SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Daddy ma ɗan darawa yai.

Najeeb kam haɗe rai yai yana yiwa Farida kallon za ki gamu da ni.

“Najeeb idan ba abinda za ka ce, za ku iya tafiya”

“Good night” ya faɗa ya tashi da sauri kaman wanda a ƙaya ya ke zaune da ɗin.

Farida ta bi bayan shi bayan ta yiwa Daddy sai da safe a nitse…

Tana shigowa ɗaki ta sameshi ya na kishingiɗe akan gado hannun sa ɗauke da waya ya na dannawa. Ƙarasawa ta yi ta cire dogon hijab da ta yi sallah da shi ta ninke ta kaishi saman bedside drawer.

“Ba a ajiye kaya anan”

“To hijabin sallah ne ai”

“Ba a ajiye kaya a nan Miss Salihu”

Dariya ta yi ta ce “yau na ji wani zance, Miss Salihu kuma? Jiya dai aka ce wai Najeeb Adam Jibo ya biya sadaki na naira dubu ɗari biyu, ko ba haka ba?. Gara ka san da me za ka kirani amma ba Miss Salihu ba”

Kallon ta ya ke yi itama ɗin ta zuba mi shi ido, doguwar rigan bacci ne a jikin ta wanda ya kai har ƙasa amma siririn hannu rigan ke da shi.

“Oh! so yanzu kin zama Mrs Jibo kenan? Congratulations”

“Ni kam Sir Najeeb mi ye acikin Aisha ko Farida da ba za ka iya kira na da shi ba?”

“Ki ɗauke kayan nan, ba a ajiye kaya a cikin ɗaki”

“To ka nuna min inda zan sa kaya na ne. Ina wancan wajen duk kayan ka ne a ciki, kaya sai ka ce wanda mutum ya buɗe boutique”

” This is my room Mrs Jibo, dole ki bi tsarin yadda ɗakin ya ke, ba na son datti, ba na son clumsiness. Kin ga yadda komai ya ke a tsare, haka na ke so komai ya kasance a inda ya ke. So ki ɗauke wancan tsummukoran a wajen nan”

“Hijabin nawa ne tsummokara, lallai”

Shiru ta yi tana kallon sa, ta ga ya maida hankalin sa kan waya.

Ƙaraman tsaki ta yi sannan ta ɗauki hijabin ta kai shi wajen closet ɗin.
Tana dawowa ta zauna bakin gado tana shirin kwanciya ya ce ” and what are you trying to do?”

“Bacci ma na”

“A ina ɗin?”

” ni fa Sir Najeeb ka ƙyale ni tam. Idan ba haka ba na gayawa Daddy, ka san ya ce har zane ka zai iya yi a kaina”

” there’s no way i’m sharing a bed with you ki na sakatariya ta. Ga chan sofa chan ki je ki kwanta akai”

“Da ka san ba za ka iya haɗa gado da ni ba miyasa ka aureni. Ni bance ka min komai ba dan na san abinda ka ke tsoro kenan” ta ƙarasa maganar tana kwanciya da kyau.
Ajiye wayar sa yai ya taso ya na ƙoƙarin ɗauketa daga kan gadon, ita kuma ta riƙe zanin gado tana ” Allah ba inda zan je, ba zan kwana a kujera ba sai dai kai ka kwana”

Wuff yai sama da ita ya zo ya sauketa a kan sofar. Yana ajiyeta ta sake tasowa ta zo za ta kwanta, yasake ɗaukan ta ya maida ita kan sofa.
“Mrs Jibo, idan ba wani abin ki ke nema a wajena ba, sleep here”

“Tabɗijam, wallahi ko a makaranta ban kwana a kujera ba balle a nan. Wallahi ka barni na kwanta ko na gayawa Daddy”

“Go on, je ki gaya ma sa” har ta fara tafiya sai kuma ta juyo ta ce “ƙila ya yi barci yanzu”

Miƙa ma ta wata na’ura yai ya ce ” za ki iya gaya ma sa ai ba sai kin fita ba, ga shi ki danna 2 ki yi ma sa magana zai ji ki a ɗakin sa”

Ita fa ta ɗauka wasa ya ke dan abin yai ma ta kama da wayar cellular ta ƙarɓa ta ce “ƙila ma ƙarya ne”

“Go on try it”

“Daddy ga Sir Najeeb ya hanani kwana a gado, ka zo ka ma sa magana” ta faɗa da ɗan ƙarfi.

Murmushi yai ya ce ” stupid girl”

Minti biyu kacal sai ga shi ana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin su.
“Najeeb be matured please, mi ye wannan shirmen”

Jin muryan Daddy ya sa Farida ta yi saurin kama baki tana dana sanin abinda ta ce.

“Sorry Dad, good night” Najeeb ya faɗa sannan ya kalli Farida da ke tsaye tana zare ido.

