SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Tana zuwa ta leƙa office ɗin Sir Najeeb amma ba ya ciki. Ta koma na ta office ɗin ta yi jugum. Ƙarfe tara saura Anas ya shigo, fiskar sa ba yabo ba fallasa.

“Yaya na ya aka yi?”

“Akwai babban matsala Farida. Kina cikin matsala, za’ayi board meeting a kan ki anjima. A ina ki ka san kamfanin VESTAC Farida?”

“VESTAC kuma?”

“Account details ɗin ki ya nuna kamfanin sun turo mi ki kuɗi miliyan biyu jiya”

Sai lokacin ta tuno da maganar kuɗi.
“Yaya ni ban san su ba, jiya nima na ga alert, abinda ya faru jiya ne ma ya sa ban yi maganar ba”

“Farida..” shigowar Najeeb ya sa ya katse maganar ya tashi ya bi bayan Najeeb ɗin.

“Allah ga ni gareka ni ‘yar marainiyar nan. Wanda ya nufeni da sharri ka mayar ma sa ya Allah. Ya Rabbil Alaamin ka ceceni” ta faɗa a fili

Ba a jima ba Najeeb da Anas su ka fito, daga baya kuma Yakubu ya zo ya kirata.
“Farida ki yi ta addu’a kawai” abinda ya iya faɗa ma ta kenan lokacin da su ka baro office ɗin na ta.

Da Bismillah ta shiga hall ɗin.

Su kusan tara ne ko goma a wajen kowa yana zaune Najeeb na tsakiyar su.
Nu na ma ta kujeran da ke tsakiyar wajen aka yi ta je ta zauna. Kowa ya zuba ma ta ido. Ba ma kaman Najeeb da ke ma ta kallon tsana.

“Miss Aisha Farida Salihu, bincike ya nuna ma na ke ki ka lalata modelling da aka yi, ki ka sa aka sace takardun zanen. Mi za ki ce gameda wannan?”

“Ni ba abinda na yi, kawai dan na shiga na ɗau hoto. Ni ba abin da na yi”

Wani a gefe ya ce ” Miss Salihu binciken mu ya nuna kin haɗa hannu da Kamfanin VESTAC domin ki lalata sunan kamfanin nan ta hanyar sace takardun zane da kuma faffasa modelling ɗin da aka haɗa”

“Ni ban san su waye VESTAC ba, jiya su ka turomin kuɗi batareda na taɓa sanin su ba”

“Ƙarya ki ke Miss Salihu, kin je bid ɗin da aka yi a Lagos tareda Mr Najeeb kuma kamfani VESTAC na ɗaya daga cikin wanda su ka je wannan bid ɗin, su na neman a basu wannan project”

” Allah ya isa na”

“Miss Salihu ga details na account ɗin ki, miliyan biyu sun shigo mi ki jiya daga Kamfanin VESTAC, mi za ki ce gameda haka? ” wani acikin su ya kuma faɗi.

“Ni kam kun sani a gaba da tambaya kamar wanda na kai ziyara ƙabari. Ni ban san VESTAC ba balle na san dalilin da za su turomin kuɗi”

Wani daga cikin su ya ɗau waya yai kira ya ce ” ku ce ya shigo”

Wani tsoho ne ya shigo, masinja ne a kamfanin tun farko-farkon buɗeshi, da ke a first floor ya ke aiki Farida ba za ta ce ta san shi ba sai dai kaman ta taɓa ganin sa.

Ce wa aka yi ya shigo yai bayani.

Ya zo ya tsaya gefen Farida saboda kujera ɗaya ne a wajen ya ce ” Ranka shi daɗe. Sakatariyar Oga Najeeb ta zo ta sameni akan an ba ta aiki amma ba ta san ya za ta aiwatar ba dan za a iya ganeta. Ta sanar da ni kamfanin Vekta”

“VESTAC” wani aciki ya gyara ma sa.

“Yawwa kamfani VESTAC sun ce ta lalata aikin da aka yi ta kuma sace takardun zane saboda ba sa so kamfanin nan ta samu wannan aiki. Sun ce za su ba ta miliyan biyu. Ni kuma ta min alkawarin za ta bani dubu ɗari biyar aciki idan na yi wannan aiki”

“Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji’oun. Tsohon banza ka ji tsoron Allah. Ni yaushe ma na taɓa magana da kai”

“Na rantse da Allah, kai na rantse da mutuwata ita ta sani na je na ɓata abun nan na kuma sace takardun zanen, ba na baku takardun ba ɗazu”

Malam Muntari irin tsofin Najadun nan ne, wanda sun yi ƙuruciyar bariki tsufan su kuma ya zo ya zama a lalace.

