SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Ai ranan na sha kwarwa. Allah, Ya Anas na ɗauka mari na zai yi yadda ya dinga banbamin nan”

“Sai ki kiyaye”…

Yana fita ta cigaba da aiki, tana so ta ƙare ta tafi gida da wuri dan kar ta yi staining dan ba ta zo da pad ba, ta ajiye a bakin gado za ta sa a jaka ta manta shi a wajen.

Minti ishirin ta haɗa komai sannan ta turawa Najeeb lokacin meeting ɗin sa ta email. Tana kan tattare kayanta Halima ta shigo.

Halima Baballe tana aiki a hawa na ɗaya ne a HR department. Halima irin matan nan ne ma su gutsuri tsomi, ‘yan haɗa waje. Bazawara ce aurenta biyu tana fitowa. Tun farkon zuwan Farida ta ke ƙoƙarin manne ma ta sai dai Faridan ba ta bata dama ba. Yawanci su ka haɗu a masallaci haka za ka ga tana liƙewa Farida tana kawo gulma da zunɗen mutane duk dan ta samu fada a wajen Farida tunda Farida sakatariyar Sir Najeeb ce, kuma kusan kowa a kamfanin yana son samun kusanci da Sir Najeeb.

“Anty nah Anty nah, ba dai kin tashi ba” ta faɗi tana washe baki

“Zan tafi gida, Sir Najeeb ba zai dawo ba kuma na gama aiki na”

“Sai na ga kin min wani lakwas, lafiya kuwa?”

“Halima yau ba na jin magana. Mi ya kawo ki?”

” Anty na kenan, baƙon wata ya zo kenan”

Farida ta yi tsaki ta saƙale jakarta a kafaɗa ta ce ” mi ya kawo ki?”

“Anty na, za a yi bikin ‘yar yata nan da sati biyu kuma wallahi adashen da na ke jefawa akwai mutum uku a gabana kafin na amsa shine na zo ko za ki ara min kuɗi?”

Kallon sama da ƙasa Farida ta ma ta sannan ta ce ” kar ki kawo min rainin hankali nan wajen. Yaushe mu ka haɗa hanya da ke da har zan ba ki aron kuɗi na?”

Halima ta yi dariya tareda ɗan dafa kafaɗar Farida ta ce “ƙawata kenan…”

“Cire hannun ki a jikina tukunna” Farida ta katse ta

” duk yadda na ɗauke ki da zuciya ɗaya amma ke har yau ba ki ɗauke ni haka ba. Ita Sister Munibat ɗin da ki ke maƙalewa an gaya mi ki son ki ta ke? Kwanaki fa har cewa ta yi ke ‘yar ƙwaya ce”

“Dalla gafara daga nan. Ba na son munafurci, halin ki na haɗa guri ya sa ba na son mu’amala da ke, idan da ba ki sani ba ki sani”

Halima ta ɗan haɗa rai ta ce ” na rantse da Allah Munibat ta ce wai ke ‘yar ƙwaya ce”

Farida ba ta ce komai ba ta ce biyo ni.
Tiryan-Tiryan su ka wuce office ɗin Sister Munibat inda ta ke ta faman aikin zane.

“A’a Sister Aisha ke ce tafe, ban ganki a masallaci ba ko lafiya?”

Farida ta kalli Sister Munibat sannan ta kalli Halima ta ce ” maimaita abin da ki ka faɗa a office ɗina”

Halima ta ji ras dan ba ta ɗauka abinda Farida za ta ce ba kenan. Ta ɗauka su na zuwa za ta fara yiwa Sister Munibat masifa.
Sai dai kamar yadda ta ke pro a wannan ɓangare sai ta dake, ta kalli Sister Munibat ta ce ” cewa na yi Sister Munibat ta ce ke ‘yar ƙwaya ce”

“Astagfurullah” Sister Munibat ta faɗi da sauri tana yin wiki-wiki da ido tana ƙara cigaba da istigfari a zuciyarta.

Farida ta ce ” to kin ji mi tace?”

Kafin sister Munibat ta yi wani magana Halima ta amsa da cewa ” za ki ce ba ki faɗi haka ba, ranan a masallaci. Idan kin manta ni ban manta ba”
Ta ƙarasa maganar tana matsowa kusa da ita kamar za ta maketa.
Jikin sister Munibat ya fara ɓari musamman da ta tuno abinda ya faru.

“Kin gani ai ta ka sa magana saboda ta san gaskiya ne, munafuka, kina jikinta kina zaginta”

Farida ta kalli sister Munibat ta ce ” ki faɗa min gaskiya. Kin faɗi haka ko baki faɗi haka ba?”

Sister Munibat ta buɗe baki za ta yi magana sai hawaye.

“Shikenan! Kukan munafurci. Dama yare, yare ai sai a hankali, dukkan su munafukai ne”

“Yi min shiru” Farida ta daka ma ta tsawa. Ta kalli sister Munibat ta ce ” kin bani mamaki. Ina ɗaukan ki da daraja ina mugun mutuntaki. I consider you an older sister”

Ta juya ta fita saboda ba ta da ƙarfin yin masifa.

