SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

………………………..

A falon Najeeb su ke aikata abubuwa. Yammacin ranan litinin. Daga dawowar su daga office kenan ko abinci ba su ci ba. Bayan komai ya kankama su ka je su ka yi wanka.

Yunwa ta ke ji dan haka ta sauka ƙasa dan ta nemi abinda za su ci. Tasallah bata nan an musu rasuwa ta ɗau hutun kwana uku.

Tana kitchen ta ji ana danna doorbell. Ta ajiye frying pan da ta ke son ɗaurawa a gas ta fito. Shirt ɗin Najeeb ne a jikin ta, ga cikinta ɗan wata biyar da ya fito sosai. Leƙawa ta yi dan ta ga ko mace ce ta buɗe ba sai ta je ta nemi hijab ba. Ganin mace cikin liƙabi ya sa ta buɗe ƙofa.
Tana buɗe ƙofar ta amsa sallamar da matar ta ma ta.
Ɗaga liƙabin da matar ta yi ne ya sa Farida faɗin “Sabreen!”

Sabreen ta yi murmushi ta rungumeta…

A falo ta zauna tana jiran Faridan ta sauko. Bayan ta haura sama dan ta kira Najeeb.

Najeeb na aiki akan laptop Farida ta shigo ɗauke da murmushi.

“Ga amarya ta biyo angonta” ta faɗa da sigar tsokana.

“Hmm ki ce ango zai yi abubuwa kenan”

Farida ta ja hancin sa ta ce “Sabreen ce ta zo”

“Sabreen!” Ya faɗa da mamaki…

Sosai Sabreen ta bawa Farida tausayi. Cewa ta yi ta zo mu su bakwana ne dan ba lallai su sake ganin ta ba. Mahaifinta ya rasu wata biyu da su ka wuce. Ta ajiye aikin film gaba ɗaya, ta biya tara ta fanshi kan ta saboda ba ta gama aikin da ta signing za ta yi ba da wani production company.
Dukiyarta da dukiyar da ta samu na gadon Baban ta da shi ta ke son buɗe foundation dan ta dinga taimakawa marayu da mabuƙata da su.

“Sabreen aure fa” Farida ta tambaya da zuciya ɗaya.

“Ba wanda zai iya aurena Ayshah. Ni ma kuma na haƙura da aure. Allah bai yi zan yi aure a rayuwata ba. Zan cigaba da istigfari da neman ilimi har iya ƙarshen rayuwata”

Farida sai da ta yi hawaye itama ganin yadda Sabreen ke kuka cikin nadama. Yes duniya ta yi yayinta na ɗan wassu shekaru amma yanzu duniya ta juya ma ta baya. Wanda su ke tareda ita duk sun watse.

Tare su ka shiga kitchen su ka yi girki. Bayan sun ƙare cin abinci kafin Sabreen ta tafi akan ranan Monday za ta tafi.

………………………

Naomi gani ta ke yi abinda IfaGbemi ya gaya ma ta ba mai yiwuwa ba ne. Tun da ta ke ba ta taɓa ganin Najeeb yai fushi da Farida ba. They are inseparable. They are madly inlove.

Wannan weekend ɗin da ta wuce ta je jahar Ekiti chan cikin wani ƙauye tareda ƙawarta Maureen.
Ba komai ne ya kaita wajen ba sai saboda Najeeb ɗ. Tsawon watanni tana dakon soyayyarsa amma shi kam bai ma san tana yi ba. Har aranta ta ƙudura idan har Najeeb zai so ta to za ta bar kiristanci ta koma musulunci.

Maganganun Ifagbemi na ma ta yawo a ka lokacin da ta ke jujjuya kwallin da ya bata a hannunta.

“Mace ɗaya aka rubuta mi shi a gaba ɗaya rayuwar sa. Duk inda zai je ya dawo mace ɗayan nan ita ce ƙaddarar sa”

“Baba to ya zan yi kenan? Ba zai taɓa sona ba kenan?”

Bokan yai wata baƙar dariya ya ce ” idan ki na so ya so ki sai dai ya gan ki a matsayin matar da ya ke so. Idan ki ka yi kamaceceniya da ita zuciyar sa zai so ki”

Maureen da Naomi su ka haɗa baki wajen faɗin “ba mu gane ba”

Wata ƙwarya da aka lulluɓe da jan ƙyalle ya ɗauko sai da yai ta surkullen sa sannan ya buɗe ƙwaryar sai ga kwalli a ciki.
Ya ɗau kwallin da hannun hagu ya miƙawa Naomi ya ce ta amsa da hannun hagu.
Naomi ta amshi kwallin tana jujjuya shi.

“Duk ranan da yai fushi da matar sa, ki saka wannan kwallin a idon ki ki ƙyafta ma sa ido ki kwantar ma sa da hankali. Zai dinga kallon ki a matsayin matar sa, duk soyayyar da ya ke mata zai dawo kan ki Amma…”

“Naomi” muryan Farida ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.

“Yes ma” ta faɗa da muryan girmamawa.

