SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Anty Farida wani mai ƙatuwar mota yana kiran ki a waje. Maijiddah ke kuma wai inji Rashidan Bala wai za ta samu kitso?”

“Zo nan Sadiƙ” Farida ta faɗa tana kallon molelen kan yaron da ya sha aski.
Yana zuwa ta kama shi ta ma sa dundu uku a baya.
“Ban hana ku kiran Maijiddah da sunan ta ba? Eh. Mi na ce ku dinga ce ma ta?”

Yaron cikin kuka ya ce “Anty Maijiddah”

“Good boy. Yanzu ka je ka cewa Rashida, Anty Maijiddah ta dena kitso”

Yaron ya fita yana kuka yana ƙoƙarin sosa bayan sa….

Ba ta gane motar wayeba amma ta san koma waye to babba ne. Ba ta tunanin kuma Alhaji Hussaini ne, wanda ta haɗu da shi a wajen aiki ya zo wajen Sir Najeeb ya nace ya nemi numbarta, sai da ta sissilleshi sannan ya haƙura ya dena kiran ta.

Tana ƙarasawa jikin motar ta zagaya wajen driver ta ƙwanƙwasa glass ɗin saboda tinted ce ba ta ga wanda ke ciki ba. Ɗan sauke glass ɗin aka yi sannan aka miƙo ma ta waya, tana ganin hannun ta ce “Sir Najeeb!” sai kuma ta yi saurin rufe baki tunowa da ta yi da abinda ta yi a office yau.

Ƙarasa sauke window ɗin yai sannan ya ce ” Miss Salihu karɓi wayan ki”

Ta yi saurin karɓan wayan sannan ta ce “na gode Sir” bai ce komai ba ya ja motar sa ya tafi…

“Kaman motar Sir Najeeb na gani ɗazu a ƙofar gida”

“Shine. Waya ta ya kawomin”

Da mamaki Yakubu ya ce ” Sir Najeeb ɗin?

“Iyi”

“Sir Najeeb ya kawo mi ki waya har gida”

“To miye aciki, ni ba sakatariyar sa ba ce”

Shiru Yakubu yai yana tunanin ko dai gulman da ake yi a office gaskiya ne. To idan ba haka ba Sir Najeeb ɗin da ya sani a da kam bai damu da damuwar kowa ba, kan sa kawai ya sani. To idan kuma akwai abu a tsakanin su fa? Baba ya ce a ƙarshen watan December za ayi bikin Farida.
Farida ce ta katse shi da cewa “yawwa Yakubu ka san numbar nan?” Ta nuna ma sa numbar NJ. Ɗaukan numbar yai ya sa a wayarsa sai dai bai da irin numbar ma a wayarsa…

……………….

Fitowar sa kenan daga wanka ya ganta zaune abakin gadon sa.

“What are you doing here?”

“Son, Kakan ka ya rasu da safiyar yau” ta faɗi cikin muryan kuka

“Allah ya ma sa rahama”

“Zan wuce Bahrain gobe. Za ka je?”

“i’m busy” ya faɗa a taƙaice

“Saboda ni ko saboda Sabreen ne ba za ka je ba”

“Enough Justice Nabilah. Ki fita min a ɗaki”

“Najeeb please” Mom ta faɗa kamar za ta yi kuka.

“Ke ko Sabreen, ba ku da wani matsayi da zai sa na yi abu ko kar na yi abu”

Hawaye ne ya gangarowa Mom ta yi saurin sharewa ta ce ” sai yaushe za ka yafe mi ni”

“When you are ready to tell the truth”

“Najeeb!” Ta faɗa da ƙarfi.

“Oh, Justice ki na tsoron gaskiyan ne?”

Shiru Mom ta yi tana ƙoƙarin maida hawaye.

Sai da ya ga ta fice ɗakin sannan ya sauke numfashi, zama yai a bakin gadon lokaci guda jikin sa ya fara maƙyarƙyata, abinda ya gani shekaru ashirin da ɗaya da su ka wuce ya fara dawo ma sa. Duk yadda yai ya manta da komai ya ka sa. He was only thirteen amma yana iya tuna komai harta fiskar wanɗanda su ka ɗau gawan a ranan…

……………

Washe gari da wuri Farida ta je office ta ajiyewa Najeeb takarda a table ɗin sa. Bai fi minti shabiyar da isowarta ba sai ga shi ya zo. Tana gaishe shi ma amma ko kallon ta bai yi ba. Sai da ta bashi minti biyar sannan ta bi bayan shi. Takardar ne a hannunsa lokacin da ta shigo.

“Sir na san na yi laifi amma ka yi haƙuri dan Allah”

Ya na so ya ma ta faɗa, ya na so ya nuna ma ta ko shi waye, amma ba zai iya ba saboda ransa da ke a ɓace saboda kuma…

Cillar da takardar ba da haƙurin da ta rubuto yai sannan ya ce ” get back to work”

Ta yi mamaki da bai yi masifa ba ita kam hutarerenta ai. Har za ta fita sai kuma ta lura da yanayin sa kaman ba shi da lafiya ko kuma akwai abinda ke daminsa dan tsakanin jiya da yau ya chanja ma ta gaba ɗaya.

“Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?”

“Get out Miss Salihu”

Simi-simi ta fita kar ma ta tunzura shi ya ce zai hukuntata.

Ya fara duba wasu takardu amma hankalinsa ya kau, tunanin kyakyawar fiskarta ya ke da murmushinta mai shiga zuciya. Ya missing ɗin ta sosai, Aysherh ya furta a hankali.

Ya na mamaki da Aysherh Farida ba ta da sanyi da haƙuri irin na Aysherh. Halin su ya sha banban duk da kuwa sunan su ɗaya….


Aisha Mustafah Jibo ta taso cikin soyayya da kulawar iyaye da ‘yan uwanta. Kasancewarta kurmiya bai rage ma ta komai ba na jin daɗi a wajen iyayenta. Gata kam tana samu tun daga kan Alhaji da yayyanta ga uwa uba uwar da ta shayar da ita wato Hajiya Mama.

Karatu mai zurfi Alhaji Mustafah ke so Aisha ta samu saboda ya zamo ma ta gata ko ba sa raye, wannan ya sa ya turata ƙasar waje karatu wajen yayanta Adam. Komai cikin sauƙi Adam ya nema ma ta tundaga dreba zuwa ma su kula da ita a gida saboda shi da Nabilah ba zama su ke ba. Sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin Aisha da yaran Adam musamman Najeeb wanda ke da shekara tara a lokacin. Kamar wata babbar yayarsu su ka ɗauketa hakanan itama ta kan zama yarinya acikinsu duk da ita ɗin ma ba wai ta girme su da yawa bane dan shekararta goma shabakwai.
Yaran da sun dawo daga makaranta su na maƙale da ita, za ka gansu da biro da takarda suna hira da Aisha ko kuma suna wasa. A hankali har su ka iya maganan kurame ya zamo idan za su yi magana ba sa buƙatar su rubuta sai dai su yi yaren kurame.
Shekaru biyu kenan da komawar Aisha wajen Adam. Duk hutun ƙarshen shekara ta ke zuwa gida amma su Alhaji da Hajiya Mama su na kawo ma ta ziyara lokaci zuwa lokaci. A wannan ƙarshen shekaran da ta je ta tarar Alhaji ba lafiya. Nan ta tubure akan ba za ta koma America ba sai dai ta zauna kusa da Baban ta.

Adam daga Belgium ya taho dubiyan Alhaji saboda a lokacin an maida shi chan. Zuwan sa kuwa ya tarar jikin Alhaji yai tsanani. Shi da su Sulaiman su ka fara yunƙurin yadda za a yi su turashi ganin likita a ƙasar waje sai dai shi Alhajin ya ce ba inda zai je. Ana gobe Adam zai koma Alhaji ya nemi alfarma a wajen sa duk da alfarmar ta zo ma sa bazata amma Alhaji ya fi ƙarfin haka a wajensa dan haka ba tareda ya ja ba ya amince. A yammacin ranan aka ɗaura auren Adam Usman Jibo da ‘yar uwar sa Aisha Mustafah Jibo. Washegari ya koma saboda jikin Alhajin ya fara sauƙi dan an sallamoshi daga asibiti.
Kwana uku da tafiyar Adam, Alhaji ya rasu mutuwar da ta girgiza ‘ya’ya da ‘yan uwansa musamman Aisha.

Sai da aka yi da gaske kafin Aisha ta yarda ta koma karatu duk da kuwa ta san da auren Adam a kanta dan Alhaji ya gaya ma ta kafin ya rasu.

Larabawa da shegen baƙin kishi, tunda Adam yai wa Nabilah bayanin aurensa da Aisha sai ta tuɓure ma sa ta ce ita ba ta san zan ce ba. Sosai abin ya jawo rikici tsakanin su.
A da ba ta shiga harkan Aishan dan ba ta da lokacin ta amma tunda ta zamo matar Adam sai abin ya chanja, kullum cikin tsangwamarta ta ke. Ta kori dreba da mai kula da ita da Adam ya ɗauka ma ta, ta hana yaranta kulata amma Najeeb bai daina ba sai ma ƙara jin son Aishar da ya yi.
Lokaci guda Aisha ta chanja kullum sai ta yi kuka a ɓoye saboda indai Najeeb ya ganta cikin ɓacin rai to sai ya yi ta tambayar ta dalili haka shima ranan ba za a gane ma sa ba.
Allah-Allah Aisha ta dinga yi ta gama makaranta ta bar mu su gidan ta koma Nigeria.
Shi Adam a nashi ɓangaren duk lokacin da ya zo yana ƙoƙarin ganin komai ya tafi dai-dai sai dai ita Aisha ba ta nuna ma sa tana cikin matsala haka nan Nabilah ma tana nuna komai na tafiya dai-dai.
Ganin ba abinda ya ke shiga tsakanin su ya sa Nabilah ta ɗan saki ranta kaɗan, sai dai shi a nashi ɓangaren ganin Aisha na karatu ya sa ya bari har sai ta gama tukunna ya tare da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button