SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Yadda Daddy ya ke magana cikin kwantar da murya ya sa Malam Abdullahi yarda da maganar sa domin Daddy babban mutum ne a gari kai a ma ƙasar gaba ɗaya ba zai yiwu ya zo wajen sa dan kawai ya ma sa ƙarya ba.

“Alhaji na fahimceka, sai dai gaskiya al’amarin nan ya riga ya ɓaci. Ni da Alhaji Musa mun samu saɓanin harshe a yau ɗin nan saboda wannan magana. Yanzu haka maganar da na ke maka an riga an dawo mana da sadaki da kuma kayan lefe da aka kai. Harta kayan yarinyar da aka kai gidan yarona sun je sun kwashe. Al’amarin ya ɓaci sosai gaskiya”

“Malam Abdullahi a duba dan Allah. Auren nan idan aka fasashi alhakin yarinyar nan zai bi Najeeb ‘ya’ya da jikokin sa”

“Gaskiya zan faɗa ma ka Alhaji ko da za a dawo da bikin nan to ba gobe ba”

Shiru Daddy yai na tsawon lokaci kafin ya ce wa Anas su tafi.

………………………

Su Baffa da su Ummi sun zo asibitin da aka kwantar da Farida. Baffa kam a lokacin ma ya ƙara tabbatarwa kan sa ko mi zai faru to gobe sai ya aurar da Farida, domin idan gobe ta wuce bai san halin da Farida za ta shiga ba, balle ya san halinta yanzu sai ta ce ta haƙura da aure gaba ɗaya ta ce karatu za ta cigaba da yi.

Bayan ya tabbatar da ankawo duk abubuwan da za su buƙata sannan ya musu sai da safe saboda ance sai gobe za a sallameta. Ya zo zai fita daga asibitin da shi da Yakubu su kuma su Daddy su ka shigo.

“Alhaji Musa dan Allah ka tsaya” Anas ya faɗa lokacin da ya ga Baffa Musa ya gan su amma sai ya kau da kai yai kamar bai gan su ba.

Baffa Musa ya juyo ya kalli Daddy yana ƙarasowa wajen su, girman sa ya sa ya fasa masifar da ya ke shirin yiwa Anas.

“Alhaji Musa dan Allah ko za mu iya magana da kai”

“Ni yanzu gida zan wuce Alhaji, ina sauri”

“Ba komai Alhaji Musa za mu bika gidan”

Baffa Musa dai bai so ba amma ba yadda ya iya. Haka su ka wuce gaba, su ma su Daddyn su ka bi bayan su.

Daddy da Baffa Musa ne a falon. Yayinda Anas da Yakubu ke ƙofar gida suna tattauna wannan abin al’ajabi mai kama da almara.

Duk girman Daddy da matsayin sa haka ya fara yiwa Baffa Musa magana cikin sanyi da harshe mai taushi.

“Alhaji Musa dan Allah ka duba wannan al’amari. Na yiwa Malam Abdullahi magana kuma ya ce za su duba, kar a fasa auren nan gobe dan Allah”

“Aure ai ba za a fasa shi ba, kamar yadda na gayyace ka da farko ba chanji. Gobe ƙarfe shaɗaya na safe za a ɗaura auren Farida da ɗa na Yakubu. Tunda sun shaƙu da juna idan anyi auren za su fahimci junan su sosai”

“Alhaji idan ka yi haka ba ka yafe ba kenan”

“Alhaji ko ka san ni ɗin nan ni na shiga na fita har na ga na amso takardar Farida saboda ɗan shege mu ka aura ma ta ba mu sani ba. Yanzu kuma ace duk walaƙancin da iyayen Rayyan su ka mana sai na ba su auren Farida. Wallahi ba zai yiwu ba, gara ayi tuwona maina kawai “

Daddy yai shiru yana tunani chan ya ce ” Alhaji Musa ina neman alfarma a wajen ka”

Zumɓur Baffa Musa ya tashi lokacin da ya ji buƙatar Daddy.

“Wannan zancen banza kenan, ba zan taɓa yiwa Farida auren cin fuska ba. Allah ya kiyaye”

“Alhaji Musa ka taimakeni dan Allah, yaron nan inaga son ta ya ke shiya sa yai haka”

“Alhaji ka tashi ka tafi dan Allah, abinda ka ke buƙata ba mai yiwuwa ba ne”

Maimakon Daddy ya tashi sai ya sa gwiwowinsa a ƙasa yana roƙon Baffa Musa. Tuni Baffa ya fara ƙoƙarin ɗaga Daddy yana faɗin “haba Alhaji ka fi ƙarfin haka, dan Allah ka tashi”

“Yaron nan yadda ka ke so ka ga ka aurar da Aisha haka nima na ke so yai aure. Nan da ‘yan kwanaki zai cika shekaru talatin da biyar a duniya kuma har yanzu ba shi da niyyar aure. Shi kaɗai ne ɗa na namiji Ba na fata ya ƙarasa rayuwar sa a matsayin tuzuri”

Baffa dai rasa mi zai ce zai yi dan kan sa ya kulle. Alhaji Jibo ya girmeshi a shekaru nesa ba kusa ba ya girmeshi a matsayi da komai amma shine ya ke roƙon sa har kamar zai yi kuka. Farin cikin Farida ya ke so amma idan ya amsa buƙatar Alhaji Jibo anya ba baƙin ciki zai shuka a rayuwar Farida ba….

