SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Farida ta ce “ka ce ta shigo”…

Najeeb ba ya gari ya tafi Lagos wani taro.

Fauziyya ta gaida Farida a ladafce kafin ta ce ” Ma ya jiki?”

“Da sauƙi” Farida ta faɗa fiskarta a sake dan yanzu ta yi wa kan ta faɗa. Dama cikin Zafreen ne ya sake tunzura ta.

Fauziyya ta fito da IV daga jakarta ta miƙawa Farida. Farida ta amshi IV ɗin tana karantawa. Ta ɗago ido da sauri ganin sunan da ke jiki.

Fauziyya ta yi murmushi ta ce ” Ma, you have every reason to be jealous, ko ni na ke auren Sir Najeeb ba ƙaramin kishin sa zan yi ba. He’s handsome, rich and successful. Amma ki sani ban taɓa son mijin ki ba, tun kafin na fara aiki anan an riga an ba da ni, lokaci kawai mu ke jira and now the wedding is in 12 days”

Cike da kunya Farida ta ce ” ba dai za ki bar aiki da mu ba”

“No, i love my job, kuma dear ya amince na yi aiki anan matuƙar za a maida lokacin tashi na ƙarfe ɗaya ko biyu”

“Kar ki damu za a rage miki. Wannan kamfani yana buƙatar ma su ƙwazo irin ki”

Fauziyya ta miƙe tana faɗin ” na gode Ma”

Farida ta ce ” dan Allah ki yi haƙuri abinda ya faru baya”

Fauziyya ta ce ba komai ya wuce…

……………………..

Tun da su ka dawo daga sunan Zafreen ta ke jin jikin ta ba daɗi. Ba ta son gayawa Lukman saboda kar hankalin sa ya tashi. Ciwon kai idan ta ce tana ji ranan za ka ga Lukman ya rikice yana ƙoƙarin ba ta kulawa na musamman. Yana son ta sosai yana kula da ita, she’s really lucky da ta aure shi. Ya iya soyayya ga iya kula da mace, ba shi da zafi kwata-kwata. Cikin zaman auren su za ta iya irga lokutan da ta ga ransa a ɓace hakanan ana ɗaukan wassu awowi za ka ga ya sauko ya koma normal. Itama ɗin ba ƙaramin tattalin sa ta ke ba, cikin ‘yan kwanakin nan ma tunanin samun haihuwa ta ke dan ta san shine kaɗai abinda za ta yi ta sa Lukman farin ciki, ga shi har yanzu shiru. Wani lokaci sai ta ga ko dan shekarun ta ne, amma kuma ai mata na haihuwa har a fifties na su balle ita da ke talatin da biyar.

Ta tuno da lokacin da ake tsakiyar shooting wani film hajijiya ya kwashe ta ta faɗi, da aka kaita asibiti aka ce tana da ciki. Baƙin cikin da ta ji a lokacin ba zai misaltu ba. Bayan kwana uku ta sayi wassu pills ta sha ranan ta yi bleeding kamar jinin ta zai ƙare. Ƙarshe sai da ta yi jinyar sati biyu a asibiti Ta rintse ido tana hawaye….

Lukman na fitowa daga asibiti ya haɗu Da Dr Jennifer wanda ta koma Dr Aisha. Ta jima da barin aiki da asibitin da ya ke, few months bayan ta yi aure.

Gaisawa su ka yi sama-sama har zai tafi ta tsayar da shi akan tana son magana da shi.

“Faɗi maganar ki da sauri dan my wife na chan gida tana jira na”

Jikinta yai sanyi da jin kalaman sa amma ta daure ta shiga koro ma sa bayanin yadda mijin ta Dr Faisal ya walaƙantata ya hana ta aiki ga shi ba ya wani kula da ita, ga matan sa da su ka sa ta a gaba akan ita yare ce kuma kafira wacce ta gama yawon titi. Walaƙanci dai iri-iri, yanzu gashi ko wata shida ba ta cika da haihuwa ba ya saketa.

“Sorry ko, ya sunan babyn?” Lukman ya faɗa cikin halin ko in kula.

“Fatima amma ta rasu few days bayan sunan ta”

Lukman ya ce ” Allah ya sa me ceto ce amin. Barin je gida kar wife ɗina ta jini shiru”

Ya wuce ya bar Dr Aisha cike da tarin nadama, yau da Dr Lukman ta aura ta tabbata ba zai taɓa walaƙantata haka ba, he’ll love her and cherish her for the rest of his life, sai ga shi ta ƙi auren ɗan shege ta auri ɗan asali kuma tana nadama…

Lukman na zuwa gida ya samu Sabreen na kela amai a banɗaki. He’s being suspecting pregnancy ‘yan kwana biyun nan amma saboda rashin samun isashshen lokaci ya sa bai damu ya tsaya ya tabbatar da zargin sa ba. Bayan ya taimaka ma ta ta gyara jikin ta sannan ya fara duba ta. Daga idanun ta zuwa tafin hannunta kafin ya ɗaga rigarta yana sa hannu a mararta da cikin ta.

“What is it?” Sabreen ta tambaya ganin taɓe-taɓen yai yawa.

