SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Farida ta ce ” Ya Anas na gode sosai Allah ya saka da alkhairi”

Najdah ta cire girman kai ta ce ” Anty Farida, Big B yana son ki sosai, ba zai taɓa walaƙanta ki cikin hankalin sa ba, Please kar ki yi fushi da shi”

” Na gode Najdah, ku dai cigaba da tayamu da addu’a”

Najdah ta ce Insha Allah.

Sun ɗan jima kafin su ka tafi. Su na ma tunanin Najeeb zai dawo ya same su amma har su ka tafi bai dawo ba…

A ɓangaren Najeeb kuwa zuciyarsa tafarfasa ya ke lokacin da ya isa gidan su Naomi ya isketa kwance. Maureen ce ta kira shi ta sanar da shi komai.

Lokacin da Mrs Comfort ta ga Najeeb ya shigo gidan su hankalin sa a tashe ta fara tunanin kaman maganar Farida gaskiya ne. Idan ba haka ba Sir Najeeb ɗin da ta sani ɗan ƙwalisa mai ji da kan sa ba zai taɓa kallon Naomi ba balle ya damu da ita ko kuma ya so ta.

Tana gani ya ɗauki Naomi a hannun sa su ka fita tareda Maureen. Tana faɗin su tsaya amma ba wanda ya kulata cikin su…

Da su ka je asibiti gado aka ce ta kwanta sannan Likita ya duba ta daga sama har ƙasa. Da ya gama examining na ta ya nemi bahasin abinda ya faru har cirnaku su ka cize ta haka musamman a ta wajen abun ta. Maureen ta fara koro bayani akan ai wata Ogar Naomin ce ta sa ma ta cirnaku a jiki.

“Saboda me? Wannan ya kamata akai case ɗin nan gaban ‘yan sanda” Likitan ya faɗa cikin faɗa.
Maureen ta ce yanzu ma daga asibitin police station za su wuce.

Magani ya rubuta mu su na sha da na shafawa sannan aka sallamesu bayan ya rubuta mu su report da za su kai police station.

Daga asibiti Najeeb ya ce Abdullahi ya kai su police station. Abdullahi dai mamaki ya cika shi dan bai gane wannan al’amari ba daga asibiti sai police station. Ya dai cika umurni ya wuce da su…

Ganin report ɗin da su ka kawo da kuma testimony da Naomi da Maureen su ka bayar ya sa aka haɗa su da police biyu dan su je su arresting wannan muguwar mata da aka kira da Madam Farida.
Cikin su Naomi ba wanda ya ambata cewa Madam Farida matar Najeeb ne. Shi kuma Najeeb yana zaune kaman wawa duk abinda Naomi ta faɗa to daidai ne…

Motar su na gaba motar police na baya har su ka isa gida. Abdullahi dai bai san mi ya ke faruwa ba.

Maureen sai kumfar baki ta ke tana faɗin “today she go know say our madness pass her own”
Naomi kam maƙalewa ta yi jikin Najeeb wanda ke ta ce ma ta sorry…

Bayan tafiyar su Anas, wanka Farida ta yi ta gabatar da sallar Isha. Tana ma kan sallayar tana addu’a Tasallah ta shigo ɗakin da gudu tana haki.

“Baaba Tasallah lafiya?” Farida ta faɗa ganin yadda ta tsorata.

“Folisawa a falo, Folisawa suna neman ki Hajiya”

“Police kuma”

Tasallah ta gyaɗa kai.

“To ki je ina zuwa”

Tasallah ta fita, still tana tsoro dan ganin Najeeb ne ya zo da su ya sa ta ƙara tsorata da lamarin.

Farida ta cire hijabin sallar ta ta je ta ɗauko ƙarami ta saka dama gown ɗin material ne a jikin ta.

Najeeb da su Naomi na zaune a falon su kuma police ɗin su na tsaye.
Ganin Naomi ya sa ta gane dalilin zuwan police.

“Suna na Sergeant Iliya. Mu na tambaya ko ke ce Madam Farida Salihu?”

Farida ta kalli Najeeb wanda ko wajen da ta ke tsaye bai kalla ba sannan ta kalli sergeant ɗin ta ce “eh ni ce”

“Madam you are under arrest”

Farida ta yi murmushi ta ce “mu je ko”

Tasallah da ke chan wajen dining ta fashe da kuka tana faɗin “Alhaji ka yi wani abu dan Allah. Za su tafi da ita”
Ko gizau Najeeb bai yi ba balle ya sa baki.

