SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Sleep Mrs Jibo” …

……………….

Kamar yadda Sabreen ta nema haka washe gari aka ware ma ta office a second floor. Da ta zo ta gani ta ce ba ta so sai a top floor inda office ɗin Najeeb ya ke. Anas ya ce sai dai ta yi manage ahaka zuwa kwana biyu. Ba ta da haƙurin kwana biyu dan haka ta ce ba za ta zauna ba.

Kamar yadda Anas yaiwa Farida alkawari hakan ya sa ya kira Yakubu su ka fara reviewing ɗin case ɗin Farida da aka yi kwanan baya.

Najeeb ya jima yana zaune yana aiki, Sabreen ta sa shi a gaba da kallo. Ya ce ta tafi ta ƙi tafiya sai yai kamar bai san da zaman ta ba a wajen.
Farida ba ta office lokacin da Sabreen ta zo ta wuce. Ta dawo daga kai saƙo ta zauna tana yin aiki sai ta tuna ya kamata ta chanja pad. Ta ɗau jakar ta ta nufi office ɗin Sir Najeeb tunda banɗakin sa ya fi clean.

Yana zaune ya ji hannun Sabreen a kafaɗar sa. Ya juyo a fusace.
“Whats the meaning of this?”

“I know you missed my touch Noory” ta faɗa tana ƙara shigewa jikin sa.

“To karuwancin har a office” muryan Farida ta dakatar da ita.

Dukkan su su ka kalli Farida da ke tsaye ta sa hannu a kafaɗa.

“Miss celebrity you’re stepping beyond your boundary” ta ƙaraso har gaban ta ta nuna ta da yatsa.
Kamar yadda ta ce mata she has his heart haka itama ta kwaikwayi maganan ta ta ce ” fuck off old woman, i am his wife”

Sabreen ta cize leɓe tana huci.

“As as as, mai guri ta zo sai mai tabarma ta naɗe”

“Wow! I like your courage” ta faɗa tana haɗiye duk wani baƙin ciki da ta ke ji.
Har ta fita Farida ba ta bar cewa as as as ba.

Ta juyo ta kalli Najeeb da ya zuba ma ta ido yana ganin shaƙiyancin da ta ke wa Sabreen. Not minding ko waye Sabreen ɗin.

“An dai ji kunya, mace ta gudu ta barka shekara takwas amma ka gan ta yanzu jikin ka ya fara rawa kamar mazari” ta yi wani juyi sannan ta wuce banɗaki.

………………..

A hankali ta fara barbaɗa tankaɗaɗɗen yajin da ke hannunta, tun daga pillow zuwa duka bedsheet ɗin. Bedsheet ɗin ba fari bane balle a gane. Tana gamawa ta fice daga ɗakin ta maida roban yajin zuwa kitchen. Ta haura sama abinta.
Sabreen ta dawo tayi wanka ta shirya cikin rigan baccinta ɗan filili da shi. Ta kwanta akan gado. Juyawar da za tayi sai ta ji zafi a wuyanta da cinyoyinta da ke buɗe. Ta sa hannu ta sosa wuyar ai sai ya zama kamar ƙara zafi ta yi wa wajen. Ta yi wuf ta tashi tana sosa ko’ina ajikinta…

Farida ta baza kunne tana sauraron ko saƙonta ya kai inda ya ta ke so, saboda haka ma ba ta kunna Tv ba, Shi kuma Najeeb na aiki a laptop. Lokaci ɗaya su ka ji an kurma ihu.
Da farko Najeeb ya ɗauka ko ƙaran daga TV ɗin Najdah ne tunda ya ga Farida ba ta kunna Tv ɗin su ba. Ihu da ƙaran ya cigaba da ƙaruwa hakan ya sa ya miƙe zumɓur ya fita, Farida ta bi bayan shi da sauri.
Lokacin da su ka isa ƙasa su Daddy da Mom ma sun iso ƙasan su na kan Sabreen da ke ta soshe-soshe tana ihu…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣2️⃣9️⃣

wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900

Sabreen na ganin Najeeb, ta yi kan sa tana sose-sose, ya riƙeta yana tambayar miya ke damunta amma ba magana sai kuka tana ƙara shigewa jikin Najeeb kaman jikin sa ne zai ma ta magani.
Mom ta tafi da gudu ɗauko car key. Chak ya ɗauketa za su fita dai-dai nan Farida ta sa kuka itama tana wayyo cikina wayyo cikina.
Najeeb ɗauke da Sabreen ya juyo ya ga Farida har ta kai ƙasa tana riƙe da ciki.

Dad ya ce ajiyeta ka ɗauko matar ka.
Sabreen ba ta ji mi aka ce ba amma ganin Najeeb na shirin sauketa sai ta sake ƙanƙame wuyan Najeeb tana kuka.
Chan gefe ma Faridan kuka ta ke yi Mom ta yi kan ta tana ƙoƙarin ɗagata tana tambayar miya sameta.
Tunanin Najeeb ko dai ciwon cikin period ne amma kuma she was normal throughout yau, tunda yau kwana na uku kenan da farawanta.