…….

Ƙarfe bakwai na yamma sai ga sister Munibat a gidan su Farida. Duk hayaniyar da ake na lissafe-lissafe a tsakar gidan, Farida ba ta ciki. Ƙarshen sati aka ce za a kawo lefen Maijiddah.
Tana chan kwance ta gama murƙususu akan gado saboda ciwon ciki. Maijiddah na gefe tana yiwa wata ƙaramar ƙanwarsu kitso.

“Anty Farida ga ƙawarki ta zo” Sadiq ya faɗa lokacin da ya faɗo ɗakin da gudu

Da ƙyar Farida ta ɗaga kai lokacin da sister Munibat ɗin ta shigo ɗakin su.

Sai da su ka gaisa da Maijiddah sannan ta zauna a gefen gado ta fiddo da ƙur’ani izub sittin ta ce ” Sister Aisha na riga na yi alwala kafin na taho. Zan rantse mi ki akan abinda ya faru ranan da sister Halima ta ke faɗi”

Farida ta ɗan tashi jingine ta ce ” bai kai har ga haka ba ‘yar uwa. Ke dai ki gyara halin ki, zato zunubi ne ko da da gaskiya a cikinta. Sannan ki sani saka dogon hijabi ba shine ke nuna taƙawa ba”

“Na rantse da Allah sister Aisha ba abinda na faɗa ba kenan. Ranan da ba ki zo ba farko-farkon fara aikin ki, inaga lokacin bikin gidan kun nan ne. Ana taɗi shine aka kawo maganarki, cikin maida zance sai na ce ‘ sister Aisha kam wani lokaci idan ta yi wani abu kamar ‘yar ƙwaya’. Na rantse da Rabbil Arshi iya abin da na ce kenan”

Ta ja numfashi ta ce “dan Allah ki yafe ni sister Aisha”

“Ba komai, ya wuce. Sai ki kiyaye gaba, ki dinga taka tsantsan da mutane, dan abu ɗaya za ka ce ace ka faɗi goma. Ita kuma Halima Baballe gobe sai na ci ubanta tunda haɗi ta ke son yi tsakanin mu”

“Kin yafe min?” Ta tambaya kamar za ta yi kuka

“Wallahi na yafe mi ki, nima ki yafe ni” Farida ta faɗa tana ƙara kwanciya akan gado…

……………………….

Washe gari ko office ba ta shiga ba ta biya office ɗin su Halima ta je ta ma ta wankin babban bargo, a yadda ta tsara ma ko rabi ba ta ma ta ba saboda har lokacin ba ta warke be. Sai da ta gama silleta sannan ta wuce office ɗin ta. Tana zuwa ta samu Sir Najeeb ya zo sai dai ko da ta shiga bai ma ta magana ba kan latti da ta yi ba. Ta lura tun jiya da ya zo ya ke wani shiru-shiru kamar akwai abinda ke damun sa. Sai dai ta ja bakinta dan kar ya sauke matsalar sa akan ta.

Yau Jumu’ah kuma yau ne za a kawo lefen Maijiddah da yamma. Da ke ranan Jumu’ah ana tashi ƙarfe uku ne maimakon huɗu da aka saba shiyasa ta ke ganin za ayi komai da ita.
Da murnan ta ta shigo kamfanin, yanzu kam ba kasafai su ke zuwa tareda Yakubu ba.

Tun daga shigowarta ake ma ta wani kallo ana ƙus-ƙus sai dai ba abinda ya dameta tunda ba akan kowa ta ke ba. Lifter ta shiga ya kaita hawa na uku.

Abin mamaki sai ta ga Anas da Yakubu suna magana a office ɗin ta, ga Khalidah a gefe tana yamutse-yamutsen fiska.

“Sannun ku dai. Lafiya na ga wajen ya ɗau hayaƙi, Ya Anas me ke faruwa?”

Kallon tsana ya ma ta ya ce ” na ɗauke ki a matsayin ƙanwata ashe kallon da ki ke min kenan?. Farida ashe za ki iya jefanmu da wannan mummunan ƙazafi. A dalilin me?
You know what? kafin ma Najeeb ya koreki ni na koreki, ba ma buƙatar mai hali irin na ki a wannan kamfani” ya shige office ɗin Sir Najeeb cikin fushi.

Mamaki, fargaba da tsoro ya cikata. Cikin rashin fahimtar kalaman Anas ta ce ” Yakubu mi ya faru? Mi na yi?”…..

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Free page

0️⃣1️⃣2️⃣

“Asirin ki ya tonu, Munafuka ‘yar matsiyata. Yau dai dole ki bar aiki anan tunda an koreki” Khalidah ta faɗa tana murmushi.

“Yakubu mi ya ke faruwa ne, mi na yi da har Ya Anas ke faɗin maganganu marasa daɗin ji haka?”

Anas ya miƙa ma ta wayar sa ya ce “ki kunna ki saurara”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button