SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Mrs Comfort ta mutu kafin Naomi ta samu lafiya, ta samu lafiyan ne bayan Boka Ifagbemi ya mutu. Chan wani ƙauye a Owerri Naomi ta tsinci kanta lokacin da hankalinta ya dawo jikinta. Mutanen ƙauyen su ka ce ai tafi shekara biyu tana hauka. Su su ka haɗa ma ta kuɗi su ka bata kaya ta shiga mota sai Kano. Da ƙyar ta samu ƙaninta Abel saboda ya riga ya tashi a gidan su na da. Bayan ta samu masauki a gidan Pastor kafin aka sanar da ita mutuwar mahaifiyarta ta yi kuka kuma ta yi baƙin ciki sosai. Daga ƙarshe dai da ita da Pastor su ka je gidan su Najeeb inda ta ba wa Najeeb da Farida haƙuri. Sun riga sun yafe ma ta tuntuni, haka ta tafi tana kuka. Neman Maureen ƙawarta ta shiga yi inda ta gano ta bi wani chief ne hotel aka neme ta aka rasa har yau. Zance dai da ya fi tabbata shi ne an tsafe Maureen ne. Naomi ta yiwa kan ta karatun ta nitsu ta koma zama a gidan Pastor tana yiwa church ɗin su hidima alƙawari ma ta yi za ta zama Nun saboda ma kar ta yi aure. Pastor dai ya ba ta shawaran ta ƙara tunani a kai….

Rayyan kam ya rasa Farida har abada. Matar sa Aisha tana ƙoƙarin kyautata ma sa, sai dai har yau akwai ƙaramin gurbin Aisha Farida a zuciyar sa. Suna zaune da matar sa da ‘ya’yan su uku Kamal, Abdullahi da Zainab

………. ………. ……..

Gaba ɗayan su su ke airport ɗin. Ƙarshen shekara ne inda iyalen uku su ka shirya zuwa Maldives da kuma London dan yin hutun ƙarshen shekara.
Lukman da Sabreen suna tare da Little Farida ‘yar shekara uku sai Mubarak ɗan shekara ɗaya.
Najdah da Anas ma na tareda Najeeb Bobo da kuma Amira ‘yar shekara biyu.

Sai zugan FARNAJ
Yaman ɗan shekara biyar
Zafreen huɗu
Aasim biyu da kuma babyn da ke cikin Farida ɗan wata biyar…

…………..

…Maldives 2017…

Wajen beach ɗin ya cika da mutane kala-kala. Kowa ka gani yana sha’aninsa ne a wajen.

Wani mutum ne ya hango Zafreen da Little Farida su na wasa a wajen yashi yaran sun burgeshi. Shima tareda ɗan sa Nasir su ka zo beach ɗin tunda mai ɗakin sa shekararta ɗaya kenan da rasuwa.

Jin suna ingautsan Hausa Larabci da turanci ya sa su ka ƙara burgeshi. Ya ƙarasa wajen su riƙe da hannun ɗan na sa ɗan shekara bakwai.

“Hey pretty” ya faɗa yana kallon Little.

“Ya sunan ki” little ta kalleshi daga sama har ƙasa kafin ta ce ” Aisha Farida Lukman Magaji”

“Wow what a cute name”

Kafin ya tambayi Zafreen ta yi caraf ta ce ” my name is more cute than hers”

Ya ce ” Oh really and whats your name?”

“Nabeelah Zafreen Najeeb Adam Jibo, see i have the most cutest name in the world and i’m also a princess” ta faɗa tana cuno baki

Yai ƙaramar dariya ya ce “where are your parents?”

Dukkan su biyu su ka ma sa nuni da inda iyayen na su su ke.

Mutumin yai murmushi tareda nufo su Najeeb saboda kodan yaran da su ka burgeshi yana son ƙulla ƙawance da iyayen su tunda shima ɗan Nigeria ne…

Bilal yana magana da su Najeeb inda ya introducing kan sa a matsayin Engineer Bilal Bello Bukar sai ga Bobo ya zo da gudu yana kuka.

Wajen Anas ya nufa yana kuka sosai. Sai ga sauran yaran suma sun iso wajen da gudu.
Anas ya tambayi ɗan na sa ko mi ya faru sai Bobo ya nuna Zafreen.