Akwai Dr Lukman da zai zo wajena anjima ki barshi ya shigo.

Naomi ta gyaɗa kai…

Najeeb ya fita supervision. Ita kaɗai ke office. So ta ke ta surprising Najeeb amma bayan Lukman ya amince za ta sanar da shi komai.

Ba’a jima ba sai ga Lukman ya shigo.

“Hajiya Farida ya aiki”

“Lafiya Dr, ya hanya”

“Alhamdulillah”

“Ya haƙuri kuma na ji ance Alhaji Magaji ya rasu”

“Hakane kusan 5weeks ma yanzu”

Farida ta ce Allah jiƙan sa.

Shiru ya ɗan ratsa office ɗin. Kafin daga baya Farida ta ce ” Doctor har yanzu ka ƙi aure”

Lukman yai murmushi mai ɗaci ya ce ” har yanzu Allah bai nufa ba. Kowacce mace ba ta son auren ɗan shege”

“I’m sorry” Farida ta faɗa cike da tausayin shi.

“No dont be. Allah ba ya taɓa ɗaurawa bawa jarrabawar da ta fi ƙarfin sa”

Farida ta ce hakane.

“Amma ba ka sake nema ba ne ko ya?”

Lukman ya nisa ya fara ba ta labarin yadda yai sanadin musuluntar da wata colleage na shi Dr Jennifer, har sun tsara za su yi aure ta amince da shi duk da ya gaya ma ta matsayin shi. Ƙwatsam wani abokin aikin su wanda ya ke da mata biyu fa Dr Faisal ya shiga nemanta yai ta hure ma ta kunne da ma ta burga da asalin sa yana kushe Lukman a matsayin sa na shege. Ƙarshe dai Dr Faisal ta aura.

“Kai duniya, yanzu musulmi ɗan uwan musulmi amma sai ya ha’inci ɗan uwan sa. Shi da ke da mata biyu amma ba su ishe shi ba sai sun hanaka samun mata?”

Lukman yai dariya mai ciwo ya ce ” mi za ta yi da shege bayan ga cikakken namiji mai asali”

Jikin Farida yai sanyi. Yadda ta tsara anya zai yadda da shawaranta kuwa? Dama so ta ke ta ma sa maganar Sabreen. Sabreen tana buƙatar aure sannan tana buƙatar auren mai addini wanda zai kula da ita. To kuma Lukman shi ne candidate ɗin da ta ke ganin ya dace ya auri Sabreen dan ya ƙara gyara ma ta rayuwar ta…

Shigar Dr Lukman office ɗin Farida ya sa Naomi ta sa do not disturb tag a jikin ƙofa tana addu’ar Allah ya sa Najeeb ya dawo da wuri.

Tana zaune kuwa sai ga Najeeb, as usual ko kallon ta bai yi ba ya zo zai shige office sai ya ga tag ɗin da ta sa.
Ya juyo a fusace yana tambayar dalilin saka tag ɗin.

“Sorry Sir, Madam ce ta ce na sa dan ta yi baƙo. Tun tafiyar ka su ke tare”

Najeeb bai kawo komai a ransa ba ya buɗe office ya shiga. Ta glass ɗin da ya raba office ɗin sa dana Farida ya hango Farida da Lukman su na zaune. Zahiri ba wai su na wani abu ba ne. Magana ce su ke yi amma fiskan Farida ɗauke da murmushi.
Sheɗan ne ya tunzura shi a wannan lokaci. Har zai buɗe office ɗin ya shiga sai kuma ya juya ya fita, Kan sa ke wani irin ciwo. Idon sa ya yi ja zir.
Yana fitowa ransa a ɓace zai tafi Naomi ta kira shi.

“Sir”

Ya juyo a fusace ya kalleta. Naomi ta fara ƙyafƙyafta ido, ta taso ta zo gaban shi har lokacin bai iya janye idon sa daga na ta ba. “dear ka yi haƙuri. Ka kwantar da hankalin ka, ina tareda kai”…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣5️⃣1️⃣

Naomi ta sa hannu ta fara shafa ƙirjin Najeeb. Bai motsa ba bai kuma hana ta ba. Ganin bai yi masifa ba yasa wanni daɗi ya ziyarci zuciyar Naomi. Ta kwantar da kai jikinsa tana cigaba da shafa shi. Najeeb dai yana tsaye kaman gunki bai iya aiwatar da komai ba.

“Sweetheart ka yi haƙuri ka ji”
Najeeb ya tsinci kan sa da gyaɗa ma ta kai…

Farida ta ji farin ciki sosai da amincewar Lukman. Tanada yaƙinin Sabreen za ta amince da shi musamman idan Najeeb ne ya ma ta maganar.

“Barin kira mijina yanzu na san ya kusa dawowa”
Ta ɗau waya ta fara kiran numban Najeeb. Sau uku tana kira sau uku wayan na tsinkewa ba tareda an ɗauka ba.
Duk da gabanta ya faɗi da hakan amma ba ta nuna ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button