SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Alhaji Matawalle zai biya kamfani taran miliyan ishirin ita kuma Khalidah za ta biya Farida miliyan biyu.

” ‘yar uwa mun yi kuɗi fa. Dan Allah ayi kason da mu”

Farida murmushi kawai ta yi dan ba wannan ba ne damuwar ta.

Ranan duk wani ɗokin dawowa Kano da ta yi ta ji Kanon ya fita ma ta a kai. Da yamma bayan ta dawo Baba Sabuwa ke kiran ta akan ‘yan uwan Najeeb sun kawo lefen ta yau da safe. Su kan su ba su san da zuwan ba ko karramawar kirki ba a mu su ba.
Farida kin ga kaya ki godewa Allah gaskiya domin an zuba dukiya a lefen ki. Yanzu ya za ayi? Za a kawo mi ki shi chan gidan kun ne ko ya?

“Baaba Sabuwa duk yadda ku ka yi” ta faɗi hakan ne saboda ko kaɗan maganar lefen bai sa ta ji raɗaɗin da ta ke ji ya ragu a zuciyar ta ba…

……………………

Yana shigowa Daddy ya kirashi tambayar sa yai ko ya je ya duba Mom ya ce bai je ba.

“Yanzu Najeeb ka kyautawa kan ka, da girman ka da ilimin ka amma ba za ka kyautatawa mahaifiyar ka ba. Duk abinda ta yi ma ka bai kai ace tana kwance a asibiti yau kwana uku ka kasa zuwa ka dubata ba. Najeeb tsinuwa ka ke nemawa kan ka?”

Maganganun Daddy su na shiga su na fita ta ɗaya kunnen ne, saboda ba jin su ya ke ba hankalin sa ya tafi wani wajen. Jini kawai ya ke gani malale a ƙasa ga kuma gawar Aisha…

Daddy ya gama ma sa wa’azi sai Najeeb ya tashi ya fita ba tareda ya ce komai ba…

Tuƙi ya ke amma zuciyar sa na tuno ma sa abun da ya faru shekaru da su ka wuce. Duk da yanzu ya girma kuma ya san ƙaddarar Aisha ne ta zo da haka amma wannan trauma ɗin da ya dasu a ransa tun yana yaro ya ƙi sake shi…


Cikin Aisha na wata takwas abin ya faru. Immediately Adam ya saki Nabilah ta tattare yaranta ta bar ma sa gida. Sai dai hakan bai sa Najeeb ya dena zuwa wajen Aisha ba. Idan ya taso daga makaranta chan zai wuce sai dare ya dawo. Mom ta ma sa faɗan amma baya ji.
Ana haka sai ɗaya daga cikin ma su kula da Aisha ta yi tafiya saboda Maman ta da ta mutu. Ganin haka ya sa Najeeb ya dawo wajen Aisha da zama duk da kuwa akwai Mrs Beverly tareda ita. A kwana na uku da ya koma wajen Aisha, Mom ta zo da ƙarfin tsiya ta tafi da shi gida ta hana shi zuwa wajen Aisha. Abu da renon turawa sai ya fara maida ma ta magana akan ba ta isa ta hana shi fita ba, Ya fita da gudu.
Mom ta nemi restraining order daga kotu akan ba ta yadda ɗan ta ya je gidan Aisha ba saboda tana tunanin Aisha za ta ma sa lahani. Da ke Najeeb under 18 ne sai ya zama dole yana ƙarƙashin kulawar iyayen shi. Ranan da letter ɗin ta fito haka Mom da jami’an kotu su ka je su ka ɗauko Najeeb tareda faɗawa security ɗin gidan ko da wasa kar ya bari Najeeb ya shiga gidan.

Daren ranan yai wani mummunan mafarki akan Aisha ta mutu hakan ya sa da safe ya kira Daddy da ke Belgium a kan ya sa baki yana son zuwa wajen Aisha.
Mom ta ce indai ya na America yara za su zo wajen sa amma Yaran ta ba za su je wajen Aisha ba. Da Najeeb ya fita school bai je ba sai da ya fara biyawa wajen Aisha ya ga tana lafiya kafin ya tafi.
Yammacin ranan da ya dawo ya samu Mom tana masifa akan Aisha ta dameta da kira. Najeeb bai kulata ba sai da Najma ta dawo ta ke ce ma sa yau ta ji tausayin Aisha domin ta kira kusan so biyar amma saboda ba ta magana ba ta iya ba da saƙon da ta ke son faɗa ba. Ƙila tana son ganin ka ne.

