koma school sannan su ka Dad ɗin su.

……………….

Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro, duk da dai abubuwan sun zo a tsukekken lokaci amma hakan bai hana Baffa ko Baaba Sabuwa yin ƙoƙari wajen yiwa ‘yar su gata ba. Da ke AbdulWahab na da gida a Kano anan za a ma ta jeren kayan ta.
Farida kam abun ya haɗu ya ma ta yawa kwana biyu su na aiki sosai a kamfani da ke akwai wani sabon contract da Kamfanin ya samu ga kuma shirye-shiryen biki. Har ɗan rama ta yi saboda zirga-zirga. A cewarta Maijiddah tana da gidadanci ba kaman ƙannen ta da idon su ya buɗe ba, dan haka ta ke sa’ido akan komai saboda ayi komai na zamani…

Gulma kam a Najeeb constructions sai ma abinda ya ƙaru musamman da aka kori Halima sannan aka ba wa Khalidah suspensio. Dayawa su na tafiya da cewa Najeeb da Farida su na soyayya ne musamman kasancewa har yanzu bai koreta ba duk da kuwa irin karya dokoki da ta ke. Sai dai duk gulman a bayan fage a keyi dan ba mai iya tunkaran Najeeb ko Farida. Irin dukan da Faridan ta yiwa Halima ma ya sa su ke tunanin ƙila Farida na da taɓin hankali…

Ɗan baccin da ba ta samu sosai cikin kwanakin nan saboda matsowar bikin Maijiddah shi ta ke yanzu a office. Sallaya ta shimfiɗa a ƙasa ta kwanta tana narkan bacci hankali kwance.

Ya kira telephone ba a ɗaga ba, ya kira wayarta still ba a ɗauka ba. Computer ɗin sa ya jawo ya duba ko ta fita ne sai ya hangota chan ƙasa tana bacci. Ya jima yana kallonta kafin ya tashi ya ɗau key da wayarsa ya fita.

“Miss Salihu” ya faɗa da ɗan karfi lokacin ya tsugunna kusa da ita. Sai da ya kirata a na uku sannan ta tashi a firgice. Ganin shi tsugunne ya zuba ma ta ido ya sa ta ɗan goge fiskarta ta ce ” sannu Sir Najeeb”

“Bacci a bakin aiki Miss Salihu”

“Yanzu sai ka ce acikin albashina. To ka yi haƙuri gajiya na yi”

Yadda ta yi maganar ya bashi dariya sai dai haɗa rai yai ya miƙe ya ce ta tashi za su fita.

Bin sa ta yi zuwa office ya nuna ma ta takardun da za ta ɗauka. Bacci bai gama saketa ba amma haka ta tattaro takardun ta biyoshi. Tsabar mugunta sai ya ƙi ya bi lifter ya bi stairs.
Suna saukowa ta fito da biro ta ɗan ƙara sauri ta caka ma sa biro a bayan wuyan sa. Hannu ya sa ya shafa wajen ba tareda ya juyo ba. Ƙaramar tsaki ta ja ta sake kai hannu za ta sake caka ma sa sai kuwa ƙiris ya juyo.
“Wayyo Allah na!….Wayyo!” Ta faɗi cikin ihu, ta zubar da files ɗin hannunta ta koma baya da gudu.

Irin yadda ya ga ta tsorata ta fita da gudu sai abin ya sa shi dariya. Sometimes ya kan yi tunanin yarinyar nan na da taɓin hankali…

Kai tsaye office ɗin Anas ta je. Tana magana tana haki ta ce ” Ya Anas…. ka taimakeni… yau na tsokano tsuliyar dodo”

“Mi ya faru? Mi ki ka yi?”

Ba ta bashi amsa ba sai ma ta cigaba ” wallahi ba zan sake ba. Ni ban ma san ya akayi na ma sa haka ba, dan Allah ka je ka bashi haƙuri”

“Me ki ka yiwa Najeeb”

Ta ɗan yi ajiyar zuciya ta ce “biro na chaka ma sa a wuyan sa”

“Biro” Anas ya maimaita sannan ya kwashe da dariya.

“Ya Anas ba dariya za ka yi ba fa, haƙuri za ka je ka bashi”

“Yanzu ke Farida a wanni dalilin za ki ma sa haka?”

“Kawai haushi na ji ya tashe ni a bacci kuma ya ce wai mu sauko ta stairs”

Cikin zuciyarsa ya ce “lallai Farida na jinjina mi ki”

A fili kuwa cewa yai ” yanzu dai kin amince kin yi laifi?”

“Na yi. Wallahi na yi”

“Shikenan, mu je na same shi”

“A’a kai ka fara zuwa tukunna, ni zan jira ka anan”

“Ki zo mu je ba abinda zai mi ki”

Jiki a sanyaye ta bi bayan Anas su ka wuce office ɗin Najeeb.

