SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Tana shiga ta tadda baƙi sun cika falon ƙasa, kusan ba zai fi mutum biyu ta gane a ciki ba sauran duk baƙin fiska ne a wajen ta. A tsanake su ka gaisa kafin ta haura sama.

Wanka ta yi da ruwan zafi saboda jikinta da ke ma ta ciwo. Bayan ta fito ta shafa mai ta ɗau wata atamfar ta riga da skirt ta sa. Dariya ta farayi lokacin da ta kalli kan ta a madubi ta ga yadda kayan ya ma ta ruwa. Gaskiya yanzu kam ta yarda ta rame sosai. Cire kayan ta yi ta je ta ɗauko wani Anarkali gown kalar abin cikin ƙwai, zanen adon flowers da ke jikin kayan kuma ja. Ba wani kwalliya ta yi ba powder ce kawai da kwalli, sai ta ɗan goga jan lipstick kaɗan a lips ɗin ta. Tana yafa gyalen tana murmushi. Ta ya ba za ta yi farin ciki ba, taya fiskarta ba zai zamo ma’abocin murmushi ba akoda yaushe. Kaman yau fa ta ke cikin nishaɗi saboda first kiss ɗin su, gashi duk da matsaloli da su ka fiskan ta, duk da ƙaddara da ta afka mu su. Allah ya sake dawo da wani ranan da su ka sake sharing kiss. Akwai lokutan da ta ke jin kaman ba zai tashi ba amma sai ta dake ta dinga maimaitawa kanta cewa ita da Najeeb akwai rayuwa mai tsawo a gaban su, rayuwa mai tarin farinciki da annashuwa, rayuwa da za su ga ‘ya’ya da jikokin su.
Wani abu ta tuno da ya sa ta rufe fiskan ta tana murmushi. Tana kuma fatan Allah ya sa wannan rana ta iya jurewa ta daure ta faranta ma sa rai sosai…
Kiran Ummi ne ya katse ma ta dogon tunanin da ta tafi.

“Mun iso gidan na ku ki fito ki shigo da mu”

“Ummi na yaushe a gari? Shi ne ba ki ce za ki zo ba”

“Ba na son surutu ki fito yanzu, ba ni ɗaya ba ne harda su Baaba Sabuwa”

“Yeeeeh, ganinan zuwa”…

Taro ne da ya haɗa manya-manyan mutane, ‘yan uwa da abokan arziƙi. Wanda aka gayyata da wanda su ka zo gayyar soɗi duk an cika garden ɗin maƙil. Manya manyan tents huɗu aka kafa amma sun cika maƙil har ma wassu ba su samu wajen zama ba.
Abinci kam Masha Allah domin anyi varieties kala-kala, caterers aka ɗauko su ke serving mutane abincin.

Malami aka kira ya fara buɗe taro da addu’a kafin Daddy ya yi jawabin godiya da kuma farinciki da ya ke ciki a yau. Daddy yai hawaye lokacin da ya ke bayyana halin da su ka shiga da Najeeb ya shiga coma, tun ana irga kwanaki da satuttuka aka koma irga watanni, daga ƙarshe ma da Allah ya tada shi sai da aka yi kusan wata biyu cur kafin ta kai har yau yana tafiya normal, yana magana yana kuma gane mutane, gaskiya abin godiya ne. Bayan ya gama jawabi aka kira Najeeb. Najeeb ya karɓi mic yai taƙaitacciyar jawabi wanda godiya ce ga dukkan wanda su ka taya shi da addu’a da kuma wanda su ka dinga ware lokutan su mai muhimmanci su na zuwa dubashi a asibiti bayan sun san ba ganin su zai yi ba balle ya ji su. Har ya miƙawa MC mic ɗin sai kuma ya ƙarɓa ya ce “Aysherh Farida Salihu should please come here”

Farida na zaune kusa da su Ummi ta ji abinda ya ce. Dama tunda ya fara magana hankalin ta ke kan shi.

“Mrs Jibo” ya sake kira.

Duƙar da kan ta ta yi tana ƙoƙarin danne hawayen da ke shirin zubo ma ta.

“Farida ba za ki je bane?” Muryan Ummi ya doki kunnen ta.

“Mrs Jibo please come out” ya sake maimaitawa.

A hankali ta ke tafiya kan ta a ƙasa, ba wai kunyan mutanen wajen ta ke ji ba. Abubuwan da su ka faru ne su ke mata zirya a ƙwaƙwalwar ta.

Tana isowa wajen da ya ke ta ɗaga ido ta kalleshi, shi ma ɗin ita ya ke kallo. Hannunta ɗaya ya kama ya jawota kusa da jikin sa sosai.

“Ga wanda ba su san wacece wannan ba, ko su ke tunanin minene alaƙata da ita. To dai Aysherh Farida Salihu sakatariya ta ce”

Wurin ne ya ɗau hayaniya, domin dayawa sun san Farida matar sa ce.

Ɗan murmushi Najeeb yai wanda ya ƙara bayyana kyaunsa.
Ƙirjin Farida ya fara bugawa da sauri-sauri.

