SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

amin

Gaskiyarsa ya fi komai birgeta. ” ina son matata sosai Hauwerh, sai dai umurnin Hajiyata ne akan lallai in ƙara aure kafin shekara ta ƙare. Kuma kallo ɗaya na mi ki na ji kin birgeni”

Ta sha ji ana hiran sa idan ta je yiwa Hajiya Yelwa kitso. A yadda ta fahimta matarsa na aiki a Abuja shi kuma da yara su na Lagos, sai ƙarshen wata ta ke zuwa mu su. Wannan ne dalilin da ya sa Hajiya Yelwa ta sa shi ƙara aure.

Kamar yadda Anty Farida ta ce za ta yi shiru har sai ya aiko gidan su. A da tunanin da ta yi shine gobe da safe ta playing record ɗin hiran su wa Baabar ta ta ji saboda ta yadda da maganarta ta kuma yiwa Baba bayani…

……………………

Washe gari ma shigar atamfa ta yi duk da kuwa a dresscode ranar Jumua’a ne kawai aka amince asa kaya native.
Yana shigowa ta bi bayan sa da sauri.

“Sir kana da meeting da Sudanese ƙarfe goma. Sannan akwai wani Mr Habib Olalekan da ya kira ya ce yana buƙatar ganinka na ce ya zo ƙarfe tara”

“What about the files that i asked you to arrange?”

” na gama Sir”

“Bring them here”…

………

Sati ɗaya kenan da fara zuwa aiki. Duk wani kafa da Sir Najeeb ya ɓullo da shi dan ya muzguna ma ta tana shanyewa, acewarta dole ta jure kar ya ɗauka ta gaza aikinta ne. Tsawa da masifa kam tana shan shi kullum.

A ɓangaren Maijiddah kam tunda sauran ‘yan gidan su su ka ji labarin abinda ya faru sai su ka koma tsokanarta da habaici da Matar custom. Abin yana sosa ma ta rai sai dai ba yadda za ta yi tunda dama sun saba tsokanarta. Bisa umurnin Farida ta amince da AbdulWahab. A yadda ya tsara immediately zai tura iyayensa ayi maganar sai dai ta ce ya bari a gama bikin ƙannenta tukunna.

Da sati ta zagayo ta je yiwa Hajiya Yelwa kitso, kunya duk ya cikata lokacin da Hajiyar ta kira ta da ‘surkuwa ta’ da kyar ta iya ƙarasa kitson saboda yadda ƙannen AbdulWahab su ka sa ta agaba da tsokana.

Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro. Dan asabat za a ɗaura aure…

Kallon rainin hankali ya ma ta sannan ya ce “repeat what you just said”

“Sir Najeeb ina son ɗaukan leave na kwana uku. Ba zan zo aiki ba ranan Laraba Alhamis da kuma Jumma’a”

“You are crazy right? Yaushe ki ka fara aiki da za ki ɗau 3days leave?”

Ta yi shiru

“Answer me!” Ya daka ma ta tsawa.

“Sir, bikin ƙannena za ayi kuma…”

“And so?”

“Sir….”

“Get out of my office”….

Washe gari laraba ya ɗauka ba za ta zo ba sai ya ganta. A zuciyarsa ya ce ashe ta san mi ta ke yi. Sai dai ƙarfe ɗaya na yi da aka fita sallah ta yi tafiyarta.

Da ya dawo daga masallaci ya shiga office ya ga takarda akan desk ɗin sa.

Sir na tafi, sai Monday zan dawo. Ka yi haƙuri wannan hidimar ta gida ce dole ayi komai da ni

Duƙunƙuna takardar yai sannan ya cillar ” crazy bitch”
Ya ɗau waya ya kira Anas.

“Hello mutumina ya aka yi?”

“Find another secretary”…

????SAKATARIYA TA????
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Free page

0️⃣0️⃣7️⃣

Hankali kwance Farida ta ke hidiman biki. Anas dai ya kira ya ma ta faɗa akan tafiyarta, acewarsa kwana uku yai yawa sannan ya sanar da ita Najeeb ya koreta sai dai kar ta damu ta zo ranan Monday ɗin kafin nan zai roƙe shi. Ita kam ko ajikinta dan ta san abinda ta shirya wa Najeeb.

Ranan Jumma’a su Ummi su ka zo daga Jos, murna wajen Farida ba’a magana. Ranan Asabat aka ɗaura auren Hajara Musa Wase da Haladu Iliyasu sai Salima Musa Wase da Jabir Muhammad

‘Yan uwa daga Wase da Giyaɗe duk sun zo, da ke Baffa Musa da Baaba Sabuwa duka ‘yan Wase ne. Ita Anty Hanne kuma ‘yar Giyaɗe ce.
Haka aka sha hidima lafiya, duk da an ɗan samu rikici ranan yini saboda magulmata wanda su ka tisa Baaba Sabuwa a gaba kan rashin auren ‘yarta Maijiddah. Maijiddah ta yi kuka har ta ƙoshi duk da ta san akwai alamun kukan na ta ya kusa ƙarewa amma kuma madamar ba auren ta yi ba, ita ko Baabarta ba wanda zai samu sukuni…

…………………..

