SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“What!”….

????SAKATARIYA TA????
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Free page

0️⃣0️⃣9️⃣

“Wayyo Allah Ummi na. Wayyo Ummi naaaaa” abinda ta farka da shi kenan lokacin da ɗaya daga cikin mutanen da su ka sato su ya watsa musu ruwa.

“Shut up” ya daka ma ta tsawa. Nan kuma ta fashe da kuka tana cewa ” dan Allah kar ku kashe ni, ni ɗaya ce a wajen Mahaifina kuma ko jika ban haifa ma sa ba”

Tare aka ɗauresu da Najeeb bayansu na gogan na juna sai dai tun da ya farfaɗo baice ƙala ba.

“Sir Najeeb ka ce su bar ni na tafi. Iyayena talakawa ne, ba su da kuɗin da za su basu, yanzu ma Baffa na cikin bashi yake saboda hidimar biki da yai…” saukar mari taji a fiskarta wanda ba shiri ta fashe da wani matsananci kuka.

“Chachachacha, you talk too much abeg”

Buɗe ƙofar ɗakin aka yi Joseph da sauran su ka shigo.

“Well well well. The Almighty Sir Najeeb, the perfect man. Mr get out of my office” ya sa hannu ya murɗe kunnen Najeeb da ƙarfi.

“I will make sure you suffer before this is over”

“Untie him” ya faɗi yana yiwa Najeeb kallon tsana.

Kunce shi su ka yi ya ce su ma sa tsirara ai Farida na jin haka ta fara bada haƙuri.

Ɗaya daga cikin su wanda ya ke kamar shine Oga ya zuƙa wiwi da ya ke sha ya ce ma sa ɗan uwa ba haka akeyi ba, idan kana so su biya kuɗi to dole ‘yan uwan sa su tabbatar yana cikin ƙoshin lafiya.
“Emeka why now?” Joseph ya faɗi cike da takaici

“Bros let me handle it” wanda aka kira da Emeka ya faɗi. Zuwa yai ya cirewa Najeeb takalmansa da agogo yace ” so na designer you wear” naushin cikin Najeeb yai wanda sai da Najeeb ya wantsila.
Shi kuwa Joseph zuwa yai ya taka kafar Najeeb. Ba ƙaramin zafi ya ji ba amma haka ya shanye bai nuna ba.
Lokacin da za su tafi Joseph ya tofa wa Najeeb miyau a fiska. Har su ka fita daga ɗakin bai buɗe ido ba saboda tsananin ƙyanƙyamin abinda Joseph ya ma sa.
Ɗankwalin atamfar ta ta ɗan yaga ta zo ta goge ma sa miyau ɗin.
“Wai mi ka yiwa wannan guntun ne? Joseph ko me su ke kiran sa”

Bai buɗe ido ba kuma bai yi magana ba.

“Dalla buɗe idon. Ba na riga na goge miyau ɗin ba”

A hankali ya buɗe rinannun idanunsa ya ɗaura akan na ta. Itama ɗin shi ta ke kallo for some weird reasons sai ta ji ya ba ta tausayi. Wannan fa ɗan gata ne gaba da baya, CEO na babban kamfani amma Joseph ya ma sa wannan walaƙanci.

“Wannan bayan kuɗi da su ke so akwai bita da ƙulli tsakanin ku. Allah ya sa dai kar su kashe mu”

Ta kalli ƙafar da Joseph ya taka yatsun wajen sun yi jaa sun kumbura. Ta kai hannu za ta taɓa ya janye ƙafarsa da sauri.
” kaa! Dan ma zan taimaka ɗin, to ka ci kan ka”
Ta koma chan gefe ta zauna. Yanzu da aka kuncesu ta ɗan ji saƙayau.

“Ni wallahi yunwa na ke ji, ba dan kai ba da yanzu ina gida ina cin abinci. Ni daga mun kai gida lafiya ma ajiye ma ka aiki zan yi. Irin wannan aiki da kasada ba dani ba”

Tana cikin surutu aka buɗe ƙofa, abinci aka kawo mu su, take away guda biyu na shinkafa da satchet water guda biyu. Ko kallon inda abincin ya ke Najeeb bai yi ba. Farida kam jawo abincin ta yi ta fara ci dan Allah na gani ba ta iya juran yunwa. Abincin ba wani yawane da shi ba hakanan nan taste ɗin dai ba laifi da alama daga restaurant su ka ƙarɓo.

“Sir Najeeb ka ci abinci fa, da zafin sa kar yai sanyi”

Tashi yai ya ɗau ruwa ya shiga wani ƙofa da ke cikin ɗakin wanda ya ke tunanin banɗaki ne. Banɗakin ne sai dai gaba ɗaya a ƙazance ya ke da ƙyar ya kama ruwa yai alwala ya fito dan ba ruwa a wajen, famfom baya aiki.

Sai da ta ga ya je gefe ya tada sallah itama ta ankara ba ta yi sallar maghrib da Isha ba, gashi ta shanye ruwanta.
Dole sai taimama ta yi bayan ta leƙa banɗakin ta ga ba ruwa.

