SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Adama waye?”

Kafin ta bada amsa Farida ta ce “Aisha Farida ce”

Sunan ba baƙon suna ba ne a wajen su duka biyun, dan sun san labarinta a Najeeb constructions. Ranan da su ka fara zuwa wajen Najeeb farko-farkon fara aikin Farida. Hana su shiga office ɗin sa ta yi ta sa su ka jira shi a office ɗin ta har sai da ya dawo. Ranan cikin shagwaɓa Najdah ta dinga complain wa Najeeb har da cewa “Big B, your secretary was rude to us”. Daga baya Najeeb ya ce wa Farida duk lokacin da ƙanwar sa ta zo yana nan ko baya nan ka da ta hana ta shiga office ɗin sa.

“Ehen, duk haɗuwar ku na office bai isa ba sai kin biyoshi gida” Afrah ta faɗa tana huhhura hanci.

“Idan aiki na ya tsone mi ki ido, kya iya zuwa ki ƙarɓa”

“Mtsww” Afrah ta ja tsaki

“Mi ki ka zo yi?” Najdah ta faɗa ita ɗin ma fiskan ba yabo ba fallasa.

“Na kawo wa Sir Najeeb wa su files ne, sannan na zo neman bayanai gameda masoyina Anas kasancewa kin fini sanin shi”

“Masoyin ki Anas?” Najdah ta maimaita

“Wanni Anas tukunna?” Afrah ta saka baki.

“Abokin yayanki ma na, ko kin san wani Anas ɗin bayan shi?”

Najdah ba ta ce komai ba sai haurawa da ta yi sama da gudu fuuuu itama Afran ta bi bayanta tana kiran ta.

Ganin su duka biyun sun bar wajen ya sa Adama ta je wajen SHS ɗin falon ta danna 6 muryarta na rawa ta ce “Ranka shi daɗe ga Sakatariyar ka ta zo neman ka”

Shiru kusan minti ɗaya ba a ce komai ba, har Adama ta fidda rai sai ga muryar sa ya na cewa ” send her to my room”

“Ina ne ɗakin?” Farida ta tambaya

“Idan kin haura sama shine ɗaki na ƙarshe a ɓangaren hagu”

Ok kawai ta ce ta haura saman. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta yi lokacin da ta iso. Ta tsaya na aƙalla minti biyu kafin aka buɗe ƙofar.

Sanye ya ke da jallabiya na ‘yan Morocco kalar toka.

“What do you want?” Ya faɗi fiskar sa tamau.

“Ya Allah, wai haka gidan ma su kuɗi su ke ne, daga ka zo sai a fara tambayarka mi ka zo yi. To ni ba maula na zo yi ba ziyara na kawo”

Ƙofar ya jawo zai rufe ta yi saurin sa hannu ta ce ” yi haƙuri Sir Najeeb saƙo na kawo”

Ya dakata da rufe ƙofar yana kallonta. Ta fito da wani file ta miƙa ma sa sannan ta ce ” Sir MD na Hafzal suites ya zo neman ka ya ce da ka ji saƙon nan ka kira shi akwai magana mai muhimmanci da za ku yi sannan dan Allah ka bawa Ya Anas haƙuri abinda ka…” baam ya rufe ƙofar sa.

” Mr Egocentric” ta faɗa kafin ta juya ta fita.

A falo ta haɗu da Daddy shi ma ya shigo gidan kenan, har ƙasa ta rusunna ta gaida shi.

“Kaman na san fiskar nan”

“Yallaɓai ai ni ce sakatariyar Sir Najeeb wanda aka sace mu kwanaki”

“Oh Aisha ko?”

“E”

“Sannu ya Baban na ki”

“Ya na lafiya”

“Ki gaida min shi ko”

“Insha Allah zai ji”

“Gida za ki je ne?”

Ta amsa da E

“To to, Adama ki fita ki ce Iliya ya kaita gida ko”

“Na gode Daddy”

Ya fito da kuɗi a Aljihu ba tareda ya irga ba ya miƙa ma ta ya ce ta sha ruwa a hanya.

“Daddy ka barshi na gode”

“Idan ki ka yi haka ba ki ɗauke ni Daddy ba kenan”

Ai tuni Farida ta karɓa tana ƙara faɗaɗa murmushinta lokacin da ta ji kaurin kuɗin zai iya kaiwa dubu goma.

Ita kam bajau ɗin ta, ta tafi gida a mota mai kyau ga AC ga dubu takwas da Daddy ya bata…

Ai ba ta gama zama ba Anas ya kira ta.

” ‘yar uwa mi ki ka faɗawa Najdah ne? Ta kira ni wai muna soyayya da ke kuma na ɓoye ma ta bla bla bla…”

Sai da Farida ta yi dariya mai isar ta sannan ta ce ” Yaya na kenan, idan akwai kishi to akwai so. Najdah na son ka, ka saurari plan ɗina ka ji…”

…………

Su na cin breakfast a dining Najdah ta ce ” Big B wai ashe Ya Anas da sakatariyar ka soyayya su ke”

Tea ɗin da Najeeb ya kai baki ya furzar da sauri.

