SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

team Farida kun karɓi haƙurin Najeeb ko ya?

Skt 57

“Ka yi haƙuri amma ba zan koma yanzu ba” ta faɗa a hankali duk da kuwa maganganun sa sun karya ma ta zuciya.

Ya cize leɓen sa na ƙasa yana huci, bayan ‘yan daƙiƙai ya miƙe tsaye ya ce “tunda abinda ki ke so kenan zan jira ki”…

Ba ta iya ɗaga ido akan sa ba har ya fita daga ɗakin.
Anya ta ma sa adalci kuwa? Ta tambayi kan ta. Sai dai kuma ta rasa gane amsar da za ta bawa kan ta…

Yinin ranan sai sintiri ta ke tsakanin falo da ɗaki amma Najeeb bai dawo ba. Washe gari ma bai zo gidan ba…

Su uku ne a dining su na cin breakfast lokacin da Najeeb ya shigo. Kwana biyu kenan bai zo gidan ba.
Wajen Mom ya je ya gaisheta, ta shafa gashin sa tareda ma sa peck a goshi.

Ya duba Sabreen ya ce “amarya ya shirye-shirye”

Sabreen ta yi murmushi ta ce “shiri ai sai su Mom da Ayshah, su ke ta komai”

“Allah ya kaimu lokacin”

Mom ta amsa da amin yayinda Sabreen ta sunkuyar da kai tana murmushi.

“Zan wuce Abuja, i’ll be there for two days”

Mom da Sabreen su ka ma sa addu’ar Allah ya kiyaye.
Farida tunda ya zo ta ke binsa da ido amma bai ko kalli wajen da ta ke ba.

Ganin ya juya zai tafi ya sa ta yi saurin sake mug ɗin tea da ta riƙe, Mug ɗin ya faɗi kan tile ya ɗan fashe.

“Ouch…Ouch … Wayyo zafi…” Farida ta faɗa saboda tea ɗin ya ɗan fetsu ma ta.

“Sannu Ayshah, sannu, ba ki ji ciwo ba ko?” Mom ta faɗi tana ƙoƙarin riƙe hannun Farida.
Farida kam idon ta na kan Najeeb wanda ta ke tunanin zai zo da gudu ya dubata. Sai taga saɓanin haka tsayawa kawai yana kallon ta.

Ɗan gyaran murya yai ya ce ” na tafi”

Farida na jin haka ta fashe da kuka.
Sabreen mi za ta yi banda dariya. Mom ma dariyan ta ke son yi amma ta gimtse.

Har ya fita Farida bata dena kuka ba. Sabreen ta ce “someone is missing her husband”

Farida ta kalleta ta galla ma ta harara. Mom kam yi ta yi kaman ba ta san sunayi ba, Adama ma ta kira akan ta zo ta tattare wajen da Mug ɗin ya fashe…

Ƙarshe haushi ya sa Farida tashi daga wajen ba tareda ta gama cin abincin ba…

………………………

Tana jiran kiran sa ko text amma shiru. Baƙin ciki ya tokare ma ta maƙoshi, kowa ma haushin sa ta fara ji a gidan. Sabreen kuwa indai su ka haɗu sai ta tsokaneta akan Najeeb.

Ranan da zai dawo ta samu Mom a ɗakin ta da su ka gaisa ta ce “Mom zan je na ɗau wassu kaya a chan gida”

Mom ta yi murmushi dan ta gano Ayshah na son komawa gidan ta ne. Ta ce ” ‘yata ni inaga horon ya isa haka, Son zai cutu idan ki ka cigaba da zama a nan”

“Amma Mom…”

Mom ta katseta da cewa “ki yi haƙuri ki koma kin ji”

Farida ta yi ajiyar zuciya ta ce “shikenan zan koma saboda ke”

Mom ta ce na gode. Sai da Farida ta fita sannan Mom ta yi murmushin manya…

Farida ta kira Adama ta tayata haɗa kaya, da su ka gama ta kai ma ta su cikin mota. Da ta shirya ta je ta yiwa Mom sallama sannan ta shiga ɗakin Sabreen. Waya su ke da Lukman lokacin da ta shigo, tana kallon ta da jaka ta sa dariya har da hawaye.

“Ni ba na son gulma, Mom ce ta ce na koma” Farida ta faɗa tana haɗa rai.

Sabreen ta ce ” to Allah ya kiyaye hanya sai mun zo karɓan tsaraba”…

Saloon ta fara wucewa aka ma ta gyaran gashi da lalle sannan ta wuce gida. Ko’ina na nan tsaf-tsaf saboda Tasallah ba ta wasa da gyaran gidan.