……………………….

Bayan fitan su Daddy ya shiga wani tashin hankali, bai taɓa ganin Daddy cikin ɓacin rai haka ba, he only mean to punish her. So ya ke idan an fasa auren ta yi kuka ta ji baƙin ciki sai ya koma ya nuna wa mahaifin Rayyan gaskiyar lamari cewa hotunan nan aikin photoshop ne. But is he stupid or what, idan ya je will that undo what has already been done.
Ya kira Anas sau ba adadi amma ya ƙi ɗauka. Ya fito da robar maganin sa ya ɗauko guda biyu sai kuma ya maida su. Ashe Daddy ya san halin da ya ke ciki all this while, shi bai san Daddy ya san da zuwan sa wajen theraphist ba, balle har ya san he has being on drugs all this while.
Duk da hasken da ke office ɗin na shi bai hana shi ganin duhu ba.
Mi ya sa koyaushe mace ce ke sa shi cikin ƙunci, first it was his Mom then Sabreen sannan wannan Miss Salihun.
Ya dafe goshin sa da ke sara ma sa kaman zai tsage…

……….

Bai san lokacin da ya isa gida ba balle ya san lokacin da bacci ya ɗaukeshi. Buga ƙofan sa da ake da ƙarfi ya sa ya farka. Tasowa yai da ƙyar ya je ya buɗe ƙofan.
Anas ya gani yana faɗaɗa murmushin sa.

“Maigida har yanzu ba ka tashi ba, yau fa ranan ka ce”

Najeeb ya juya ba tareda ya ce komai ba ya wuce banɗaki.

Anas ƙaramin walk in closet da ke ɗakin ya shiga yana duba kayan Najeeb ɗin.

Najeeb ya shimfiɗa sallaya ya gabatar da sallar asuba lokacin agogo ƙarfe bakwai saura kwata.

Anas ya fito da wasu kaya ya shimfiɗa akan gado barin ga wanne zai fi fito da kai. Blue ko fari ko ash.

“And what are you doing exactly?”

” ina nema ma ka kayan da zai dace da kai a rana irin ta yau”

Wayar Najeeb ɗin ce ta fara ringing ya ɗauka da sauri ganin Daddy ne.

“I’m coming Dad”

Anas dai dariya ya fara ƙasa-ƙasa lokacin da Najeeb ya fita.

A ƙaramin falon Daddy da ke sama ya sameshi yana zaune yana waya.

“E ƙarfe shaɗaya ne, e masallacin wajen ne. Abin ne ya zo bagtatan ayi haƙuri” ya na gama wayar ya kalli Najeeb da ke zaune opposite da shi ya yi zuru-zuru da ido.

“Muhammad Najeeb” ya faɗa da sigar jan hankali.

“Ka kunna wuta a rayuwarka kuma ni nan na nemi hanyar kashe wutan. Idan ka amince ni Adam ni na haifeka kuma ka yadda ina da hakkin na samu biyayya daga gareka to yau ina umurtar ka da ka je ka shirya, ƙarfe shaɗaya za’a ɗaura auren ka da Aisha”

“What!”

“Ka jini da kyau kuma ba na buƙatar wani dogon bayani e ne ko a’a, idan ka ce e to ka yiwa kan ka adalci, idan kuma ka ce a’a to ka zaɓi samun wani uban daban kenan ba ni ba”

“Dad i’ll sort this out, zan je na gaya mu su gaskiya. You dont need to do this”

“NAJEEB!”

Shiru ya ratsa falon.

“Yes or no?”…

……………

Yana shiga ɗakin ya fara kaiwa Anas duka ta ko’ina.

“Dude ba fa ni na ma ta sharri ba fa da za ka sauke a kaina. Abinda ka shuka shi za ka girba”…

Duk da kasancewa abu ne da ya zo cikin ƙurarren lokaci hakan bai sa wannan aure ya tara jama’a ba. Daga ɓangaren Alhaji Jibo zuwa na Najeeb wanda Anas ne yai ta inviting mutane. Ma’aikatan Najeeb constructions da ma su son gulma da ma su zuwa dan Allah da ma su zuwa dan su yi tsegumi da zunɗen Ogan na su duk sun hallara.

Ranan ta asabat wanda ya kafa tarihi a ɓangaren gidajen biyu wato iyalen Alhaji Jibo da na Alhaji Musa Umar Wase.
Ƙarfe shaɗaya da ‘yan mintoti aka ɗaura auren Engineer kuma Architect Najeeb Adam Jibo, CEO Najeeb constructions ???? tareda amaryarsa Aisha Farida Salihu (ex- secretary @Najeeb constructions????)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button