SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

…….

Ya fito daga wanka kenan ya ji ana buga ma sa ƙofar ɗaki. Ya sani sarai ita ce amma ya share. Ganin ancigaba da bugun ba a daina ba ya sa ya je ya buɗe.
Tsaye ta ke ta sha light make up a fiskarta, jikinta na fidda wani ƙanshi mai jan hankali, tana sanye da doguwar night robe baƙa.

“Yes, what can i do for you?” Ya faɗa yana kallon ƙwayar idon ta.
Ba ta yi magana ba, ta sa hannu ta zarge igiyar robe ɗin da ta sa, a hankali robe ɗin ya sulluɓo ƙasa.

Idon sa ne ya fara tracing ɗin jikinta tun daga sama har ƙasa. Haɗiyar miyau kawai ya ke saboda yadda ran sa ke ayyana ma sa abubuwa dayawa. Wata arniyar lingerie ta saka, wato yadda ka san an sa igiya an matse ƙasan breast ɗin ta haka nonuwanta su ka ɗago sama su ka cika tam cikin raga-ragar rigan. Riga ce da ta bayyana ko’ina a jikinta.

Da wata mitsitaiyar murya ta ce ” in shigo?”

Gyaran murya yai yana ƙoƙarin saita nitsuwar sa, kusan 3 seconds kafin ya matsa daga bakin ƙofar ta shigo. Yana ƙoƙarin janyo ƙofar ya ji ta kwanta a bayan shi.

“Mijin na, abin alfahari na, jarumin namiji” ta faɗa tana wasa da kunnen sa duka biyu. A hankali ya juyo saboda gwiwowin sa da su ka yi sanyi.

“Mi ki k…”

“Shhhhh, ni ce da magana ba kai ba” ta faɗa tana sa yatsar ta ɗaya akan lips ɗin sa tana wasa da shi. Ɗaya hannun kuma ƙasa ta yi dashi tana gaisawa da abunsa da ke ƙoƙarin leƙowa waje ta cikin towel ɗin da aka rufe shi.

“Na yi ba dai-dai ba. Ka na da dukkan dama akan Yaman da ni kai na, ka yi haƙuri dan Allah. Ka yafemin My Crown, My King, My Hero, My Mr BLTD”

Zai yi magana ta rufe bakin sa da na ta. Yayin da hannun ta ya ratsa cikin towel ɗin yana yiwa BLTD wasa.

“Aysherh you know…” ya faɗa lokacin da ya samu damar breaking kiss ɗin.

Hawayen da ya gani a idon ta ya sa ya kasa ƙarasa maganar.

“Ka yafe min dan Allah” ta faɗa da muryan kuka.

Sake haɗe bakin su yai su ka cigaba da abubuwa, tuni Farida ta warware, dama hawayen na kissa ne…

………………………

Wannan cikin kam ya sa Farida cikin yanayi na saurin fushi da faɗa. Da farko farkon cikin dai abin da ɗan sauƙi amma cikin na ƙara girma abin na ƙara gaba. Ba sa sati ba su yi ƙaramin faɗa da Najeeb ba. Ga shegen kishi, sau biyu ta ke zuwa office a sati amma da ƙarfi ta maida shi duka kwana biyar ɗin. Indai ta ga mace ta shigo wajen Najeeb to haka za ta je ta zauna da su ayi duk maganan da za a yi a gaban ta. Tun Najeeb na tanka ma ta har ya haƙura ya daina kulata dan ya lura idan ya kulata ma shine ke ƙara ma ta ƙarfin gwiwa…

Bayan wata biyu da sati ɗaya Najdah ta haifi ɗan ta namiji. Ranan suna aka yiwa Najeeb takwara. A gidan sunan kuwa sai da Farida ta yi halin ta. Fauziyya sabuwar ma’aikaciya ce a Najeeb constructions, Architect ce da ta yi karatu a South Africa, asalin iyayen ta Nupawan Minna ne, amma sun jima suna zaune a Kano. Yarinyar ba ta da girman kai ga ta da yawan fara’a. Guruwa ce dan first class ta fita da shi.

A matsayinta na ma’aikaciya a Najeeb constructions ta zo sunan Najdah tunda Anas Ogan ta ne. Amma daga zuwan ta Farida ta fara yaɓa ma ta magana. Wai ta zo shishshigi da neman suna. Fauziyya ba ta kulata ba haka ta ajiye ledar da ta kawo ta fita ko babyn ba ta ɗauka ba…

Abun bai tsaya a nan ba, da dare da Farida ta dawo gida haka ta kama yiwa Najeeb faɗa wai ya turo budurwarsa ta zo ta yi gaisuwa.

“My Goodness Aysherh. Fauziyya is a staff @ the Company. Ta je gaishe da matar Ogan ta miye laifi a ciki?”

