SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Miss Salihu” muryarsa ya doki kunnenta, ta tsaya da tafiya sannan ta juyo a hankali. Kafin ta yi magana ya sa hannu ya ɗauketa cak.
Mamaki ƙarara ya bayyana a fiskarta. Anas da ke gefe ma mamakin ne ya kamashi.

Kai tsaye motar Anas ya nufa da ita sai da ya kwantar da ita a backseat sannan ya dawo gaba ya shiga, Anas ya ja su su ka bar wajen.

Suna cikin tafiya Anas ya ce “asibiti za mu je ko gida”

“Asibiti” Najeeb ya faɗi a hankali….

Ƙarfe goma da rabi su ka baro asibitin bayan an duba ƙafar Farida. Ganin an yi wata hanya da ba ta gidan su ba ya sa ta ce ” Ya Anas ka kaini gida ina so na ga Ummi na. Na san tana chan hankalinta ya tashi”

Anas ya ce ” ai su Baffan na ki su na gidan su Najeeb”

Ba ta sake cewa komai ba har su ka isa gidan su Najeeb.
Ana jin tsayuwar mota gaba ɗaya aka fito dan dama duk iyalen gidan a matse su ke. Baffa Musa, Yakubu da Ya Faruƙ su ma suna nan suna jiran dawowarsu. Dama tunda abin ya faru su ke sintiri tsakanin gidan su Najeeb. Ummi ta so ta biyosu Baffa Musa ne ya hana…

Najeeb ne ya fara fitowa da sauri ya buɗewa Farida ƙofa ya taimaka ma ta ta fito duk da kuwa yanzu ƙafar ta rage zogi.

Baby ce ta fara zuwa da gudu ta rungume Najeeb kafin sauran su ka ƙaraso.

Baffa Musa abinda bai saba ba yau ya yi. Shima zuwa yai ya rungume Farida yana hamdala. Ita kaɗai ce ɗiyar ɗan uwansa, ita ya ke gani ya tuna da ɗan uwansa.

Daga compound ɗin gidan Baffa Musa ya ce za su wuce gida. Dad ya ce su bari sai da safe tunda dare ya yi. Baffa ya ce ” Alhaji ai idan ban kai ‘yar nan wa uwarta ba, uwarta za ta iya haɗiyar zuciya. Bari mu tafi kawai”
Musabaha su ka yi da Dad sannan su ka wuce wajen na su Motar. Yakubu ne ya tallafa ma ta har su ka isa wajen motar Baffan…

Idan ka cire yara ƙanana duk sauran kowa idon sa biyu saboda jiran dawowar Farida. Su Baffa ba su iso gida ba sai sha biyu saura na dare.

Su ma ɗin daga bakin gate aka taresu. Farida ta rungume Ummi tana kuka Ummin ma na yi. Da kyar aka raba su.

Wanka da ruwa mai zafi ta yi, ta gasa jikinta sosai, ta jima a banɗakin dan kwana biyu kenan ba wanka. Tana fitowa Ummi ta sa ta a gaba da abinci. Allah na gani bacci ne yanzu a idonta ba abinci ba amma da Ummi ta takura dole ta zauna za ta ci.
Ummi ta ƙarɓa cokali ta fara ba ta abincin a baki. Hakan ya sa Farida ta tuno lokacin da Sir Najeeb ke ba ta abinci, haka kawai sai ta tsinci kan ta da murmushi.

????SAKATARIYA TA????
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Free page

0️⃣1️⃣0️⃣

Tana tsaye jikin balcony na gidan tana kallon mai yankan flower wanda ke faman gyara flowers ɗin gidan, ya saƙalo hannunsa ta ƙugunta sannan ya manna ma ta kiss a wuya ya ce “do you like it?”

“Gidan yai kyau sosai. Its perfect” ta amsa ma sa

Juyo da ita yai ya ce”This is our home Aysherh”

Murmushi ta yi ta manna ma sa light kiss sannan ta ce “our home is beautiful my love”….

A hankali ya buɗe idonsa wanda su ka ma sa nauyi saboda gajiya, ya rufesu saboda hasken da ya karaɗe ɗakin yaiwa idonsa ƙarfi. Ɗan wasu daƙiƙai ya ɗauka kafin ya sake buɗe idon a karo na biyu.
Lokaci guda kuma mafarkin da yai ya dawo ma sa. Da sauri ya tashi zaune saboda tunowa da yai da abinda ya gani a mafarkin. Agogo ya duba ya ga ƙarfe shaɗaya na safe, kenan ya jima yana barci. Idan ya tuna da kyau to ba maganin bacci ya sha ba jiya. Ya shigo ɗaki, ya taking hot shower ya sanya jallabiya ya gabatar da sallar maghrib da Isha, kaman yana azkar bacci ya tafi da shi. To wa ya maidashi kan gado? Ya janye tunanin ta hanyar tashi ya shiga banɗaki…

Fitowar da zai yi bayan ya shirya cikin ƙananun kaya baƙar shirt da guntun wando baƙi na jeans ya haɗu da Mom tana haurawa sama.