A zaune su ka sameshi yana waya. Daga bakin ƙofa Farida ta tsaya dan idan ma wani abin zai ma ta za ta samu ta gudu da wuri. Anas ya ƙarasa wajen sa ya zauna yana ɗan dariya ƙasa-ƙasa.
Yana ajiye wayan Anas ya ce “Yallaɓai mun zo biko, ƙanwar mu ta yi laifi kuma ta gane kuskurenta. Ayi haƙuri”

Shiru yai na ɗan daƙiƙai sannan ya ce ” ta gaya ma abinda ta yi?”

“Ta gaya min, kuma na ma ta faɗa sosai”

“Good, akwai psychiatrist da na kira yanzu, zai zo ya gwada min ita dan ban yarda da lafiyar ƙwaƙwalwar ta ba”

Daga inda ta ke tsaye ta ce ” haba Sir Najeeb, psychiatrist kuma. Sai kace mai taɓin hankali”

Kallon Anas yai ya ce ” idan aka tabbatar min da lafiyarta ƙalau, then she can work with me. Idan tanada matsala kuma sai ta je ayi treating ɗin ta, dan ba zan iya aiki da mahaukaciya ba”

“Sir ka rama abin da na ma ka idan haka ne” ta faɗi da ɗan ƙarfi

Shiru yai yana kallonta sai chan kuma ya ɗau biro ya miƙe tsaye. Tana ganin ya nufota da biro a hannu ta tsume, wai a dole ba ta damuba irin ta surrender ɗin nan. Sai dai saura taku kaɗan ya isota ta buɗe ƙofa ta fita da sauri.

Najeeb ya ce ” you see, she’s crazy”

Anas yana dariya ya ce ” she’s just funny. Dan Allah kar ka ma ta komai”…

Fitan Aisha Farida kam ai sai gida, dan ba ta yadda ta tsaya ba. Sai da ta je ta tuna ai ko wayarta ba ta tsaya ɗauka ba jakarta kawai ta ɗauka. Ta yi tsaki sannan ta yi amfani da wayar Jiddah ta kira Yakubu ta ce ya je ya ɗauko ma ta wayarta a office.

“Yanzu ke tafiya gida ki ka yi ba tareda an tashi ba, Sir Najeeb ya sani?”

“Ya sani mana, kai dai je ka ɗauko min wayata kawai”…

Najeeb ya fito daga office ɗin sa zai fita ya ji wayar Farida na ringing, ganin bai ga jakarta ba yai tunanin ta tafi ne. Zuwa yai ya ɗau wayar amma kafin ya ɗauka kiran ya yanke, take kuma aka sake kira sai ya ga sunan mai kiran an saving da My Ray. Tsaki ya ja sannan ya saka wayar a Aljihu ya fita.
Yakubu da ya zo bai ga waya ba ya kira Farida ya gaya ma ta. Ita kuwa ta rantse indai aka sace ma ta waya a Najeeb constructions to za ayi ƙaramin yaƙi dan kuwa ba za ta yadda ba sai an fito ma ta da waya…

………………

“Yanzu kinga wannan jakar, duk kayan ciki na ki ne. Na fi awa ɗaya ina zaƙulo waɗannan kayan a wajen ma su gwanjo. Wallahi ko manya-manyan boutique ki ka je ba za ki samu kaya ma su kyaun wannan ba, ai gwanjo rufin asiri ne. Sai ki samu kayan da har ki gama yayinsa ba za ki taɓa ganin irin sa ajikin wani ba”

Maijiddah ta buɗe jakar ta fara fiddo kayan da ke ciki. Duk wanda ta ɗaga sai ta yi saurin ajiyewa saboda yanayin kayan sun bata kunya.

“Jiddah ya na ga kina wani yanƙwane fiska kaman kin ga kashi?”

“Anty Farida wannan kayan ai….”

“Ai me? Na ce ai me?. Dan Uban ki ina siya mi ki mutunci kina cewa ke tsiya ki ke so. Wannan kayan da ki ke gani da su ake cin gari. Balle ke da ki ke da kishiya, kishiyar ma wayayyiya ‘yar boko”

“To Anty kuma sai insa wannan kayan in fito?”

Wani kallon banza Farida ta ma ta sannan ta ce ” idan kin ga dama ki sa, idan kin ga dama kuma ki ƙona su idan kin je chan. Ni dai na san watarana sai kin kirani kince Anty Farida zan iya samun irin kayan nan wallahi ko nawa zan biya ki nemo min su. Lokacin ni kuma sai na karɓi kuɗi mai tsoka a wajen ki kafin na nemo mi ki”

“Ki yi haƙuri Anty”

“Ba batun haƙuri ba ne Jiddah, so na ke ki waye ki shigo gari kema. Idan kin je kin mallake zuciyan maigidan gaba ɗaya. And Wallahi zan faɗa mi ki gaskiya ba da hijabi ko manyan kaya ake sace zuciyan miji ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button