SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ko zama ba ta yi ba Sabreen ta shigo. ” ba ki isa ki yi haka ba. Ba ki da matsayin da za ki kafa doka ki ce dole sai an bi ba”

Farida ta sa dariya ta ce ” na samu matsayi tun ranan da aka ɗaura aure na da Miji na Najeeb. Love of my life, my heartbeat, my champion, my handsome..” mari Sabreen ta kai ma ta Farida ta riƙe hannun.

“Ka da ki kuskura ki taɓa ni, ko kuma na sa a yanke mi ki hannu. Duk wanni matsayi da ki ke da shi outside Nigeria ya ke da tasiri. This is Nigeria ba wanda ya damu da wata karuwar Hollywood a nan. Ki tattara ki koma inda ki ka fito ko kuma idan na waiwayeki ba za ki ji daɗi ba” ta tura hannun gefe.

Yadda ta ke magana da masifa ya sa Sabreen ta ɗan ji tsoro.

“Now get out of my office”
Yadda ta yi tsawan tamkar Najeeb ne ke wannan tsawa.

Sabreen ta ce ” we’ll see” sannan ta fita.

Daga fitan ta Yakubu ya shigo.

“Haba Farida, ta ya za ki yiwa Anas haka. Anas ya mi ki halacci ta ya za ki ma sa haka?”

Wayar ta ne ya fara ringing ta duba ta ga Doctor Sadiq ta ɗauki kiran tana faɗin to gani nan zuwa. Tana gama wayan ta kalli Yakubu ta ce.

“Barinje na yi magana da likitan mijina, duk wani ƙorafin ka zan saurara idan na dawo”

Yakubu yai galala da baki yana kallon ‘yar uwartasa yadda ta koma Najeeb sak.

Jaka kawai ta ɗauka ta fita ta barshi a office ɗin…

…………

Kai tsaye ɗakin Najeeb ta wuce lokacin da ta iso. Ba kowa a ciki dan haka ta kira likitan ta gaya ma sa cewa ta iso. Kusan minti goma sai ga doctor Sadiq ya shigo tareda wani likitan.
Idon sani ta gani, idon da ba za ta taɓa mancewa ba.

“Dr Lukman ga matar patience ɗin na mu” ya kalli Farida ya ce “Aisha ga Dr Lukman wanda na miki maganar sa jiya”

“Green eyes” ta faɗa bakin ta na rawa…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣3️⃣5️⃣

“Kin san shi ne?” Dr Sadiq ya tambaya. Ba ta bashi amsa ba sai kawai kallon Lukman da ta ke, bai chanja ba ya de ɗan ƙara ƙiba da kuma gemu amma bayan nan yadda ta sanshi haka ya ke.
Lukman ya katse shirun da cewa ” ka san na zauna a Jos, itama ‘yar Jos ce”

Dr Sadiq ya ce ok barin barku. Sai da ya fita sannan ya kalli Farida da kyau. Although kayan jikin ta sun nuna tana cikin jin daɗi amma yanayin fiskarta ya nuna saɓanin haka.

“Aisha ya ki ke ya mai jikin?”

Da ƙyar ta haɗiyi miyau ta ce ” lafiya Alhamdulillah”

Ƙarasawa yai gadon Najeeb duk da ma dai kafin zuwan Faridan shi da Dr Sadiq sun shigo sun duba shi, sai dai ɗazun rashin sanin ko waye ya sa bai damu da kallon ya patient ɗin ya ke ba. Masha Allah ya faɗa chan ƙasar zuciyar sa lokacin da ya ƙare ma sa kallo.

“Yaushe ka dawo?” Farida ta tambaya tana matsowa kusa da shi.

” shekara ɗaya da ya wuce”

“Ok”

“Sai dai tun lokacin da na dawo ban je Jos ba gaskiya”

Farida ba ta ce komai ba sai bin hannun sa ta ke da ido yadda ya ke tattaɓa jikin Najeeb.

“Kinga Allah ya amsa addu’a ta ko? He’s handsome”

Maimakon ta bashi amsa sai ta ce “ka na ga zai tashi nan kusa?”

“Na duba records ɗin sa kuma na ga cewa ya taɓa motsa hannu sau ɗaya which is good news gaskiya. Insha Allah zai farfaɗo Aisha, dole ma ya tashi ya kula min da ke”

Sai alokacin Farida ta yi murmushi…

Daga asibiti dreba ya mai da ta kamfani. Tana zuwa sakatariyar ta ta miƙa ma ta resignation letter ɗin Anas. Har ga Allah ta ɗauka Anas ba zai yi haka ba. Dama so ta ke ya gane da gaske ta ke ba za ta janye ƙudirinta ba. Amma sai gashi ya ɗau abin da zafi.

Yakubu ta kira akan ya zo office ɗin ta. Bayan ya zo dai faɗa ya fara ma ta kan abinda ta yiwa Anas ga shi yanzu ta sa Anas ya ajiye aiki.
“Sai mu ga yadda za ki kula da kamfanin ba tareda Najeeb ko Anas ba”

“Akwai Allah Yakubu, da Allah na dogara kuma shi zai taimakeni”

Tashi yai zai bar office ɗin ta ce ya tsaya.