Farida cikin kuka ta fara cewa “Mom ulcer, ulcer na ne ya tashi”

Bai san ko maganar Daddyn ne ta shige shi ba, ko kuma dai ya zaɓi tallafawa Farida ne akan Sabreen ɗin. Amma tsintar kan sa yai da sauke Sabreen ya nufi wajen da Farida ke murƙususun ƙarya a ƙasa. Daddy da Mom su ka tallafawa Sabreen su ka fita da ita. Daddy na cewa yai sauri ya ɗauko Farida. Faridan na hannun sa ya ce su tafi da Sabreen zai taho da Farida.
Ba tareda ya ji nauyin ta ba haka ya haura da ita sama dan ya ɗauko key ɗin motar sa, har da ce ma ta sorry.
Ya ɗauki key ɗin su ka fito still yana ɗauke da ita. Kafin su isa wajen motar sa motar su Daddy ta fice daga gidan. Sai da ya ajiyeta sannan ya zago da gudu ya shiga wajen zaman driver, yana ƙoƙarin tada motar ya ji ta ce “Sir Najeeb mu koma cikin gida, idan na sha Gestid ma zai lafa mun”

Kallon ta ya tsaya yi cike da mamaki da takaici, sai yanzu ya lura fiskarta ba ɗigon hawaye ko ɗaya. Lokaci guda zuciyar sa ta ankara da cewa lallai Farida na da hannu wajen abinda ya samu Sabreen, yanzu haka wani abin ta sa ma ta a ɗaki.

“You lied?” Ya faɗa da ɗan ƙarfi

“Sir Najeeb Allah Wallahi ina da ulcer, na ji alamun zai tashi ne shi ne ya sa na tareshi tun kafin ya zo”

Zaro ido yai waje lokaci guda kuma ya kwashe da dariya har da dukan steering.

“Now i’m very certain that you’re crazy Mrs Jibo”

“Sir Najeeb da laifi idan mutum ya tari rashin lafiya ne?”

Sai da ya sha dariyar sa sannan ya ce ” faɗamin gaskiya mi ki ka yiwa Sabreen?”

“Ni ba abin da na ma ta. Ance idan duka yai yawa na kai ake karewa. Da ka je kana dakon ɗaukar wata ƙatuwar banza ba gara ka ɗauke ni ba, har lada za ka samu a hakan fa”

“So, kin ƙirƙiri ciwo ne kawai dan na ɗauke ki?”

“Allankatafir ba haka ba ne. Ciwon a jikina ya ke tun asali”

” Ok ok, so yanzu mi za ki ce da su Dad? Su ma za ki gaya mu su taro ciwo ki ka yi?”

“Cewa zan yi na sha magani na warke”

“Ni kuma sai na kai ki asibitin, a taro miki ciwon da kyau”

Ganin yana ƙoƙarin ta da motar ne ya sa ta yi saurin buɗe ƙofa ta fita da gudu. Yana gani ta fita ya kwantar da kan sa ajikin kujera yana murmushi. Shi kan sa mamaki ya ke, a da ya tsani yawan surutun ta amma yanzu ya na jin nishaɗi idan tana yin wasu abubuwan.

Ya jima a cikin motar yana tuno wassu abubuwa da su ka faru a baya. Yana fitowa zai koma cikin gida Daddy ya kirashi yana tambayar ya aka yi ba su iso ba. Cewa yai cikin Faridan ya lafa ta ce ba sai anje asibiti ba.
Daddy ya ce “to Alhamdulillah, Allah ya ƙara lafiya”

Yana kashe wayar ya fara mamakin ƙaryar da yai saboda Farida.
Duƙunƙunewa ta yi ajikin bargo tana tsoron mi Sir Najeeb zai yi dan ta tabbata ya gane ita ta yiwa Sabreen wannan abu.
Yana shigowa ta sake duƙunƙunewa ta na rintse ido.

“Ki gayamin gaskiya mi ki ka sa ma ta?”

Ta yi shiru ba ta kulashi ba.
“Idan ba ki gayamin ba zan gayawa Dad ƙaryan da ki ka yi”

Ta ɗan buɗe idon ta ta leƙo shi yana tsaye yana kallon ta.

“Borkono ne, dakakken borkono na sa ma ta a bedsheet”

“You’re a criminal Mrs Jibo, ya kamata a kama ki”

“Allah ya kiyaye”

Wucewa yai ya shiga banɗaki dan ya sake wanka…
Farida na ganin ya shiga banɗaki ta san ba fitowa zai yi da wuri ba ta yi wuff ta tashi ta fita daga ɗakin. Ɗakin Sabreen da ke ƙasa ta je ta cire bedsheet ta karkaɗe sannan ta juyashi baya ta shimfiɗa, filon ma ta ma sa haka sannan ta fito.

(yau na ci yaji dayawa, hakan ya tada min ulcer na. That’s d trigger for writing this scene????. Ni ma daga yau irin na Farida zan na yi, zan dinga taro ulcer tun kafin ya tashi, saboda idan ya zo kar ya wahalar da ni????)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button