“Son ya jiki?” Ta faɗa a hankali

” lafiya Justice” ya faɗa ba tareda ya kalleta ba.

Mom ta bishi da ido tana haɗiye wani abu mai ɗaci da ya taso ma ta tun daga wuya.

Adama ya samu tana goge-goge a falo.

“Hey ina baby?”

“Sir ta tafi makaranta”

“Dad fa”

“Yana waje”

Fita yai daga falon dan ya san inda zai samu Dad ɗin.

A wajen gazebo da ke garden ya samu Dad, yana zaune yana karatun littafi.

“Come here son” Dad ya faɗi lokacin da Najeeb ke ƙoƙarin zama a ɗaya kujeran.
Zuwa yai ya tsugunna a gaban Dad, Dad ya manna ma sa peck a goshi ya ce “Allah ya ma ka albarka”
Najeeb ya amsa da Amin

“Ya jikin na ka?”

“I’m fine Dad”

“Allah ya ƙara sauƙi”
Dad ya ajiye littafin ya fara bayani

“Ka ga irin abinda na ke gaya ma ka ko. Joseph ya ce korarsa da ka yi shi ya sa shi ɗaukan wannan mummunan mataki a kan ka. Ɗa na, ka dinga danne zuciyarka kana haƙuri da mutane, Allah ya baka ɗaukaka da daraja ne domin ya jarrabaka. Su wanda su ke ƙasa da kai akwai haƙƙin su akan ka kuma Allah zai tambayeka ranar gobe”
Ƙaran wayan Dad ne ya katse hirar ta su. Yana ɗauka ya ce ” to muna shigowa”

“Najeeb, Hajiya ce ta zo. Mu shiga ciki”

Ba mu su ya tashi su ka jera da Dad ɗin.

Hajiya Mama da kan ta ta yiwa Najeeb girki ta kawo, wai dole sai ya cinye dan ta san bai ci abinci ba a chan. Haka ta tisa shi a gaba yana cin abinci tana tambayarsa gameda kwana biyun da yai a hannun su Joseph. Mom na gefe tana kallon su, kwaɗayin wannan dama da ta rasa ta ke yi, hira tsakanin uwa da ɗa.
Ko sai yaushe Najeeb zai ba ta dama ta gyara kura-kurenta na baya?…

……………………

Da yamma Yakubu ya kawowa Farida wayarta wanda aka samu a gidan da aka tsaresu duk da kuwa an yarda sim ɗin ciki.

“Anas ya ce zai zo ya gaishe ki bayan sallar isha”

“Allah ya kawoshi lafiya” ta faɗi tana cin farfesun kayan cikin da Ummi ta haɗa ma ta…

Tana sallar Isha aka kira wayar Maijiddah. Maijiddah ta duba numbar ta ja tsaki ta ajiye wayar gefe.
Kwana biyu kenan Aneesa matar AbdulWahab tana damunta da kira da texts, ranan da ta fara kira ba irin ɗibar albarkar da ba ta ma ta ba. Gashi ita ba mai iya maida magana bane, haka ta gama zagin ta kashe wayar. Lokacin jimamin rashin Farida ya sa ba ta wani damu da abinda Aneesar ke ma ta ba.

“Matar AbdulWahab ce ta kira ki ko?”

Maijiddah ta gyaɗa kai.

“Ban wayar na bata amsar maganganunta”

Maijiddah ta langwaɓe kai ta ce ” Anty dan Allah ki barta. Idan ta gaji za ta bari”

“Hmmm a tarihin rayuwata ba na gani in ƙyale dan haka bani wayar kawai”

Maijiddah ta miƙo wayar dan ba yadda ta iya.
Bugun farko ba a ɗauka ba sai a na biyu.

“Assalamu Alaikum Uwargida ran gida, da fatan kina ta shirye-shiryen zuwan amarya?”

Daga ɓangaren Aneesa ta ce ” who’s this?” Dan muryan bai yi kama da na Maijiddah ba wacce ranan farko da ta kirata haƙuri ta dinga ba ta.

“Aisha Farida ce, yayar Amarya Hauwa Maijiddah. Na kira ne in gaya mi ki kar ki kuskura ki sake kiran ƙanwata saboda naga alama ƙwaƙwalwar kifi ce a kwanyar ki”

“Ke! ƙaramar karuwa ki kiyayi bakin ki. Ki kuma ja wa ƙanwar ki kunne karta yadda ta shigo gidana”

“Ashe ke Jaka ce, daƙiƙiya, Tinkiya mai kamar Aladu. Har kin isa ki hana Jidda zuwa gidan ki. Idan ba kwartonci ba, mijinki na Lagos kin maƙale a Abuja wai ke sarkin aiki. To tunda ke bakisan yadda ake riƙe miji a tarairayeshi ba, shi ya samu wacce za ta zauna kusa da shi ta kula da shi. Kuma wallahi wallahi ki ja girman ki ki dena kiran ƙanwata ko kuma mazaunanki su yi tsami”

Yadda Farida ke magana da faɗa-faɗa ya ƙara tunzura Aneesa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button