SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Ko kai fa mutumina” Anas ya faɗi tareda tashi tsaye. Har ya fara tafiya ya juyo ya ce ” Dan Allah, ya ka ji da ta hanaka shiga office ɗin ka?”
Najeeb ya jefe shi da biro, Anas ya goce yana dariya…
Yana fita ya samu Farida tana zaune hankalinta kwance kamar ba laifin da ta yi.
” ƙanwata na roƙa miki shi, dan haka ba wata matsala amma ki bishi a hankali”
“Na gode Ya Anas”…
Ta so jin maganarsu, amma bangon office ɗin sa soundproof ne ba abinda ta ji shiyasa ta haƙura da laɓen da ta yi ta je ta zauna…
Fitan Anas ke da wuya telephone ɗin office ɗinta ya fara ƙara. Ta san shine, dan ta nan Anas ya ce za ta fi comminicating da Ogan ta.
Ba tareda wani tsoro ko fargaba ba ta amsa kiran.
“In my office now” abinda ta ji ya faɗa kenan da kakkausan murya……….
????SAKATARIYA TA????
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Free page
0️⃣0️⃣6️⃣
Ta fi Minti biyar a tsaye bai ce ma ta komai ba, aiki ya ke yi ma a system na shi.
“Sir kai ka kirani kuma ka shanya ni kamar kayan wanki, idan ba abinda zan yi zan koma dan bana iya juran tsayuwa”
Ɗago ido yai yana kallonta. Lallai ma yarinyar nan, shi a tunaninsa da ta shigo office ɗin sa za ta bashi haƙuri sai ta yi ƙum da bakinta ko gaishe shi ba tayiba.
“Let me make this clear to you…”
“Sir Najeeb ka yi Hausa kawai zan fi ganewa, turancinkan nan ban faye ganeta ba. Lanƙwashe harshe ka ke kamar bature”
Bai ji mamakin maganarta ba duba da yadda ya san halinta.
” i will say this only once Miss Salihu. I do not tolerate laziness. This is an office, you should learn to behave yourself according to this company’s rules. Is that clear?”
Kallon sa kawai ta ke yi ba ko kiftawa
“Miss Salihu is that clear!” Ya daka ma ta tsawa.
“Yes…yes Sir”
“Good, now get out of my office”…
Tafi minti goma ta rasa yadda za ta arranging files ɗin da ya bata, kamar da gayya aka hargitsa files su ka zama haka. Tana cikin yi kira ya shigo, ta yi tsaki kafin ta ɗauka.
“In my office now”
Doguwar tsaki ta ja sannan ta tashi ta wuce office ɗin sa.
Ce ma ta yai yana da meeting ƙarfe shabiyu. Baƙin ciki ya zo ma ta har wuya. Maimakon ya gaya ma ta da ya kira sai da ya bari ta sha wahala ta zo har office ɗin sa.
“Why are you still standing, get out?”
“Sir, na san kai Oga na ne kuma zan ba ka girman ka amma kuma wallahi ba zan ɗau walaƙanci ba. Sir daga zuwa na na yi jelen tsakanin office ɗinka ya fi sau goma. Haba dan Allah, indai saƙon magana ne idan ka kirani sai ka gaya min ba wai sai na zo har nan ba. Wannan ai salon mutum ya samu ciwon baya ne”
Ganin ya miƙe ya sa tai shiru. Har gabanta ya tako ya tsaya. ” Miss Salihu, i know you are a lousy crazy girl but that should stop outside this company. Here, you are just a secretary, so work like one” yana gama faɗin haka ya fice daga office ɗin ya bar Farida baki buɗe.
“Allah ya isa na, mugu kawai. Daga ranan farko a addabi mutum da aiki kaman Jaki” ta yi tsaki sannan ta fice daga office ɗin…
………………………
Ƙarfe sha biyu saura minti biyu ya fito daga office biye da shi kuma sakatariyar sa Farida, tana ɗauke da wasu files a hannunta. Lifter su ka shiga saboda a second floor za a yi meeting ɗin. Ƙanshinsa ne duk ya bi ya cikata, ta rasa wannan ƙanshin na shi, its so inviting, so cool.
Kiiiinnnnn. lifter ta tsaya su ka fito yana gaba tana bin bayan sa har su ka shiga hall ɗin.
Kowa ya hallara a wajen dama shi ake jira. Dokar Najeeb ne lateness is a punishable offence.
Ta samu kujera kusa da mace ɗaya da ke wajen ta zauna bayan ta ajiye files a gaban Najeeb.
Duk yawancin bayanan su ba ganewa ta ke yi ba, ko dan maganar ta fi karkata zuwa ga ayyukan gine-gine da kamfanin ke yi ne…
Ƙarfe ɗaya saura minti biyar aka rufe meeting,su ka fito.
