SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Suna fitowa a canteen ɗin Yakubu ya ce ” tunda aikin ne bakyaso shikenan. Idan ya koreki za ki san zafin neman aiki ai”
“Haba Yakubu, mutumin nan fa mutum ne amma yadda ku ke zuzuta shi ku ke tsoronsa sai ka ce wani ifritun Aljani”
“Ni dai na gaya mi ki”
Wai da su ka taho da Sister Munibat ma harda ba ta addua’ar da za ta yi idan ta shiga office, ita kan dariya kawai ta yi ta wuce.
……………………..
Tana zama a kujerar ta aka kira, as usual dai cewa yai ta zo.
“Sir gani”
Kallon walaƙanci ya ma ta sannan ya jefa ma ta takardar da ke hannunsa.
“Read it”
Tsugunnawa ta yi ta ɗauko takardar ta fara karantawa a zuciyarta.
“Read it loud” ya daka ma ta tsawa
Haka ta fara karanta ma sa daga farko har ƙarshe. Sai da ta tsaya sannan ya ce ” i’m sure lokacin da aka baki takardar ɗaukan aiki an haɗa mi ki da wannan takardar, but you are so dumb to not have read it. Now, daga gobe ki fara shiga irin yadda aka tsara a dress code ɗin nan. This is a construction company not a fashion show”
“Sir, ni banda kuɗin siyan kaya irin wannan, kuma dai yau na fara aiki balle ace zan samu albashi dan haka sai ka yi hakuri har na karɓa albashi tukunna”
“Miss Salihu you are stepping beyond your limits, dont you dare talk back to me again” ya nuna ta da yatsa
“I gave you a week to find cooperate clothes. A week Miss Salihu”
“Ok Sir”
Hannu ya ɗaga ma ta ta juya ta tafi.
Ta ɗauka zai ma ta maganar abinda ya faru a wajen canteen sai ga shi bai yi ba. Ita kan bonus ɗin ta dama ta riga ta tanadi amsar da za ta bashi idan ya ma ta magana…
Aiki dai ta aikatu dan da gayya ma ya ke sata wasu ayyukan. Sai dai tunda ranar farko ce haka ta haƙura ta dinga binshi a hankali kar ya ce ma ta lazy.
A haka su ka ƙare aikin ranan, ƙarfe huɗu za su dinga tashi dan haka ƙarfe huɗu saura kwata ta fara haɗa kayanta. Kiririnkiririn sai ga telephone na ƙara.
“Mtsww sarkin naci” ta ɗauka fiska ɗaure kamar tana gaban Sir Najeeb ɗin.
Ajiye wayar ta yi ta shiga office ɗin sa. A ranta tana ayyana abin da za ta ce idan wani aikin zai ba ta.
Tana shigowa ya nuna ma ta wata laptop ya ce ta ɗauka ta tafi da shi gida wanda za ta dinga ƙarasa aiki da shi a gida kenan.
“O’o ni Aisha, wato agidan ma ba hutu za kai ba”
“What do you say?”
“Babu, na ce Thank you Sir”
Sai da ta juya za ta fita ya ce “Miss Salihu”
Haɗiye miyau ta yi tareda dunkule hannunta ɗaya ta juyo.
“Fix a meeting with the Sudanese tomorrow”
Wa su Sudanese kuma? Ta faɗi a zuciyarta a fili kuma ta ce “Ok sir”
Ta san ko ta tambaye shi ma ba gaya ma ta zai yi ba dan haka ta bari akan za ta samu Anas ya ma ta bayani…
………………….
Gaba ɗaya a gajiye ta isa gida, Yakubu sai dariya ya ke ma ta wai indai a haka za ta ci gaba ba za ta jima da Sir Najeeb ba dan shi kam aiki ya ke so a mishi tuƙuru.
Bayan Maghrib ta kira numbar da Anas ya bata na wasu Sudanese da ke son haɗa hannun jari da Najeeb. Ta faɗa mu su meeting ɗin su da Najeeb gobe ƙarfe goma.
Su na cin abincin dare Baffa Musa ya aiko a kirata. A falonsa ta sameshi yana aikin lissafi a takarda. Ɗan nesa da shi ta zauna a ƙasa ta gaishe shi.
“Ya aikin dai”
“Alhamdulillah Baffa”
“Allah ya taimaka, iyayen yaron nan sun sameni kuma mun tattauna da su. Na ce su bani lokaci na yi bincike saboda kar a samu matsala irin na baya”
Farida ta rintse ido tana tuno abinda ya faru a baya. Ta ya za ta manta wannan babban al’amari daya faru a rayuwarta.
Maganar Baffa ya dawo da ita.
“Sun ce Asalin su ‘yan Wudil ne amma kuma tunda Kakansa ya dawo cikin Kano da zama ya zamana ‘yan uwan su sunfi yawa anan. Ina so idan komai ya daidaita da yardar Allah da ke da Maijiddah ƙarshen shekara ayi bikin ku tare. Tunda Allah ya sa Saminu ya amince. Na huta da yawan maganganu da ake akanta”
“Baffa wani Saminu kuma?”