“Ni dan Allah ka koreta, ba ta min ba. Idan ta zo wajen ka ta dinga buɗe haƙora kenan tana ma ka tallan open teeth ɗin ta dan wannan ya fi ƙarfin wushirya”

“Fauziyya is good, wata biyu da ta fara aiki da mu i saw potential in her, i saw raw talent. Kuma kin san ba na ɗaukan ma’aikata sai ma su ƙwazo”

“Ni gaskiya ka koreta, ba ta min ba. Idan ba za ka iya ba ni zan koreta”

Rasa abin cewa yai ya tashi a falon ya ba ta waje…

Kwanaki su na tafiya, lokaci na gudu. Fauziyya kam tana shan magana a wajen Farida sai dai abu bai kawota office ɗin Najeeb ba. Yarinyar ba ta taɓa tankawa Farida ba, tana mugun respecting ɗin ta. Domin ta ji labarin bajintar da Faridan ta nuna lokacin da Najeeb ya ke kwance a asibiti…

…………..

Yau ma Najeeb shiryawa ya ke zai je wani taro Kaduna. Saboda faɗan da su ka yi ɗazu ya sa bai ce ta haɗa ma sa kayaba ya fara haɗawa da kan sa.
Har ta shigo ta zauna bai yi alamar ya gan ta ba.

“Wannan karan ma da Fauziyyar za ka tafi?”

Ya cigaba da abinda ya ke ba tareda ya tanka ma ta ba.

“Tambaya fa na ke dan na ga Fauziyya ce ‘yar gaban goshi a Kamfani yanzu”

” Aysherh please, ba na son tashin hankali”

“Wallahi indai da ita za ka je sai dai mu tafi tare. Ba za ayi irin tafiyar ku Portharcort ba”

Sai a lokacin ya ɗago yana kallon matar ta sa. Cikin ya sa ta yi ƙiba ga baƙi da ta yi. Ba kaman lokacin cikin Yaman ba da ta yi haske ta yi kyau, wannan kam banda faɗa ba abinda ya ke sata whilst cikinta na farko ya sa ta cin abinci kamar gara.

“Queen Aysherh, my heart belongs to you, my love is only for you. Mun je Portharcort as a team ba wai na ɗau mace na tafi Portharcort ba. Ni, Yakubu, Hassan, Peter and Fauziyya. As a team Aysherh, ki dena yi min mummunan fassara”

Ta turo baki ta ce ” to ai a hotel kuka kwana, Allah kaɗai ya san mi ya faru a wajen”

Maganar ta ma sa ɗaci, amma ya shanye dan yana ƙara magana ɗaya anan sai ta Allah, dan Farida idan ta fara masifa ka ɗauka dukan sa za ta yi. Yai shiru kawai yana sauraron maganganun ta wanda su ka fi kama da tuhuma…

……….

Washegari da sassafe ya fita, ruwan tea kawai ya sha ya fita har ya kusa kai wa bakin ƙofa ya dawo ya manna ma ta kiss a goshi ya ce ” sai na dawo”

Sai alokacin Farida ta saki ranta ta ce ” Allah ya kiyaye hanya ya dawo da kai lafiya” ya amsa da amin sannan ya fita…

Shiru- shiru har ƙarfe uku Najeeb bai kira ba bai kuma turo text ba. Ina Kano da Kaduna ace tun bakwai saura da ya tafi bai isa ba. Da farko ta ɗauka ko dan maganar jiya ne amma yanzu kam hankalinta ya tashi dan duk faɗan da su ka yi ko text zai tura ma ta ya ce ya isa.
Ta fara kiran numbar sa switch off, ta kira numbar Abdullahi dreba shima switch off. Nan jikinta ya hau rawa ta shiga kiran Mom. Tambayar Mom ta yi ko Najeeb ya kirata ta ce ma ta a’a.
Cikin kuka ta ce “Mom ki tambayamin Daddy ko sun yi magana da shi”…

Zaune su ke a falon kowa yai jugum saboda rashin sanin halin da Najeeb ya ke, da shi da dreban sa duk wayoyin su a kashe.
Daddy dai baya nan dan ya fita kai report ko zai ji labari ko anyi hatsari hanyar Kano to Kaduna.

Najma na jijjiga ɗan ta Bobo da ke kuka wayar Farida ta fara ringing Farida ta yi saurin tashi ta ɗau wayar da ke kan centre table. Ganin My Champion ke kira ya sa ta fara murmushi.

“My Champ saura kaɗan na mutu yau, ina ka shiga? Are you Ok”

“Yana nan lafiya idan har kun amince da sharuɗɗan mu” muryan wani ƙato ya doki kunnen ta.

“Waye, mi kuka yiwa mijina? Ina mijina?” Tambayoyin da ta fara jerowa kenan.

Jin maganarta ya sa Mom tashi da sauri ta amshi wayar ta sa a speaker tana faɗin ” ina Najeeb?, mi ku ke so”

Mutumin yai wata mahaukaciyar dariya sannan ya ce ” Najeeb Adam Jibo yana nan lafiya until kun fanshi ran sa a wajen mu”

” what do you want?” Mom ta faɗa tana danne hawayen ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button