Maureen na faɗin “evil woman. You’ll rot in jail for this”

Haka Farida ta bi bayan su suka fita. Tasallah na ihun matar gidan ne fa, mi ta yi?.
Ganin ba wannan ba ne zai fishsheta ya sa ta nufi ɗaki ta ɗau wayarta ta kira Mom…

Ganin gidan Najeeb ya ƙara haukata Naomi. Duk ciwon da ta ke ji sai ya zamana ta watsar da shi gefe, babban burinta shi ne yadda za ta mallaki wannan gida ita kaɗai…

………………………

Tun kan su isa police station ɗin Daddy ya fara kiraye-kirayen waya. Su na zuwa ma ba wani dogon bayani kawai sake Farida aka yi. Domin Comissioner of police ne ya kira ya ce a saketa.
Abinda ya ƙara sa Daddy ya tsorata da lamarin shine jin cewa Najeeb ne ya zo ya bada report sannan ya ce a arresting Farida. Gaskiya Najeeb yana buƙatar addu’a.
Farida kam har su ka iso gida ba ta ce ƙala ba. Mom ce ma ke ta aikin ba ta haƙuri.
Daddy ya ce wa Mom gobe Tasallah ta kwasowa Farida kayanta. Daga yanzu a nan za ta dinga kwana tunda abin ya kai ga haka kar su wayi gari Najeeb ya kashe Farida.

Farida sai da ta shiga tsohon ɗakin su sannan ta fashe da kuka. Tun ɗazu ma tanajin kukan, kawai ta daure ne saboda su Mom. Wai ita ce yau Najeeb da kan shi ya ke kawo ma ta police har gida.
Najeeb ɗin da lokacin da Sabreen ta sa aka kamata haka hankalin sa ya tashi ya zo police station yana masifa kaman zararre. Ta tuna first kiss ɗin su a ranan. Shi ne yau Najeeb ke gani ana tafiya da ita amma ko ajikin sa, kai duniya!…

……………………..

Washegari kamar yadda Daddy ya ce haka Tasallah ta ɗebo wa Farida wa su daga cikin kayan ta. Daddy ya ce ta fita hanyar Najeeb kar ya illata ta tun da abin ya kai ga haka.

Addu’a aka ci gaba da yiwa Najeeb dan addu’ar ce kaɗai garesu. Tasallah ba ta fasa sawa Najeeb ruwan zamzam a abinci ba kaman yadda Farida ta buƙata…

A ɓangaren Naomi duk faɗa da wani masifa da Mrs Comfort ke yi ba wanda ya shigeta. Tun da su ka shiga ɗaki ita da Maureen su ka fara shirya yadda za su kawo ƙarshen Farida saboda ma kar a samu matsala a gaba…

Bayan kwana biyu

Maureen da Naomi su ka sake duƙufa gaban Boka Ifagbemi.
Lokacin da Naomi ta gama kwararo buƙatunta Boka ya kece da mahaukaciyar dariya. Sai da yai mai isar sa sannan ya ce “a kasheta? Ko kin manta annurin matar sa ya ke gani a idon ki, ko kin manta duk ranan da Matar sa ta mutu zai dena miki kallon so?”

“To Baba ya za ayi tunda idan aka kasheta maganin zai warware?”

Boka ya fara buga ƙirji yana surkulle sannan ya ɗago ya kalli Naomi ya ce “akwai abinda za a yi amma da ɗan wahala”

Naomi ta ce ko minene za ta yi.

Boka ya miƙa ma ta wani ƙaramin ƙwarya ya ce ” ki samu gashinta ko farcenta ki sa a cikin wannan ƙwarya sai ki rufe. Da ƙarfe ɗayan dare ki toni rami ki sa wannan ƙwaryan a ciki sai ki saka saurayin kare wanda bai taɓa hawa mace ba akan ƙwaryan ki bisine tare. Yadda karen nan ya danne ƙwaryan nan haka za ta ƙarasa rayuwarta a kwance ba za ta taɓa tashi ba har sai idan wani ne ya tone ramin ya ɗaga karen daga kan ƙwaryan shi ne za ta tashi”

“Baba taya za mu gane saurayin kare da be taɓa hawa mace ba?” Naomi ta faɗa cike da fargaba.
Boka ya kwashe da dariya…

Sai da ya gama mu su bayani ya ce ” ikilo pataki. Kar ki yarda wani mutum ya gan ki lokacin da ki ke businewa”

Naomi da Maureen su ka haɗa kai wajen cewa wannan mai sauƙi ne…

……………………..

Bayan sun dawo Kano tunanin samun gashin Farida ko farcenta ya sa su ka shiga ruɗani dan da sun ɗau abin da sauƙi. Daga baya Maureen ta ba ta shawara akan su je gidan ko za su samu. Hakan kuwa aka yi. Naomi ta tambayi Najeeb ya kai ta gidan shi. Ba tareda ya musa ba ya amsa ma ta.
Suna zuwa ɗakin Farida ta ce ya kaita. Tasallah ganin tare su ke da Najeeb ya sa ba ta iya hana Naomi ba…

Su na zuwa wajen dressing mirror ɗin ɗakin ta je tana dube-dube. Ta jima tana dubawa ko za ta ga gashin Farida ko da tsilli ɗaya ne amma ba ta gani ba. Har za ta tafi ta lura da wani baƙin Comb da ke wajen da kyau ta ga akwai tsillin gashi guda biyu a jiki ta yi murmushi ta cire su…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button