Lokacin da ta shiga ɗaki wanka ta yi ta feshe jikin ta da turaruka.
Ƙarfe biyar na yamma Abdullahi ya faɗa ma ta zai je ya ɗauko Najeeb a airport yanzu kuma ƙarfe huɗu da kwata.
Gyara ɗakinta ta yi kafin ta wuce na shi ɗakin. Yana nan a gyare amma sai da ta cire zanin gado ta sake sa wani sannan ta shiga banɗaki dan ta wanke…

Tun ƙarfe biyar da kwata ta ke tsaye jikin balcony na falon sama tana jiran dawowarshi amma Abdullahi bai shigo gidan ba sai ƙarfe shida saura minti goma. Tana ganin ya fito daga motan ta yi saurin barin wajen. Ɗakin sa ta shiga ta fara gyara arrangement na turaruka da mayukan sa…

Ta ji shigowar sa amma ta dake ba ta kulashi ba ta cigaba da gyaran har da faɗin ” duk an bar ɗaki a hargitse. Komai gashi nan ba tsari kaman ba mutum ke kwana a ɗakin ba”

Yana tsaye yana kallon ta bai ce komai ba duk da farin cikin da ya mamaye zuciyar sa.

Ya ajiye jakar sa ya shige banɗaki ba tareda ya ce ƙala ba. Tana binsa da wutsiyar ido har ya shige banɗakin.

Ta ɗan yi ƙaramar tsaki ta ce ” koma ya nuna ya gannin nan”
Ta zauna bakin gado tana jiran sa. Ya jima a banɗakin kafin ya fito sanye da bathrobe fari.

“Ni fa kar mutum ya ga na zo ya nemi yi min walaƙanci Mom ce ta ce na zo.”

Shiru Najeeb bai ce komai ba. Ta ɗaga ido ta kalleshi yana tsaye gaban mirror yana shafa jikin sa da mai.

“Allah na gani sai na tafi tunda ba a son ganina, dama ba wai da son rai na na zo ba”

Najeeb ya ajiye man da ke hannun sa ya je ya buɗe ƙofar ɗakin ya ce ” a gaida Mom da su Sabreen. Allah ya kiyaye hanya”

“Kuturun Uban chan. Au’uzubillahi har ka sa ina zagi”
Ta tashi fuuuu ta ce ” zan tafi ɗin koma ba za ka sake ganina ba”

Sai da ta zo shigewa ta ƙofan ya riƙe hannun ta.

“Ni ka sake ni in tafi, ka sake ni na ce”

Ya jawota jikin sa yana kallon ƙwayar idon ta. Itama ɗin kallon sa ta ke ƙirjin ta na bugawa da sauri-sauri ba abinda jikinta ke muradi irin tajita kwance kan faffaɗan ƙirjin sa.

“My stubborn Mrs Jibo. Na san duk maganan nan cika baki ne kawai, you miss me, i see it in your eyes”

“Ba wani. Ni dama taimakon ka zan yi tunda Mom Allah Annabi ta roƙeni akan na dawo”

“Oh really?” Ya faɗa tareda sunkuyo da kan sa, ganin yana matso da bakin sa kusa da nata bakin ya sa ta lumshe ido tana jiran haɗuwar bakin su.

Maimakon kiss a baki sai ya kissing kumatun ta. Ta buɗe ido a hankali gaba ɗaya ta yi laushi saboda wani mugun sha’awar sa da ke taso ma ta.

Murmushi ya ma ta ya sake matsowa da bakin sa wannan karan kam tuni ta yi saurin matsawa da nata bakin, bakin su ya haɗe waje guda…
Sun jima suna aikawa junan su hot kiss kafin ya jawota zuwa kan gadon. . Wata ɗaya da ‘yan kwanaki rabonta da shi, ba ƙaramin missing ɗin sa ta yi ba. Yadda ya ke sarrafata haka itama ke mayar ma sa da martani, sun jima su na gogar junan su saboda an jima ba a gamu ba…

Bayan komai ya kankama da su ka yi wanka Najeeb ya ce ” ki shirya na maida ki wajen Mom na haƙura ki huta a chan”
Duka ta kai ma sa ya goce yana dariya…

……………………..

Rayuwan masoyan gwanin sha’awa, kullum su na manne da juna. Duk dare sai sun tashi sun gudanar da sallah sun roƙawa junan su addu’an samun zaman lafiya da kuma samun ‘ya’ya ma su albarka. Duk Jumu’ah Farida ba ta fasa yin sadaka ba…

Ranan Asabat aka ɗaura auren Sabreen da Lukman. Daddy ne ya zama alwalin Sabreen ‘yan uwanta sun zo ba laifi, wannan karan har mahaifiyarta sai da ta zo. Anyi walima kuma anyi family dinner a gida. Washe gari Sunday kuma aka wuce da Sabreen Abuja. Farida ta so zuwa amma Najeeb ya hana saboda yanzu ta yi nauyi.

Duk cikin ‘yan uwanta babu wanda ya nuna damuwar sa da asalin Lukman, su daɗin su ne ma Allah ya shirya mu su Sabreen har kuma ta yi aure hankali kwance…

…………………..

Wanda su ka kawo Sabreen mutum huɗu ne Mom ce da Najdah sai Aunt Mouna da wata cousin ɗin Sabreen ɗin Nihaya. Ba su fi awa biyu a gidan ba suka koma bayan sun yiwa Sabreen ‘yan nasihohi.

Ƙarfe biyar Lukman ya shigo gidan na su. Cike da farin ciki, finally shima ya zama ango…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button