“Anas ya gaya mi ki?”

“Jiya da sakatariyar ka ta zo ta ke gaya min. Big B, Ya Anas ya rasa wanda zai nema sai masifaffiyar yarinyar nan, that girl fa ba za ta rasa mu’amala da ƙwaya ba”

Miƙewa Najeeb yai bai ce komai ba ya bar dining ɗin.

Ranan da Anas da Farida ban san wanda ya fi shan masifar Najeeb ba. Abu kaɗan masifa, lokaci guda Najeeb ya dawo wa Farida Najeeb ɗin da ta sani farkon zuwan ta. ” get out, fuct you, stupid, nonsense” waɗannan kalmomi da su na tsiro da sun tsiro a jikin Farida saboda tsabar yadda ta ji su a wajen Najeeb. Idan ta kawo takarda ya signing kuwa yana gamawa zai wurgeta da shi ba zai miƙa ma ta da hannu kamar yadda ya saba ba.

Anas ma ya ɗauka da Najeeb ya zo zai ba shi haƙuri a wuce wajen sai ya ga saɓanin haka. Yana tambayar sa abu maimakon yai magana sai ya fara ma sa tsawa…

Farida na tattara wasu takardu da Najeeb ya watsar Anas ya shigo office ɗin.

“Najeeb ka dubi wannan presentation ɗin nan na gobe. Wannan shi ne final edit da na yi”

Ko kallon laptop ɗin da Anas ya ajiye a gaban sa bai yi ba ya ce ” kar ka damu kan ka, ba za ka yi presenting gobe ba”

“What”

“Ka jini da kyau”

“Najeeb are you serious? I’ve been planning for this pitch for a week now”

Da ƙarfi Najeeb ya daki table ɗin sa ya ce ” Ni Najeeb Adam Jibo, CEO of Najeeb constructions na ce Architect Anas Ali AlMustafah ba za ka yi presentation gobe ba, ka na da ja?”

Da Anas mai saurin kuka ne da ya yi a wajen nan saboda wannan cin fuska da Najeeb ya ma sa. Sai dai ya daure ya ce ” ba ni da ja, Sir Najeeb”

Wannan karo na farko da ya referring Najeeb da ‘Sir’ kenan, a cikin shekaru bakwai da su ka fara aiki tare.

Gwiwar Farida yai sanyi. Tausayin Anas ya mamaye zuciyar ta. Da ta na da iko da ta je ta wankawa Najeeb mari.

Wai a wani dalilin zai yiwa Anas haka, a wani dalilin?
(Ni dai da ‘yan group ɗi na ma su albarka mu ka haɗa baki mu ka ce a dalilin ki)

plz numbar da za a nemi yadda za’a shiga paid group ɗin sakatariya ta ita ce 08137311900, duk wani number da ba wannan ba scam ne. Kar ku manta, #200 ne kacal ko kuma ka biya #300 ka samu sakatariya ta da tsohuwar soyayya. Za ka iya biya ta wannan account ɗin 3099546325, firstbank,Azizat Hamza. Ko kuma ka turo katin waya zuwa ga wannan layin 08137311900. (Plz duk wani means of payment da ba wannan ba, babu hannun marubuciyar a ciki. Mutanen Niger za ku iya biya ta link da zan turo da yamma Insha Allah a wattpad account ɗi na 000Azee)

…………

“Yakubu dan Allah ka nemo min super glue mai kamawa sosai wanda baya saurin bushewa”

“Yanzu dan Allah mi za ki yi da super glue? Ke ba mai gyaran takalmi ko radio ba”

“Ni bana son sa’ido, ka nemo min kawai. Harda gum na ruwa ɗin nan. Yau na ke so ba gobe ba”

“Ke wallahi case ce, na ji zan nemo”

Farida ta yi murmushi

Da wurwuri ta zo office yau. Tana daƙontar zuwan Najeeb dama ta gayawa security da zaran Najeeb ya ya shigo ya kirata.
Tana zaune kuwa security ya kira ya ce ga Najeeb ya shigo. Ta yi sauri ta shiga office ɗin sa ta samu kujeran sa ta fara matsa super glue ɗin da Yakubu ya kawo ma ta.
Za ta fito kenan ta yi kiciɓis da Najeeb zai shigo dama tuni ta sa tubes ɗin a jakarta.
“Good morning Sir”
Bai amsa ma ta ba ya wuce wajen zaman sa.

“Sir Ya Anas ya kawo flash ɗin da za ka yi amfani wajen presentation ɗin na ajiye a table ɗin ka” wannan magana shi ya ɗaukewa Najeeb hankali ya zauna ba tareda ya lura da kujerar sa ba.
Tana gani ya zauna ta yi murmushi.

“Ki tabbatar duk wanda ke cikin team ya isa conference room kafin ƙarfe tara”

“Ok Sir” ta fita tana murmushi.

Flash ɗin ya ɗauka ya sa a laptop na shi yana duba presentation ɗin da Anas ya sha wahala ya tsara.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button