“Malam Muntari munji bayanin ka za ka iya tafiya”

Sai da ya fita wani da ke gafen Najeeb ya ce ” Miss Salihu kin dai ji abinda ya ce, mi za ki ce gameda abinda ya faɗa domin ki kare kan ki”

Ajiyar zuciya Farida ta yi sannan ta ce ” ni ba abinda zan ce, tunda tsoho kamar wannan bai ji tsoron Allah ya faɗi gaskiya ba ai ba abinda zan ce. Allah ne shaida ta, ni ban san VESTAC ba, wannan tsohon kuma ban taɓa magana da shi ba”

“To Miss Salihu ki ɗan bamu Minti biyar”

Har ta zauna a lobby ɗin wajen ba ta daina maimaita kalmar Hasbunallahu wa ni’imal wakil ba.

Minti shabiyu ta yi a wajen sannan a ka kirata.

Tana zama wanda ke gafen Najeeb ya ce ” Miss Salihu mun sameki da laifin ɓata sunan kamfani. Daga yau kin bar aiki a Najeeb Constructions sannan kamfanin nan tana bin ki taran miliyan biyu da rabi za ki biya cikin kwana talatin, idan ba ki amince da wannan hukunci ba ko kuma ki ka ƙi biyan wannan kuɗi to za mu shigar da ke ƙara kotu”

Kallon Sir Najeeb ta ke idon ta ya ciko da hawaye. Shima ɗin kallon ta ya ke amma wannan karan ita kan ta ba ta san kallon tausayi ya ke ma ta ba ko kallon madallah.

“Sir ka na da abin cewa?” Wanda yai maganar ɗa zu ya tambayi Najeeb…

Allah ya kaimu daren yau da rai da lafiya sai ku ji mi Sir Najeeb zai ce

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣2️⃣1️⃣

“She stays” abinda ya faɗa kenan.

“Sir amma…”

“Za ta biya taran kamfani but she stays”

Daga haka ya tashi ya fita. Tana zaune a wajen ta kasa tashi, ji ta ke kamar an kafe ƙafafuwan ta a wajen. Tana ji su na wasu maganganu a kanta da Sir Najeeb amma kuma ba wannan ne damuwar ta ba. Ita da ta ke shirin aure ina za ta samu 2.5M, ‘yan kuɗaɗen ta duk ta yi amfani da su wajen siye-siyen abubuwan biki. Ummi da Baffa Musa da wanne za su ji, da siya ma ta kayan ɗaki ko da biyan miliyan biyu da rabi.

Har su ka gama fita ba ta tashi a wajen ba sai da Yakubu ya zo.

“Farida wani hukunci su ka yanke?”

Maimakon ta bashi amsa sai ta ce “Yakubu kai ma ka yadda ni na yi abun nan?”

“Na san duk tsiyar ki iya maganar baki ta tsaya, wannan ba halin ki bane”

“Yakubu 2.5M ina zan samu?”

“Malam Muntari ɗan giya ne, zai yiwu an biyashi dan yai miki wannan sharrin ne, amma Allah ya fisu koma waye ne”

“Ni kam aikin nan nawa ake bani da mutane su ka sa mun ido a kanshi haka?”

“Akwai Allah Farida, tashi mu tafi”

Office ɗin sa ya kaita ta zauna yana daɗa ba ta baki, sai da ya ga ta samu nitsuwa kafin ya rakata zuwa office ɗin ta.

Ta zauna ne amma kaman a ƙaya ta ke, ko da ta cigaba da aiki anan, hankalinta ba zai kwanta ba domin kowa da wannan abun za a dinga ganin ta.

Tana cikin wannan tunanin Anas ya shigo.

” ‘yar uwa dan Allah ki yi haƙuri, wallahi ban yadda ke ki ka yi abin nan ba. Zan cigaba da bincike har sai na gano gaskiya”

“Ba komai Yaya na. Allah shi ne shaidata”

“Kin yi magana da Najeeb ne?”

“A’a”

“Barin sameshi”

Anas na shiga office ɗin ta yi ajiyar zuciya sannan ta jawo wayan ta ta fara dube-duben hotuna. Sai da ta kai kan hotunan modelling ɗin nan sannan ta tsaya. Hoto kawai ta je ɗauka ga shi ya zame ma ta jaraba. Tana kallon hoton ba ta san lokacin da hawaye ya fara zubo ma ta ba, hawayen da ba ta yi ɗazu ba shi ta ke yi yanzu…

“Na ji hukunci da aka yanke, amma Najeeb kai ka san Farida ba za ta iya samun 2.5M cikin 30 days ba”

Yai ajiyar zuciya ya ce “zan biya ma ta”

“No need”

“Ban gane ba?”

Najeeb yai dariya wanda ya fi kama da dariyar yaƙe.

“Ni ta yiwa laifi, so only i gets to punish her. Wannan duk formalities ne na Kamfani and i’ve cleared it up”

“Wait, ka biya ma ta 2.5M ɗin?”

“Ina da abinyi Anas, so get out”

“Najeeb are you inlove with her?” Tambayar da ta sa Najeeb ya tashi tsaye lokaci guda, cikin fushi ya ce “how dare you say that to me”

“Dude, abin ne da mamaki. Tunda Farida ta zo kamfanin nan ka chanja, when it comes to her ba ka iya taɓuka komai. What could that be if not love”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button