Tana zaune ta jingina da bango ta fara gyangyaɗi ƙarshe baccin wahala ya saceta….

……………………..

Kafin ƙarfe goma na dare iyalen Alhaji Adam Jibo sun samu mummunan labarin rashin Najeeb da Sakatariyar sa. Abinda ya ɗaure mu su kai har lokacin ba a kira su gameda ransom ba. Bacci kam ƙauracewa iyalen yai bama kamar baby da ta dinga kuka wiwi da ƙyar Mom ta shawo kan ta ta yi shiru.

Gidan Baffa Musa ma dai hankulansu a tashe ya ke. Ba ma kamar Baffa Musa wanda ya ke gani kamar sakacin sa ne ya sa Farida ta faɗa wannan hali. Yadda Baffa ya hana a sanar da Ummi amma hakan bai yiwuba dan kafin yai maganar ma tuni Anty Hanne ta kirata ta sanar ma ta an sace Farida. Hankalin mutanen Jos ya tashi a wannan dare, a daren Ummi ta so ta zo amma Baba da Nanna su ka hanata, su ka ce ba abinda za ta yiwa Farida sai addu’a ta bari idan gari ya washe sai ta je.

Haka aka wayi gari gidajen biyu ba kwanciyar hankali. Ƙarfe tara na safe aka kira Alhaji Adam Jibo bayan an tura ma sa hoton Najeeb da Farida ɗaure. Miliyan hamsin su ke buƙata cikin awa ashirin da huɗu ko kuma su rasa su gaba ɗaya.

Anas ya sanar da Yakubu cewa kidnappers ɗin sun nemi ransom na 50million. Ya kuma kwantar ma su da hankali akan za a kuɓutar da su.

Baffa Musa da Yakubu su ka nufi gidan su Najeeb. Sun samu su Alhaji Adam su na meeting da wasu special police kan al’amarin sai da su ka gama sannan Dad ya saurare su.

“Alhaji dama maganan kuɗin nan ne. Ni dai a wajena idan na shiga na fita za a samu miliyan uku sai dai kaga ko rabin abinda su ke buƙata ba a kai ba”

“Alhaji Musa ka kwantar da hankalinka Insha Allahu komai zai zo da sauƙi. Maganar kuɗi kuma Alhamdulillah an fara arranging na su. Kar ka damu”

…………………..

Da safe Emeka ya shigo ɗakin ya fara faɗa harda marin Najeeb wai ‘yan uwansa ba sa son shi suna buƙatar 48hrs su haɗa 50million.

“I thought your parents are super rich. They better not play games with me”…

Emeka cousin ɗin Joseph ne, ya jima yana fashi da makami kafin daga baya ya koma harkan kidnapping. A Kaduna ya ke operation ɗinsa sai dai wata ɗaya da ya wuce Joseph ya kira shi akan yanaso ya kidnapping Najeeb saboda ya ɗau fansar abinda ya ma sa. Wannan ya sa ya zo Kano su ka fara tsare-tsaren yadda komai zai tafi. Da ke Joseph yai aiki a Najeeb constructions hakan ya bashi daman sanin hanyoyin da za su aiwatar da ƙudirin su.

Da safe ba a basu abinci ba haka da rana, gaba ɗaya Farida ta galabaita. Tana chan ta cure gefe guda ta yi kukan ta yi surutun har ta gaji. Najeeb kam ko ehem bai ce ma ta ba.

Buɗe ƙofar ɗakin aka yi, ɗaya daga cikin ma su tsaresu ya shigo ɗauke da bindiga. Zuwa yai ya jawo Farida da ƙarfi, Najeeb ya tashi zai yi kan sa. Ya nuna ma sa bindiga tareda cewa “sit”

Farida ganin anyi hanyar waje da ita ta fara cewa Najeeb ya taimaketa.

“Dont hurt her” Najeeb ya faɗi da kakkausar murya

Wani ɗakin ya shiga da Farida bayan ya kulle Najeeb a ɗakin da su ke da farko.

Ganin ya yo kanta ya sa ta ƙwalla ƙara tana kiran Sir Najeeb da Umminta.
Guje-guje su ka fara yi a ɗakin wanda ya ke cike da tarkacen kayan maye. Cak ta tsaya lokacin da ƙafarta ya taka wata fashashshiyar kwalba. Hakan ya bawa mutumin damar kamata ya kwantar da ita da ƙarfi, sai ihu ta ke ta na ƙoƙarin tureshi amma ta kasa. Ya kama hannayenta da hannunsa ɗaya, ɗaya hannun kuma yana ƙoƙarin zuge zip ɗin wandonsa.
Wani razannannen ƙara ta ƙwala wanda gaba ɗaya gidan sai da ya ɗauka.

Emeka da wasu biyu su ka yo ɗakin da su ka ji ƙaran da gudu. Ganin Larry na shirin afkawa Farida ya sa Emeka ya ture Larry tareda kwaɗa ma sa mari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button