SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ƙarfe takwas saura su ka gabatar da sallan Isha tareda sallar godiya sannan Lukman ya gabatar ma ta da kazarta. Tare su ka ci kazar su ka ƙoshi sannan Lukman ya tattare wajen…

Kunyar Lukman ta ke ji, ta sani ita ba irin matar da ta dace da Lukman ba ne. Ya fi ta daraja da kima duk da kuwa ta fishi asali.

“Ka yi haƙuri ba nida abin da kowane ango ke farin cikin samu a rana irin ta yau. Na yi rayuwa marar daɗi a baya, na zubda mutuncina a idon duniya, na ɗauka rayuwa mai kyau na ke yi, rayuwa ta ‘yan ci da jin daɗi amma a gaskiya rayuwar ƙunci na yi a baya. Ka yi haƙuri dan Allah. Ina godiya da Allah ya bani kai. Ba ka dubi yawan shekaruna ba, ba ka dubi rayuwar bariki da na yi a baya ba amma ka amince da ni ka amince na zamo sashen rayuwar ka. Thank you Lukman”

“Shhhhhh” ya faɗi tareda haɗe bakin su…

Sabreen ta sha gyara sosai, duk da ta saba amma Lukman ya bata mamaki saboda yadda ya birkitata da salon sa, sai takejin ba ta taɓa tarayya da wani da yai kusan sa a iya sarrafa mace ba….

Skt 58

ina roƙon duk wanda ya karanta wannan shafin yai wa Mijin Maman Durratu addu’a, Allah ya jiƙan sa da rahama, ya haskaka ƙabarin sa, ya gafarta ma sa ya kuma bawa iyalen sa haƙuri da juriyan rashin sa, Amin. Wanda su ka rigamu gidan gaskiya Allah ya jiƙan su da rahama, muma idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani amin

Yau tun safe ta ke jin ta ba dai-dai ba. Ta dai daure ta cigaba da ayyukan da ta saba. Yana fitowa daga wanka ta riga ta cire ma sa kayan da zai sa. Ita ta shafa ma sa mai sannan ta taimaka ma sa ya shirya. Tana gyara mi shi tie ɗin ya ce “my Queen lafiya? You look dull this morning”

“Just ƙafafuwa na ke ciwo” ta faɗa dan kawai kar ta tada ma sa hankali

“Ko za mu je ki ga likita?”

“No, zai yi sauƙi zuwa anjima”
Ta ɗan bugi ƙirjin sa kaɗan ta ce ” mijina ka ga yadda ka yi kyau. Dan Allah ban da dogon hira da mata, banda lumshe mu su ido, ban da yi mu su murmushi, ka ji nawan”

Ya ɗan ja kumatunta ya ce “na ji your highness zan kiyaye duk abinda ki ka ce” light kiss ya manna ma ta a baki kafin ya ja hannunta su ka bar ɗakin…

Tafiyar Najeeb office da awa uku Farida ta fara naƙuda. Ɗanliti sabon dreban ta ya wuce da su asibiti. Tun a hanya Tasallah ta kira Mom ta gaya ma ta. Su na zuwa asibitin ko minti arba’in ba ta cika ba ta haihu.
Abin ya zo ma ta da sauƙi gaskiya, kuma Alhamdulillah ba wata matsala…

Tana kwance an kaita ɗakin hutu Mom na gefe tana kallon jaririn mai kama da uban sa. Cikin zuciyarta ta ke godiya wa Ubangiji da ya sa ta ga ɗan Najeeb.
Mom ta miƙawa Farida jaririn tana faɗin “he look just like his father”

Farida tana kallon jaririn tana godiya bisa wannan ni’ima da Allah ya ma ta…

Bayan minti talatin da haihuwar kafin Najeeb ya iso asibitin. He cant believe it sai da ya ga jaririn, Mom ce ta kirashi ta ma sa albishir da haihuwan. Bai kawo haihuwa ba tunda ya bar Farida lafiya gashi kuma EDD ɗin ta saura kwana shida. Sai dai al’amari na Allah yafi gaban kowa.

Ya ɗau yaron yana murmushi tareda kissing goshin yaron. Alhamdulillah ya ke ta maimaitawa a fili, bakin sa ya ƙi rufuwa saboda farin ciki.

Ƙarfe huɗu da rabi aka sallame su daga asibitin su ka dawo gida. Kafin dare gidan na su ya cika da Jama’a. Kowa na zuwa ganin babyn Farida.

…………………………..

Gidajen biyu sun kasance cikin farinciki bisa wannan ƙaruwa da aka samu. Da farko Mom ta so Farida ta dawo wajenta amma gogan sam bai ba da dama ba.

Mom za ta je gidan su tun safe sai dare ta tafi. Ita ke yiwa Farida wanka. Ummi ma kullum sai ta zo duba Farida da jikar ta.

Kafin ranan suna gidan an cika shi da tarkacen yara. Wassu abin ma jaririn kafin ya iya amfani da su sai ya shekara uku amma an siye su tun yanzu.