With excitement a fiskar sa ya ce ” Lets confirm first”

Sai da ya tabbatar ta samu ƙwarin jiki kafin ya fita ya je ya siyo PT strip. Da ya dawo su ka gwada.

Ɗaukan ta yai sama yana juyi da ita yana dariya bayan ya ga reading ɗin strip ɗin ya bada positive…

……….

Kwanci tashi cikin Sabreen ya cika wata tara inda ta sha wahala wajen naƙuda ƙarshe aka ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba aka cire ma ta kyakykyawar jaririyar ta. Yarinyar sak ubanta hatta green eyes ɗin sa sai da ta ɗauka, idan ka ɗebe farin Sabreen da ta ɗauko ba abin da ta bari na Lukman.

Murna wajen Lukman ba a magana. Finally shi ma ya samu ‘ya, ‘ya ta sunnah.

Kwana biyu kafin suna Najeeb da Farida su ka dira a Abuja, tareda yaran su Yaman da Zafreen wanda ƙiriniyar yarinyar yafi ƙarfinta. Yayinda Yaman ya ke so quite ita wannan tun aciki ta ke sa uwarta masifa da ta fito ma tun tana ‘yar jinjira ta ke nuna iya shegen ta balle yanzu da ta fara wayo. Idan mutum ya ɗauketa ba ta so har cizo tana yi.

Ranan suna gaskiya anyiwa Sabreen da Lukman kara domin kuwa an zo dayawa, ‘yan uwan Lukman ta ɓangaren mahaifiyar sa duk sun zo, ga ‘yan uwan su Najeeb da su ma su ka cika wajen.

Tsakanin ma’auratan su ka yanke shawaran sunan da za a sawa yarinyar. Farida kam ba ƙaramin mamaki ta yi ba da Najeeb ya kira ta daga masallaci yana faɗin sai ta kawo kuɗin suna domin an samu little Aisha Farida

Bayan sun gama waya ta je ta ɗauki ‘yar tana ma ta addu’a. Sabreen da ke kwance sai murmushi ta ke yi…

……………………..

Rayuwa na cigaba da tafiya shekaru sun fara ja domin kuwa an samu haɓaka na arziƙi da iyali.
Najdah da Anas sun sake haifan mace inda su ka sawa ‘yar su sunan Aisha Amira aka yiwa marigayiya Aisha takwara.

Farida ta sake haihuwan namiji bayan Zafreen ta cika shekara biyu su ka yiwa Daddy takwara *Adam * suna kiran sa da Aasim

Sabreen ma ta sake haihuwa bayan Little Farida, shima ɗin CS aka ma ta dan ance da wuya ta iya haihuwa da kan ta. Sun samu Muhammad Mubarak

Baffa Musa da iyalen sa na zaune lafiya kowacce ƙoƙarin faranta ran ɗan tsoho ta ke. Amma alamu sun nuna Amina ta ci galabar sace zuciyar wannan tsoho, ilimi da wayewa sun sa duk abubuwanta sun banbanta da na sauran matan. Ba ta ganin tsufan sa kwata-kwata, duk ranan girkin ta haka ta ke birkitashi da salon ta na matan zamani wanda ya ke sa ya ji ina matan sa su ka shiga lokacin da sauran mata ke koyan dabarun sarrafa miji. Abubuwan da ya ke yi yanzu da wanda Ummi ke ma sa ko lokacin yana matashi bai samu wannan gatan ba.

Yakubu ma shekara ɗaya bayan haihuwar Zafreen ya angonce da amaryar sa Halima.

A ɓangaren Aneesa da Majiddah ma sun haɗe kan su suna zaune lafiya. Duk da Aneesa na zuwa aiki hakan bai hanata samun lokacin miji da ‘ya’yanta ba. Bayan Mujahida haihuwa ta tsaya ma ta amma Maijiddah ta samu Yusuf bayan Al’amin ga kuma tsohon ciki da ta ke da shi yanzu. Shi kam AbdulWahab sai dai yai ta hamdala kawai domin kuwa kwanciyar hankali da nitsuwa sun samu gindin zama a gidan shi…

…………

Zama aure sai haƙuri, akwai soyayya, akwai faɗa, akwai matsaloli amma idan kuka san yadda za ku dinga tafiyar da lamuran ku sai ya zamana duk inda matsala ta kunno kai za ku samu mafita cikin ƙanƙanin lokaci.

Najeeb da Farida su na nan su na soyayyar su, su na abubuwan su ma su sanya farin ciki da jin daɗi. Idan ana aiki a office jiki ya buƙaci abubuwa, sai a kashe wuta a rufe ƙofa a cigaba da abubuwa kawai ????
It wasnt a perfect life, they werent perfect. Su na faɗa suna samun saɓani kuma suna soyayya. Ba abinda su ka maida hankali akai kamar tarbiyyan yaran su da kuma tsare gidan su da yawan addu’o’i da yawan sadaka da kuma taimakon mabuƙata. Shiyasa lokacin da Sabreen ta buɗe Foundation ɗin ta, duk wata su na zuba maƙudan kuɗi a ciki saboda a samu a tallafi mabuƙata…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button