Farida ta kalli Zafreen wanda ta yi tsaye ƙyam da ita ba ko tsoro a idon ta.

Farida ta ce ” mi ki ka ma sa?”

Zafreen ta sa hannu a ƙugunta tana faɗin ” ce min yai ‘yar lukuta, and mommy i’m not fat”

Farida ta harareta ta ce ” bakin ki ne i’m not fat ai, zo nan na cire bakin rashin kunyar na ki”

Najeeb ya ce “princess zo nan” Zafreen ta je wajen Najeeb da gudu tana dariya.
Little Farida ne ta faɗi abinda Zafreen ta yiwa Bobo. Marin sa ta yi sannan ta watsa ma sa yashi a fiska.

Kowa ya juyo yana kallon Zafreen wanda ko’ina ta je sai ta nuna halinta na rigima, ƙiriniya da masifa.

Farida ta ce “wannan ‘ya wannan ‘ya”

Najeeb ya harareta ya ce ” Thank God princess gado ta yi”

Gaba ɗaya wajen aka sa dariya. Farida kuma ta haɗe rai, ƙarshe ita ɗin ma ta joining na su aka cigaba da dariyan ana yi ana tuna baya..

Anan jirgin sakatariya ta ya sauka

Alhamdulillah

The end

Anan na kawo ƙarshen labarin Romantic Comedy mai taken SAKATARIYA TA, da fatan kun ji daɗin karanta shi. Kura-kuren da na yi Allah ya gafarta min. Duk da ya kasance RomCom hakan bai hana shi zuwa da darussa na rayuwa ba. Rayuwar gaba ɗaya cike ta ke da ƙalu bale. Labarin Najeeb da Farida was not perfect and soyayyar su ma ba perfect ba ce, dukkan su suna da flaws na su. Amma su kan yi ƙoƙari wajen saita tsakanin su cikin ƙanƙanin lokaci. Yayinda Najeeb ke da sanyi ita Farida ‘yar zafi-zafi ce

  • labarin sakatariya ta labari ne akan yadda wata sakatariya ta sace zuciyar Ogan ta. Note that, in reality mafi yawanci secretaries mata za ka ga suna ƙoƙarin shiga rayuwar Ogan su, idan Ogan bai kai zuciya nesa ba su zo su fara yin abubuwa tsakanin su and mafiyawanci za ka ga Ogan magidanci ne. Akwai wassu secretaries kuma wanda su ke munafukai ma su haɗa guri, akwai wanda su ne ke hana ruwa gudu a kamfani ko wajen aiki. Akwai wanda kafin ka ga Oga ko file ɗin ka ya je wajen Oga to sai ka bada cin hanci. Ga su nan dai birjik. Da sakatare namiji da sakatariya mace akwai na banza akwai kuma na ƙwarai. Whether namiji ne ko mace mu ji tsoron Allah a duk inda mu ke aiki sai ka ga an samu cigaba mai amfani*

ban yarda wani ko wata ya sayar min da labarin nan ba, ko kuma a karanta shi a youtube channels. Ko a yaɗa shi ta ko wanni fanni. Akwai wanda sun fara haɗa documents na labarin nan, su ma su sani ba da yarda na bane. Akwai wanda su ka yi ta sharing labarin nan bayan sun san na kuɗi ne. Har wassu idan an mu su magana su ke maida martani da furuci mai muni. Gaskiya ba ku kyauta ba.

Alhamdulillah na samu alkhairi dayawa dalilin rubuta labarin nan, wanda su ka biya jazakumullahu khairan, wanda bayan sun biya sun haɗa da wani ihsanin kuma ina godiya Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa.

zan cigaba da labarin Tsohuwar soyayya daga gobe Insha Allah. Wanda ba su samu daman biyan sa ba, akwai free story da zan yi immediately bayan Tsohuwar soyayya za su iya jiran wannan idan har Allah ya sa muna cikin ma su rai da lafiya

Suna na Azizat Hamza ina yiwa dukkan masoyana fatan alkhairi. Ma’assalam

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102

Leave a Reply

Back to top button