Hankalin Najeeb ya tashi, tunda su ka raba gida Aisha ba ta taɓa kira ba. Ta kira sau biyar kam yana nufin tana cikin matsala ne. Haka ya fita da gudu ya je ya ɗau keken sa ya tafi gidan Aisha duk da kuwa Mom tana ƙwala ma sa kira akan ya dawo.
Da ya je gidan tun daga falo ya fara kiran Aisha amma ba ta fito ba ya duba Mrs Beverly a kitchen ba ta nan sai ya haura sama da gudu. Kai tsaye ɗakin Aisha ya shiga. Amma mi sai ya ji kukan jinjira, yana duba gefen sa ya ga Aisha kwance ga jini duk ya ɓata wajen. Irin jinin da ya gani sai da wani jiri ya kusa kada shi ya dafe gini na wasu mintuna kafin ya ƙarasa wajen ta yana jijjigata amma ba ta tashi ba. Cikin kuka ya je ƙasa da gudu ya kira emergency line na police…

Yana tsaye aka zo aka ɗauke gawan Aisha, duk abinda idon sa ke sa ma sa shine Mom ce ta kashe Aisha. Ranan shima asibiti ya kwana dan yana tsaye a wajen bayan ansa gawar Aisha a mota ya faɗi ya suma…

Ko da bayan autopsy na Aisha ya fito kan ba kashe ta aka yi ba, haihuwa ta yi ita kaɗai jini ya tsinke ma ta kuma rashin Mutum a kusa da ita ya sa ba a kawota asibiti da wuri ba har ta mutu.
Najeeb bai daina ganin Mom a matsayin wanda ta kashe Aisha ba. He was very traumatized a lokacin da har ta kasance baya iya bacci sai da magani. Ya jima yana visiting therapist kafin daga baya aka ce ya dawo normal amma still a hakan bai koma dai-dai da Mom ba.
Rasuwan Aisha ya sa Mom ta saduda da rayuwa, ta nemi Adam ya maidata dan ta kula da Najdah…

“She wanted her dead all along, she’s evil” abin da ya faɗa kenan ya buga steering ɗin motar. Idon sa na buɗe amma duhu ya ke gani, yana ƙoƙarin saita motar ta shi wata babbar mota ta zo ta buge motar sa, motar Najeeb ta yi sama sannan ta dawo ta faɗi ƙasa…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣3️⃣2️⃣

wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900

wannan page ɗin na ki ne ke kaɗai Anty nah Surayyah. Wishing you health, wealth, peace, grace, mercy and joy amin. Allah ya ƙarawa rayuwarki ta Oga da ta yaran ki albarka amin. Happy birthday????????????

Tana zaune sai cika ta ke tana batsewa, abu ɗaya ta sani shi ne ta ajiye aiki da Najeeb sannan kuma dole ta rama abinda Sabreen ta ma ta. Ba za ta bar karuwan nan ta sha banza ba.
Tun tana duba agogo tana jiran Najeeb har bacci ya ɗauketa akan Sofa…

Daddy kam bayan fitan Najeeb kiran matar sa yai su ka yi hira, da ke jikin tan da sauƙi, dan likitan ya ce za’a iya sallamarta gobe.

Ƙarfe shaɗaya na dare wayar sa ta fara ringing, daga kan gado ya sa hannu ya lalubota ya ɗara a kunne dan ko gama gane numban da ya kira bai yi ba.
Abin da aka ce ma sa ne ya sa ya tashi zaune yana maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’oun jikin sa na ɓari.
Ɗaukan key yai ya fita daga ɗakin da sauri duk da kuwa pyjamas ne a jikin sa…

Tunda aka shigo da shi ake ƙoƙarin tsaida jini, yadda jini ke zuba a jikin sa da ma gefen kansa ka ce duka jikin sa zai tsiyaya zuwa ɗan ƙanƙanin lokaci.

Wani na ganin Najeeb Adam Jibo a jikin ID card ɗinsa ya gane ko ɗan waye, shi ya sa aka kira numban Daddy…

Yadda Daddy ke jinsa gani ya ke ba zai iya jira har Iliya ya taso daga BQ ya zo ya kai shi ba duk da an hana shi tuƙi da dare saboda idon sa.
Yana fitowa yana ƙwala sunan Malam Aminu maigadi akan ya buɗe gate, yadda ya ke kiran, shi kan sa Maigadi sai da ya tsorata… Ikon Allah ne kawai ya kai shi asibitin lafiya amma ƙila da shi ma hatsarin zai yi.

Yana zuwa aka ce har lokacin likitoci na kan sa. Jikin sa rawa ya ke bai iya zama ba yana safa da marwa zuciyar sa cike da addu’o’i. Tsabar rikicewa ko fitowa da wayar sa bai yi ba daga mota…

Anas ƙarfe huɗu da rabi na asuba aka kira shi, ya fito daga banɗaki kenan ya yi alwala ya ji kira kafin ya ɗauka ta katse. Ganin Daddy sai hankalin sa ya tashi, lokaci guda zuciyar sa ta raya ma sa ƙila Mom ce ta rasu. Duk da kuwa jiya da ya je dubata ya ga jikin ta da sauƙi sosai, to amma mutuwa ko da ciwo ko ba ciwo sai an tafi. Yana ƙoƙarin sake kiran Daddy kiranshi ya kuma shigowa ya ɗauka da sauri.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button