“Yakubu ka na tareda ni?”

“Farida zan ba ki goyon baya akan wani abu amma ba wannan ba”

“Ba ka yadda da ni ba ne kenan?” Ta faɗa tana matse hannayen ta.

“Mi ki ka sani gameda wannan gasa?”

“Ban san komai ba amma idan kuka min bayani zan fahimta”

“Farida abu ne mai wuya…”

“Dan Allah kar ka gujeni kamar yadda Ya Anas yai” ta faɗa tana narai-narai da ido. Ajiyar zuciya yai sannan ya ce…

……………………..

Washe gari da ta ke tunanin za’ayi yajin aiki shiru ka ke ji kamar shaho ya ci shirwa. Kowa ya kama aikin gaban sa. Ba ta jima ba Sakatariyarta ta kawo ma ta box ɗin da aka ajiye tun jiya wanda ke cike da takardu.

“Ki je ki ware min wanda su ka supporting da wanda ba su yi ba ki gayamin percentage ɗin”

Mrs Comfort ta amsa da to ta fita.

Bai fi minti talatin ba Mrs Comfort ta dawo da result
“Madam, 65% sun supporting sauran 35% kuma ba su yi supporting ba”

” ‘yan iska kawai, na gode Mrs Comfort. Yanzu ki je ki aikawa Mr Ogonna saƙo kan cewa na janye suspension da na ma sa kuma ya resuming aiki gobe”

Mrs Comfort na fita ta cigaba da duba wani littafi da ta ke ganin Najeeb na yawan dubawa lokaci zuwa lokaci idan baya aiki. Sai yanzu ta fahimci Najeeb mutum ne mai tsari. Waɗannan wa su details ne na yadda ya cimma wa su manyan projects na shi…

“Ina shegiyar ta ke?” ta jiyo muryan Najdah tana daka wa sakatariyarta tsawa.

“Ohooo! so wuyan ki yai ƙwari har za ki ce Ya Anas ya ajiye aikin sa? Who are you? Mi ki ka ɗauki kan ki ne. Idan akwai wanda ya dace ya riƙe kamfanin Big B to Ya Anas ne ba ke ba. Gold digging bitch”

Farida ta yi juyi kan kujera sannan ta ce ” idan kin gama haushin na ki dan Allah a gaida min Daddy dan ban samu zuwa gida jiya ba. Miji na baya so na bar gefen sa”

Najdah ta harzuƙa ta je gaban Farida ta sa hannu ta fara janta. Wallahi ki tashi a kan kujeran nan, ba ki dace da shi ba…” saukan mari ta ji a fiskarta wanda ya sa ta yi saurin riƙe gefen fiskan ta.

“You slapped me!”

“Idan ba ki fita harkata ba Najdah sai na sa an zane min ke. A kan ki aka fara auta ne da za ki bi ki rena mutane. Ni sa’ar ki ce? Na ce ni sa’ar ki ce?”

Farida ta koma ta zauna da kyau sannan ta ce ” ki rufe min ƙofa idan kin fita…

Najdah was so shocked da ƙwaƙwƙwaran motsi ta kasa. Ta jima tsaye kafin ta fita daga office ɗin… sai da ta fita Farida ta kalli wani hoton Najeeb da ke kan table ɗin ta ce “My champ ka ga za su haukata ni ko, Ina zaman zama na su ka ce na karɓi wannan matsayi kuma yanzu na karɓa ana min mugun kallo”…

“Najdah is my favourite sister mi ya sa ki ka mareta?”

“Ka na ganin rashin kunyar da ta min fa, dama tun ba yau ba ta ke gayamin maganganun da ta ga dama ina shareta”

“Ohooo ni da ki ke min rashin kunya kullum na taɓa marin ki?”

‘Yar dariya ta yi ta ce “Haba my champ ni yaushe na ma rashin kunya, faɗi gaskiya dai” zuwa yai gaban ta ya ja hancin ta da ƙarfi.

” ouch! My champ da zafi fa” ta faɗa tana hararan sa…

“Madam na gama aikin” muryan Mrs Comfort ya dawo da ita daga duniyar tunani.

………………………

“Daddy she slapped me fa. Daddy ka yi wani abu please”

“Na san idan ba ki ma ta rashin kunya ba ba abinda zai sa ta mareki. Ki fita a maganan kamfanin Najeeb. Karatu ne a gaban ki yanzu”

“Daddy abinda za ka ce kenan, mu zuba ma ta ido ta ɓata komai ko? I will never do that” ta tashi ta bar falon da sauri.

Waya ya janyo ya yiwa Farida text akan ta zo idan ta tashi…

Anas ne ya fara zuwa kafin Farida ta zo. Ta samu Daddy yana mishi faɗa kan ajiye aiki da yai, dan shi bai gaya ma sa ba ɗazu Najdah ke gaya ma sa da ta kawo ƙaran Farida…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button