Yanzu ma bayanshi ta bi su ka haura. Sai dai ta yi laushi sosai tana ajiye files akan table ta kwantar da kanta.
Rufe ƙofar da yai ya sa ta ɗago idon ta. Ya cire suit ɗin sa, farar shirt ɗin ne kawai ajikinsa yana warware hannun rigar da alama dai alwala yai. Su na haɗa ido ya ƙara haɗa rai…
Sai da ya tafi ta fara ƙoƙarin neman banɗaki dan ta yi tsarki ta yi alwala. Office ɗin ta dai babu, ƙoƙarin fita ta ke matar ɗazu ta shigo office ɗinta.
“Assalamu Alaikum sister”
“Wa’alaikissalam, ‘yar uwa sannu da zuwa”
“Suna na Munibat AbdulHamid, i’m an Engineer. Office ɗina na second floor”
“Masha Allahu. Suna na Aisha Farida, sabuwar sakatariyar Sir Najeeb”
“Na ce dama ko zamu sauka mu je sallah. Akwai masallaci a ƙasa”
“Wallahi na gode, kamar kin san abinda ke raina kenan , dama banɗaki na ke nema”…
Fita su ka yi Sister Munibat ta nuna ma ta inda banɗakin mata ya ke, sannan su ka sauko su ka wuce masallaci. Anan Farida ta ga wa su ma’aikata matan duk wanda tacewa ita sakatariyar Sir Najeeb ce sai su ce “Hmmm, Allah ya sa ki iya dan Sir Najeeb Sai a hankali”
Ita kam ba ta ce komai ba dan tun kafin su faɗi haka ta ji a wajen Yakubu da Anas.
Daga masallaci canteen ɗin kamfanin su ka wuce, su na shiga Farida ta hango Yakubu da wasu su na cin abinci dan haka ta yi saurin ƙarasawa wajen table ɗin su.
“Yaya Yakubu ka siya min abinci yunwa na ke ji”
Yakubu ya harareta ya ce ” idan ba ki da kuɗin siya ki je ki karɓi ruwa, ruwa is free for all the workers here”
“Haba dan Allah, na ce ma Yayan ma ba za siya mun ba”
“Yayan ai ba na Allah Annabi bane. Na cin hanci ne”
Engr Mathew da ke gefe ya ce ” sister ki zauna za’a siya miki abinci. You are our beautiful sister ai”
Farida ta je ta jawo kujera ta zauna. Yakubu ya ce “Matt, wannan yarinyar ci ta ke kamar gara ga ta da shegen son bati. Idan za ka bi shawarata ka barta ta siya da kanta idan ba haka ba kullum kai za ta maƙalewa”
“No problem, this beauty deserve to be serve like a Queen”
Farida ta yiwa Yakubu gwalo…
Su na cin abinci Najeeb da Anas su ka shigo, nan wajen yai tsit. Kai tsaye wani gefe su ka je su ka zauna inda wajene da aka tanada ɗan gefe da sauran mutane. Kujerun wajen da table ɗin ya fi sauran ƙayatuwa. Wajen cin abincin Sir Najeeb kenan, da ke Anas shi ne na hannun daman sa sai ya zamana tare su ke zama su ci a wajen.
Jin wajen yai shiru ba kamar yadda ta fara shigowa ba ya sa Farida cewa ” ni kam mutuwa ce ta wuce ne? Na ga kowa yai shiru sai ƙaran sokala da fork kawai”
Yakubu ya taƙaleta ya mata nuni da ido. Sir Najeeb da Anas ta hango su na cin abinci.
Ta gane saboda Sir Najeeb ne kowa ya nitsu a wajen. Sakamakon da da ake cin abincin ana hira yanzu kam kowa abincin ya ke ci baki gum.
“Ya Anas…Ya Anas” muryarta ya karaɗe wajen.
Anas da ya ke kurɓan juice ya ajiye glass ɗin ya juyo da sauri. “A’a ‘yar uwa ke ce, ya aiki”
“Lafiya yayana. Yaya wai ni an saka dokan hana magana ne anan? na ga anyi shiru”
Anas ya ce ” ni ma ban sani ba amma ki tambayi Ogan ki”
Farida ta maida kallonta wajen Najeeb da ya cika ya kumbura kamar zai fashe. Ta ce ” Sir Najeeb ka hana magana a nan ne??” Tambayar ta fi kama da gatse ko shaƙiyanci kuma da gangan ta yi hakan. Tashi Najeeb yai ya bar wajen. Yana fita daga canteen ɗin aka sa ihu. Wasu sai a lokacin su ka san miye aikin Farida, ta burge kowa, sai dai dayawa sun ji tausayinta dan a tunaninsu ƙarshen aikinta ya zo kenan. Harta Anas sai da yai dariya, shi kam sai da ya cinye abincinsa kafin ya tafi.