Ranan suna yaro ya ci sunan Muhammad Yaman
(Finally Farida an zama Umm Muhammad????)

Mutane ba kaɗan ba su ka halarci waliman wannan suna, tun daga mutanen Gombe zuwa na Wase da Jos kowa ya karkaɗe jiki ya zo. Sabreen da Lukman ma saura kwana ɗaya suna su ka dira a Kano. Yaro ya samu kyaututtuka ba adadi.
Sorveniers sa aka raba ba za su irgu ba. Saboda gudun evil eye, sunan yaro kawai aka sa babu hoto. Washe gari aka yi abincin sadaka aka kai Iskalin Almajirai sunfi ishirin…

Rayuwa ta cigaba da tafiya hakanan soyayyar Najeeb da Farida tana tafiya gwanin sha’awa. Baby Yaman ba ƙaramin gata ya ke gani a wajen iyayen sa ba, ga uwa uba kakannin sa. Kowa son ɗaukan sa ya ke idan aka fita da shi, amma miskilin yaro ba kowa ya ke yarda ya ɗauke shi ba. Ko Tasallah da ƙyar ya ɗan saba da ita ya dena kuka idan ta ɗauke shi…

Kamfanin Najeeb sai daɗa bunƙasa ta ke yi, yanata samun buɗi ta ko’ina…

Wannan zuwan Farida gida lokacin Yaman yana ɗan wata huɗu ta lura da cikin Ummi. Ko ya akayi ma ba ta lura da shi ba sai yanzu oho dan aƙalla cikin zai kai wata shida.

“Ummi dan Allah ki haifo mace na samu ƙanwa nima”

Ummi ta ma ta daƙuwa, Farida ta sa dariya, dan ta gane Ummi kunyar cikin ta ke ji…

………………..

Aneesa da Maijiddah sun saita kan su, sun dena kishin hauka. Aneesa ta yadda duk makaman yaƙinta, sosai ta ke kula da miji da yaranta tunda yanzu ba inda ta ke zuwa. Ciki ma ta ke da shi amma ta kasa sanar da Abdulwahab dan kar yai zaton ƙarya ta ma sa irin wancan karan.

Daren wata Monday AbdulWahab yana ɗakinta ya ke ma ta maganar wani abokinsa da ya buɗe sabon kamfani, yana yi ma sa tayi akan ya bar Aneesa ta jagoranci ɓangaren sales and marketing saboda experience da ta ke da shi.

“Mi ki ka gani?”

“Duk abinda ka ce Sweetheart” ta faɗa tana kai hannunsa daidai cikinta. Jin ɗan tauri-tauri da cikin yai ya sa shi duban Aneesan da kyau yana neman ƙarin bayani. Ta ɗaga ma sa yatsu huɗu tana murmushi.
“Da gaske?”

Ta gyaɗa ma sa kai. Ya jawota jikin sa sosai yana hamdala…

Bisa amincewar AbdulWahab ta fara aiki wanda 8am-2pm za ta dinga yi duk rintsi zuwa uku da rabi ta dawo gida randa ba ta samu traffic sosai ba ma kafin ƙarfe uku ta iso gida. Cikin be zo ma ta da wani laulayi ba shiyasa ta ke gudanar da lamuranta cikin sauƙi. Ita kuwa Maijiddah sosai Al’amin ɗinta yai wayo, kowa na son yaron a gidan ba ma kamar yayunsa Baby da Alizah, indai su na gida sun dinga faɗa akan sa kenan kowa na son ɗaukan sa…

Bayan wata biyar Aneesa ta haiho yarinyar ta mace. Yadda bata wahala a renon cikin ba sai ya zamana ta wahala wajen haihuwa, dan awa takwas ta yi tana labour ƙarshe sai da aka sa mata ruwan naƙuda kafin haihuwan ya taso gadan-gadan.

Itama wannan jaririyar a Kano aka yi sunanta, yarinyar ta ci suna Khadijah su ka sa ma ta inkiyar Mujahida…

……………………….

Ummi ma ta haihu namiji amma kwanan sa biyu yaron ya koma. Farida sai da ta yi kuka ranan tamkar ita ta yi haihuwan.
Baffa Musa ma ya ji mutuwar yaron dan yadda ya ke ji da Ummi to haka ya ke jin son abinda za ta haifo ma sa. Sai dai ƙaddara ce da ta riga fata…

Yau Jumma’a da wuri ya dawo daga office. Ɗakinsa ya fara shiga amma ba ta nan. Ya rage kayan jikin sa sannan ya wuce ɗakin ta. Abin mamaki sai ya ganta durƙushe bakin gado tana kuka. Da sauri ya ƙaraso wajenta dan tunanin sa wani abu ne ya samu Yaman.

“My Queen mi ya faru? Ina Yaman?”

Ɗaga hannu ta yi ta nuna wajen gadon yaron. Ya ƙarasa gadon da sauri, ya kalli Yaman na bacci hankalin sa kwance, sai a lokacin ya ji hankalin sa ya kwanta. Ya shafa kan yaron sannan ya koma wajen Farida da ke kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button