“Yaron shagona”
“Baffa auren sadaka za ka yiwa Maijiddah, haba dan Allah sai ka ce wanda ta ke da wani aibu”
“Bance tanada aibu ba. Amma tunda har yanzu shiru ba wanda ya zo neman aurenta kinsan dai ba zan zuba ido ina ganinta haka har a gama auren ƙannenta ba”
“Wallahi Baffa kai bagidaje ne. Wai za ka aurar da ita wa yaron shagonka, irin ta yi kwantai ɗin nan,cab ɗi”
“Tashi ki bani waje. Ba shawararki na nema ba”
“Baffa dan Allah ka saurareni, Wallahi indai ka aurar da ita wa Saminu Jiddah ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali ba. Walaƙantata zai yi dan ya san sadaka aka bashi ita”
“Ban nemi shawaranki ba. Tashi ki tafi “
“Baffa akwai wanda ya ke sonta fa”
“Waye?”
“AbdulWahab sunan shi, ɗan gidan Hajiya Yelwa wanda Jiddah ke wa kitso”
“Hajiya Yelwa?”
“Cikakken sunan sa AbdulWahab Bello Hassan”
Baffa ya ajiye biro ya kalli Farida da kyau ya ce ” na san ki da yawar magana amma ban sanki da sharri ba. Yaushe ɗan gidan Alhaji Bello Kachako ya ce yana son Maijiddah”
“Allah Baffa da gaske na ke, ka tambayi Jiddah”
“Shi kenan, kiramun ita”
Ko da ta shiga ɗaki Maijiddan ta samu tana waya. “Ki je inji Baffa”…
Farida na shirin kwanciya ta jiyo muryan Baffa yana faɗa. Da sauri ta zari hijabi ta fita saboda ƙaramar riga ce a jikinta.
” kin san ko waye shi kuwa?, babban ma’aikacin custom ne fa. Ba na son sharri Maijiddah ki riƙe matsayin ki”
Duka matan sun hallara a falon dan suma faɗan Baffa ya tado su daga matsugunninsu. Maijiddah kam ta kifa kai tana kuka dan ta tsorata da masifar Baban na ta.
“Ikon Allah! Yanzu dan ba ki da mashanshani sai ki yiwa bawan Allah sharri. Ba ki tsaya ma kusa ba sai chan nesa da ke ki ke hangowa. Ni dama na san yawan zuwa gidan Hajiya Yelwan nan kwaɗayi zai sa miki” Anty Hanne ta faɗi tana tafa hannu.
“Munafukai anzo gulma. To ta Allah ba taku ba” ta kalli Baffa ta ce “Baffa ina ni na ce ma ka AbdulWahab na son ta, to ka manta da na yi maganar. Idan gaskiya ce ai ba za ta ɓuya ba idan ma ƙarya ne za a gani. Jiddah ta shi mu tafi”
Jiddah kam tana tsugunne a wajen ko motsawa ta kasa yi. Haka Farida ta zo ta ja ta su ka bar falon…
“Dan Allah ki bar kukan nan, tukunna kukan mi ki ke yi? Saboda Baffa bai yarda da ke ba? Shareshi idan AbdulWahab ya turo ai za su ga zahiri”
Cikin kuka ta ce “Anty Farida wai Baba cewa yai idan ma asiri na ke son yi akan shi gara na bari. Allah ya bani miji Saminu, ta ya mahaifina zai min wannan zargin. Har rashin miji zai sa na koma asiri”
” Jiddah ki godewa Allah, domin addu’arki ta ƙarbu Insha Allah. Ba ga ni ba, ko kin manta abinda ya faru da ni shekaru uku da su ka wuce, i was exactly your age lokacin. Wani surutu ne ba ayi ba, an zage ni an zagi Ummi, hatta Abbana da ke kabari sai da ya samu kason shi. Dan haka ki cigaba da addu’a kuma ki yi ƙum da bakin ki. Duk lokacin da AbdulWahab ya turo su za su ji kunya ai”
“Na gode Anty”
Ta gode Allah da Anty Farida ta yadda da ita lokacin da ta ji record ɗin hiran da su ka yi a waya. Ta rintse ido tana tuno abinda ya faru tsakaninsu duk da kuwa alokacin ba ta cikin hayyacinta saboda firgicewa da ta yi da ganin kyanwa.
Hiran su ta tuno wanda ya sa duk wani baƙin ciki ya kau daga zuciyarta.
” Hauwerh za ki iya auran tsoho?”
“Mi zai hana?”
“wannan tsohon fa shekarunsa ɗai-ɗai har arba’in da ɗaya, ga yaran sa har biyu”
“ai ba tsoho ba kenan”
” haka ki dai ki ka ce gimbiya Hauwerh”
“zan samu amsata anjima ko?”
“sai bayan kwana uku”
“wai-wai har 3days. To, Allah ya kaimu”