SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Wasa-wasa ranaku su ka dinga tafiya har ya saura kwana huɗu ayi aure. Gidan na su ya fara cika da mutane. Da ke Najeeb ya cewa Sabreen baya son hayaniya shiyasa ba ta nuna zaƙewa kan wassu lamuran ba. Dama itama ta ce tanason auren ne a sirrance dan kasancewarta celebrity idan maganar auren ya fito fili za ayita cecekuce, tafiso ko da za ayi gulma to ya zama bayan auren ne…

Ba wassu ‘yan uwa ba ne su ka zo daga ɓangaren Sabreen mahaifinta ma tun zuwan sa Walimar Najeeb da ya koma ciwon sa ya tashi, yana chan London ana kulawa da shi. Sabreen independent woman ne. Da ‘yan uwa, ba ‘yan uwa za ta yi aure ba abinda ya shafeta. Ƙanin Mahaifinta ne ya zo sai kuma yayan Mom da yayar Mahaifiyar Sabreen…

Daddy ya ce baya son hayaniya saboda albarkar aure ake so ba komai ba. Najdah ta so ayi dinner amma Daddy ya hana. Shi Daddy tun ciwon Najeeb yai wa kan sa karatun ta nitsu wajen almabazzaranci da kuɗi. Da da ne ba ƙaramin bidiri za ayi a bikin ba, dan ko lokacin auren Najma ansha shagali sosai…

Daddy bai san mi Najeeb ke shiryawa ba sai da ƙanin Baban Sabreen ya ma sa maganar sadakin Sabreen. Abun ya ɗaure ma sa kai, a take a wajen ya kira Najeeb.
Da Najeeb ya zo haƙuri ya bayar tareda nuna mu su cewa ya yi hakan ne saboda ya kowa wa Sabreen hankali.
Daddy ya rufe shi da faɗa yayinda Hajj Khalid Abu Nasir ya fahimci Najeeb ɗin. Tunda shi kan sa ya san lokacin da aka kashe maƙudan kuɗi wajen shirya bikin su amma Sabreen ta gudu ta bar su da abun kunya. Hakanan bai taɓa goyon bayan shiga film da Sabreen ta yi ba…

Ranan Jumu’ah bayan an yi sallar Jummu’a aka ɗaura auren Architect Anas Ali Almustafah da Najdah Adam Jibo biki ya samu halartar manya-manyan mutane…

Sabreen wani farin wedding dress ta saka wanda ta aje maƙudan kuɗi aka designing purposely saboda ita. Ta sha ado na dimond da gwalagwalai. Hakanan make-up artist da ta zo da ita Arfa ta rangwaɗa ma ta kwalliya, ba ƙarya ta yi kyau sosai.

Wanda su ka dawo daga wajen ɗaurin aure ne su ka fara labarin yadda taro yai taro. A wajen Mouna yayar mahaifiyar Sabreen ta ji aure ɗaya aka ɗaura, auren Najdah da Anas. Mamaki ya sa ta wuce ɗakin Sabreen wanda ke ta ɗaukan selfie cikin kayanta na aure kafin su zo su yi hoto da angonta…

Maganar da Mouna ta gaya ma ta ne ya sa jikinta ya fara rawa. Waya ta ɗauko da sauri ta kira uncle ɗin ta wanda ya ƙara jaddada ma ta auren Najdah kawai aka ɗaura ban da na ta. Wayar hannun ta ya suɓuce ta yi durƙushe a ƙasa kanta na ma ta wani nauyi, zuciyarta na cigaba da bugawa da ƙarfi-ƙarfi kaman wanda zai bulluƙo…

  • ku wanke idon ku da kyau gobe za’ayi abubuwa*

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣4️⃣5️⃣

Duk yadda ta daure ma zuciyarta ta ka sa saboda wani ƙunci da ya cika ma ta zuciyar.
“Ahhhhhhhh” ta fashe da kuka

“Noory dont do this, dont do this to me plz” sunbatun da ta farayi kenan tanayi tana kuka.

“Mahlan yaa Sabreen, Mahlan binti” Mouna ta faɗa tana ɗan bubbuga bayan ta.

Lokaci guda ta yi wuff ta miƙe tsaye tareda tattare rigarta da ya baza waje ta fita da gudu, su Mouna su ka bi bayan ta…

Ɗakin Mom ta shiga ba ta nan dan haka ta sauko ƙasa da gudu tana kiran Noory.