“Then she became my wife. Auren mu bai cikata wata biyu ba na yi hatsari na shiga coma, i was unconcious for months. Kun san mi ta yi?”

Aka haɗa ba ki aka ce a’a

“Ta jira ni, ta kula min da gida da dukiya, ta aiwatar da duk wani responsibility da mata za ta yiwa mijin ta. Ba ta gujeni ba, ba ta ƙyamace ni ba, ba ta kuma nemi rabuwa da ni ba in my vulnerable state. Ba ko wace mace ba ce za ta iya abinda Aysherh ta yi. Ina so ku sani cewa Aysherh jaruma ce, she always fight and she always win”

Ya kalli Farida da ke kallon ƙasa idon ta na hawaye, ya sa hannu ɗaya ya goge ma ta hawayen da ke fiskar ta.

“Thank you Aysherh, Thank you for everything”

Fashewa ta yi da kuka me haɗe da dariya, Ya jata jikin sa ya rungumeta. Gaba ɗaya wajen aka sa tafi…

Anyi ruwan hotuna kam kamar ba gobe har sai da Najeeb ya gaji da tsayuwa. Ƙarshe da ya ji hajijiya na kama shi ya excusing kan sa ya bar wajen.

Yana ƙoƙarin shiga gida sai ga Sabreen ta biyoshi.

“Noory”

Juyowa yai ya kalleta yana jin haushinta na taso ma sa tun daga ƙasan zuciyar sa.
Lokacin da ta iso ya yi ƙoƙarin sake fiskar sa ya ce “Sabreen”

“Noory na san na yi laifi a baya kuma kana fushi da ni amma ka sani har yanzu ina son ka. Ba zan taɓa son wani kamar yadda na so ka ba. I love you Noory, Please give me another chance”

Kamar ya shaƙota ya haɗata da gini ya ke ji amma ya dake ya ce “i still have feelings for you Sabreen, but you know i have a wife now”

Marairaice murya ta yi ta ce ba ta damuba ta ƙara da cewa “I want to be your wife too, ko da ta biyu ce ba matsala”

Najeeb yai murmushi ya ce ta bari idan komai ya lafa zai wa su Daddy magana.

Murmushi ta yi ta zo za ta rungumeshi ya ce “we’ll talk later”

Har ya shige ba ta bar murmushi ba. Ba ta ɗauka Najeeb zai ƙarɓi bukatan ta da wuri haka ba…

Yana shiga ɗakin su ya ga komai na nan yadda ya ke, ya kalli kayan da ta bari a kan gado riga da skirt na atamfa wanda ta sa da fari kafin ta chanja su.

“Clumsy Aysherh, will she ever change?” ya furta a fili…

Farida kam sai da ta ga bayan taro, domin jama’a sun ma ta chaa kowa yana jinjina ma ta kan namijin ƙoƙarin da ta yi. Tun daga ‘yan uwan Najeeb na ɓangaren Daddy da su ka zo daga Gombe zuwa ‘yan uwan Mom da su ka zo daga ƙasashe daban-daban. Mom ta nuna ma ta yayun ta biyu maza da kuma cousin ɗin ta mahaifin Sabreen. Farida kam baki har kunne domin kyauta kam ita kan ta ba ta san iyakan abinda ta samu ba…

Ƙur’ani ne a hannun sa yana karatu lokacin da ta shigo ɗakin. Yadda ta ke jin jikinta idan ba ta je ta watsa ruwa ba ba za ta ganema kan ta ba.

“Aysherh”

Ya kira sunan ta.

Ta juyo ta kalleshi har da lumshe ido.

Yatsa kawai ya ɗaga ya nuna ma ta kan gado. Bin yatsar ta yi da kallo har idon ta ya sauka kan kayan ta da ke kan gado.

“Ba na son ƙa…”

“Na sani- na sani. Kawai dai su Ummi da su ka kirani ne ya sa ban ɗage kayan a wajen ba, Mr ba na son ƙazanta” tana faɗa tana tattara kayan.

“Kai fa ka dawo kenan ka yi ta yiwa mutane gadara da ɗaki, bayan ɗakin na mu ne mu biyu”

Bai kulata ba ya cigaba da karatun da ya ke yi…

Bayan ta fito daga wanka ta sa wata ƙaramar riga wanda ko rabin cinyar bai gama rufewa ba. Ƙaton hijabi mai hannu ta sa ta zo ta ɗau sallaya ta tada sallah. Lokacin da ta idar ba ya ɗakin. Ba ta san ya aka yi zuciyar ta ya raya ma ta kaza ya je nemowa ba. Haka kawai ta tashi ta fara duba hammata da gabanta ko ta yi waxing na shi da kyau, ba ta so ya kalleta ya faɗa ma ta kalmar da ke baƙanta ma ta rai ɗin nan “Mrs Jibo ba na son ƙazanta yanzu kuma Aysherh ba na son ƙazanta”
Ta girgiza kai ganin komai na nan tsaf-tsaf ba ta jima da gyara wajen ba.
Ta fesa turaruka a ɗan filingin kayan na ta, sannan ta shafa turarukan jiki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button