Shigar Abaya ta yi mai adon duwatsu kalar gold. Gyalensa ta yi rolling da shi sannan ta ɗau jakarta ta fito, gidan dai an watse sai ‘yan tsiraru. Ummi ma ta tafi jiya saboda aiki da za ta koma.

“Allah dai ya sa Sir Najeeb ya haƙura idan ba haka ba kuma kin gama aiki kenan a Najeeb constructions”

“Ya ma isa ya koreni. Lallai! ai Yakubu ka zuba ido kawai ka sha kallo amma yau ko ana ha maza ana ha mata bazan ajiye aiki ba”

Yakubu girgiza kai kawai ya yi ya tada machine ɗinsa su ka tafi…

Sandy mai goge office ɗin Najeeb ne ta cewa Farida Najeeb ya zo lokacin da su ka haɗu, za ta shiga lifter ita kuma Faridan ta fito.

Ta na ajiye jaka ta wuce office ɗin sa. Yana duba wa su takardu ta shigo.
“Good morning Sir”
Ya ji shigowarta amma ya share ko ɗagowa bai yi ba.

“Sir akwai aikin da zan yi ne?”

Sai a lokacin ya ɗago ya kalleta.
“What part of my message did you not understand?”

“Sir na ga saƙo ta email ranan Laraba wai an koreni daga aiki”

Ya ɗaga ido ya ce “and?”

“Ban koru ba mana. Ba laifin da na yi sannan ko na yi laifi ma, tsarin da ka shirya min ya hana ka koreni”

“Listen Miss Salihu. Na san Saboda Anas ki ka dawo, but ki sani. This is my company, just like you Anas is my employee. So, na koreki ba abinda Anas zai iyayi akai. Now get out of this place bitch”

Fita ta yi daga office ɗin ba tareda ta ce ƙala ba. Minti biyu sai ga ta ta zo da takardu a hannunta

“Ga shi nan, wannan takardar shedar amincewarka ce da tafiyata. Wannan kuma kai ka amince zan yi aiki da kai na wata shida ba tareda ka koreni ba, idan har ka koreni to za ka dinga biyana salary har wata shida ta cika kuma……”

“Wait whats this? When did i sign this? I never signed this”

“Ka kalla dai da kyau Sir Najeeb Jibo. Ka san tabbas signature da ke jiki kai ka yi, you stamped and signed it”

“This is bullshit” ya faɗi tareda yaga takardun

Farida ta yi dariya ta ce ” na nawa kuma wannan ma ba original ɗin bane. Original ɗin na nan, so ba inda zan je”

Ta fita daga office ɗin…

Anas ne ya shigo office ɗin ta da sauri “‘yar uwa mi ya faru? Najeeb ya kira ni yanata kwarwa”

“Ce ma sa na yi bai isa ya koreni ba”

“Barin shiga na ji mi zai ce” ya shige office ɗin Najeeb da sauri…

Yadda Anas ya ɗau alamarin fa ba da sauƙi bane. Domin Najeeb faɗa ya ke ma sa kamar tsohon zaki, cewa yai ya kawo ma sa mahaukaciya, yarinyar ba ta ganin girma ko darajar sa.

“Amma Najeeb we’ve talked about this ai, na roƙeƙa ka bata wani chance ɗin”

“To hell with her. I dont want to work with her, can you imagine wannan yarinya ta creating documents ta sa na signing ba tareda na san miye a ciki ba. The girl is a crook, she’s just….”

“Haba yallaɓai. Duk wannan tashin hankalin akan mace, ban sanka da haka ba”

Najeeb ya kalli Anas ido cikin ido ya ce ” get her out of this office or i will use force, and you know i will do it”

Ganin yadda Najeeb ya bircike ya sa ya fita ya samu Farida ya ce dan Allah ta koma gida zuwa gobe idan Najeeb ya huce zai kirata sai ta dawo. Farida ta tafa hannu ta riƙe ƙugu ta ce “Ya Anas ba inda zan je. Ai yau idan bai haƙura ba zai ga haukata muraratan. Ba ri ma kaga”

Ta wuce office ɗin Najeeb.

“Ka ga Sir Najeeb kar ka bari na nuna ma ka haukata anan, kai shikenan ba dama mutum ya ɗan yi ƙaramin laifi sai ka ce kora, to yau ka gamu da gamonka. Ba inda zan je idan ka takura kuma na shigar da kai ƙara tunda da izininka na tafi hutu” ta san hakan zai iya faruwa shiyasa ranan laraba da ta zo ta typing documents ɗin ta haɗa cikin wasu da zai signing shi kuwa ko dubawa bai yi ba ya dinga signing ɗin su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button