A falon ƙasa ta yi kiciɓus da Najma. Najma cikin rashin sanin miya faru ta fara tambayan lafiya, Noory kawai ta iya furtawa.
Najma ta ce bayanan. Sabreen ta fita da gudu tana kiran Noory…

Yana wajen reception Najma ta kira shi akan ga Sabreen tana ta kuka tana neman sa. Ya san za ayi haka, hankalin sa kwance ya ce a bashi 30mins yana zuwa. Shi yadda ya tsara ma baya so ta gano shi har sai dare idan ya zo da niyyar zai ɗauki amarya. A yadda ya sharara ma ta ƙarya cewa yai shi zai zo ya ɗauketa su je gidan sa inda anan za su ci amarcin su. Ai raka amarya ƙauyenci ne, ita kuma Sabreen ba ‘yar ƙauye ba ce…

Zuwa yanzu kusan kowa agidan ya san abinda ke faruwa. Sabreen tana zaune tana kuka, fiskar nan duk ya chaɓe, kwalliyar da aka wa idon duk ya zazzago sai idonta ya zama kaman wani horror.
Sai lallashinta ake, wanda ba su san mi Sabreen ta yiwa Najeeb ba su ka fara zagin Najeeb, wassu har cewa su ke ƙila ƙwaƙwalwarsa ce ta motsa tunda ance tun rashin lafiyan da yai ƙwaƙwalwarsa ba ta dawo dai-dai ba. Ka ji mutane fa…

Farida tun da sassafiya da su ka tashi ta fara wani tsumewa ita a dole yau za a mata kishiya. Da Najeeb ya ɗau wanka ya sha manyan kaya zai tafi ta ce ma sa “Allah ya taimaki angon Sabreen”
Yai dariya kawai ya fita. Kwanciyar ta ta yi, sai ƙarfe goma sha ɗaya ta tashi. Bayan ta yi wanka ta shirya sannan ta fito. Ƙasa ta sauka dan ta nemi abinci dan tsayawa sai Adama ko Tasallah sun kawo ma ta har ɗaki ba adalci ba ne dan ta san aiki ya sha mu su kai..
Bayan ta karya Mom ta kirata, da ta je kaya ne ta bata wanda za ta sa a yau ɗin, ta karɓa tana godiya…
Tana ɗaki ta idda sallar azahar kenan ta ji ihun Sabreen. Jin hayaniya ya fara yawa ya sa ta sauko dan kar ayi show ɗin ban da ita…

Ba ƙaramin cika aka yi a falon ba. Kowa da abinda ya ke cewa zuwa yanzu Sabreen ta dena ihun kuka. Hawaye ne kawai ke zuba a idon ta…

Har lokacin kayan da ya sa ya je ɗaurin auren ne a jikin sa amma babu malun-malun ɗin. Bai yi mamakin ganin yadda mutane su ka cika falon ba dan yasan mata da gulma. Najma da Mouna ne ke gefen Sabreen su na ƙara lallashinta.
“Ga Najeeb ɗin” Najma ta faɗa lokacin da ya shigo.
Zumɓur ta miƙe ta nufe shi.

“Noory why? Why?” Ta faɗa tana dafe ƙirjinta da ke ma ta zafi.

Ɗan murmushi yai sannan ya ce “Why? Sabreen ki na tambaya na Why?. The same why da ki ke tambaya shi na yi ta tambayan kai na 9yrs ago. We were inlove remember, we made so many promises. Sabreen why? Abinda na yi ta tambayar kai na kenan. It took years kafin na amince wa kai na cewa ni ko soyayyata ba komai ba ne a wajen ki. That being an actress ya fi ni muhimmanci a wajen ki. That having a role in a movie ya fi aure na a wajen ki, That the love we shared was fake, that everything about you is fake”

Sabreen ta tsugunna a ƙasa tana ƙara danne ƙirjinta saboda gani ta ke idan ta cire hannunta ƙirjin ne zai fito saboda yadda ya ke bugawa da ƙarfi.

“Kina ji kaman zuciyar ki za ta fashe ko? Thats exactly how i felt and even more, na tsani kowa na tsani komai, na zamo tamkar mahaukaci. Sai da na yi watanni bana cikin hayyacina Sabreen. Ba na iya bacci sai na sha magani ba na iya cin abincin kirki. Years went by and i couldnt love again, kyawawan mata, mata ma su matsayi da ƙasaita fiye da ke sun nemeni amma idona ya rufe, ba na kallon kowa sai ke. In those 8years da na yi ta yawo da dakon soyayyar ki not once ki ka waiwaiye ni, not even once Sabreen. You’re busy creating your fake life, kin manta da ni gaba ɗaya. In 8yrs kin je an mi ki butt enlargement, kin je an miki plastic surgery an gyara miki wide lips ɗin ki, in 8yrs kin dating manya-manyan mutane guda uku, in 8yrs kin zubar da ciki that almost killed you because you nearly bled to death. In 8yrs kin renouncing addinin ki saboda kina son auren wani ƙaton kafiri. In 8yrs…”

“Noory stop, plz stop” Sabreen ta faɗa tana kuka tana riƙe ƙafar sa.

“Sabreen ban miki haka dan na punishing ɗin ki ba sai dan na nuna mi ki cewa rayuwar ki tana tafiya ne base on movie scripts and you need to wake up. A year ago da ki ka dawo kin ce kin ajiye film saboda ni, kin ce kina so ki zauna kusa da ni ki samu soyayyata a karo na biyu, but few months bayan na shiga coma ki ka tattara kayan ki ki ka koma Hollywood saboda an baki role tareda Keanu Reeves”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button