“On a second thought, za ki iya kwana akan gado but” ya nuna ta da yatsa “kar ki kuskura ki matso kusa da ni, i can bite”

“Ni ma kar ka kuskura ka matso kusa da ni, i can scratch”

Zuwa yai ya jera pillow biyu a tsakiyar gadon sannan ya kwanta.

“Wallahi wajen ka ya fi yawa, wannan ba tsakiya ba ne”

Sa hannu yai ya kashe wutan ɗakin. Dole ta laluba ta kwanta a haka.
Chan ƙasar ran ta tana tunanin anya akwai ranan da Najeeb zai iya jin son ta, ko da ɗan kaɗan ne? Anya za ta iya samun kan sa kamar yadda Ummi ta ce? Anya akwai ranan da za ta kwanta da shi ta yi rayuwar aure da shi?
Ta tuno abubuwan da ta yi ta sha da ci saboda samun amarci mai cike da tarihi tareda Rayyan, amma yanzu kam duk a banza. Tana cikin tunane-tunanen nan har bacci yai gaba da ita…

Ya na kwance ne amma ba wai ya yi baccin ba. He still wonders why everything turns out this way, jiya saboda bai san yadda zai haɗu da ita ba shiyasa ya kwana a office. Komai ya zamo ma sa wani iri, she’s just his secretary and that’s what she’ll always be ????
Bai taɓa hango rayuwar aure da wata ba idan ba Sabreen ba. Sun planning komai tare, tun daga irin gidan da za su zauna har zuwa ‘ya’yan da za su haifa. Yara biyu Sabreen ta ke so, kuma shi su ka tsara za su haifa ( ka ji fa????). Ba su tsara zama a Nigeria ba saboda Sabreen ba ta so, a plan ɗin su Nigeria sai dai ziyara amma ba zama ba. But yanzu komai ya chanza and now auren Aysherh…

………………….

Washe gari da asuba alarm ɗin Najeeb ya farkar da Farida, Ita kam ganin ƙarfe huɗu kuma akwai bacci a idon ta ya sa ta cigaba da bacci.

Ƙarfe biyar da rabi na ta alarm ɗin ya buga. Ta tashi ta hango Najeeb yana aiki a laptop ɗin sa. Cikin zuciyar ta ta ce “yanzu haka tun tashin sa bai yi sallah ba, shi komai aiki kaman machine”
Ta tashi ta shiga banɗaki fitsari ta yi sannan ta yi alwala ta fito.
Ta shimfiɗa sallaya ta tada sallah.
Da ta idar ta kalleshi har lokacin yana aiki.

“Sir Najeeb ina kwana”

“Morning” ya faɗa kaman ana roƙan sa amsan…

Tana azkar ɗin safiya ya tashi ya shiga banɗaki sai kuma ya fito ya ce “Mrs Jibo, next time ki ka yi amfani da toilet, you flush it immediately”

“Fitsari kawai fa na yi”

“Ba na son ƙazanta”

“Toh na ji, kuma ni ba ƙazama ba ce”

Ya jima a banɗakin har ta gama addu’o’inta ta koma gado ta kwanta bai fito.
Ya na fitowa ta bi shi da ido daga inda ta ke kwance, bathrobe ne ajinsa fari. Zuwa yai ya tsaya gaban mirror yana ƙoƙarin shafa mai. Duk abinda ya ke tana kallon sa har ya gama ya je ya shirya cikin wani grey suit na kamfanin Dolce and Gabbana. Dole ta rasa gane wani irin turare ya ke amfani da shi saboda turarukan da ya fesa sun fi biyar. Lokacin da ya gama ya taje gashin kan sa sannan ya matsa wanni mai a hannunsa ya shafa a gashin.

Ya sake shiga banɗakin kafin ya fito ya ce ” i know you are staring Mrs Jibo, idan kin tashi ki kira Adama za ta gyara ɗakin”

“Ni mi zan gani, ni ba kai na ke kallo ba”

“Mrs Jibo think about my offer” yana faɗin haka ya ɗau brief case na shi ya fita.
Agogo ta duba ta ga ƙarfe bakwai saura minti ishirin. Kai dole Sir Najeeb ya dinga zuwa da wuri, duk da kamfanin sa ne amma ba ya wasa da zuwa da wuri.

Bayan fitan sa sai da ta mori bacci sosai kafin ta tashi wajen ƙarfe goma ta fara gyara ɗakin…

………………..

“Dan Allah wa ya ke zuwa wajen aiki ranan ukun auren sa. Haba Najeeb ko a week break ba za ka ɗauka ba”

“A week break? Bayan asaran da Miss…” ” i mean Mrs Jibo ta jawo min”

Anas ya kwashe da dariya ” Mrs Jibo, haba nawan, ba wani sweet pet name da za ka sa ma ta sai Mrs Jibo”

“Mrs Jibo ma ai matsayi ta samu”

“Akwai lokacin da za ka kirata sweetheart, my love…”

“Oh please Anas”

“Allah Wallahi. Yanzu dai akwai wani Korede da zai fara aiki da kai yau, i hope you’ll like him”

“No need, Mrs Jibo za ta resuming monday”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button