SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Well lets see how tough you are” ya faɗi tareda ɗaukar waya ya kira security.
Anas da ya shigo office ɗin ya fara bashi haƙuri. “please dont do this. Ba girmanka bane wallahi. Za ta bar maka aiki amma banda koran walaƙanci dan Allah”
Farida ta ce ” Ya Anas ka barshi, security ɗin su zo ina nan ba inda zan je”
“Farida ki yi shiru ki fita, i’ll handle this”
“Yadda ya ke ji da taurinkai ni nawa ya ninka na shi. Mun fafata da arnan Jos ma balle shi”
Ana haka sai ga wasu murɗaɗɗun security sun shigo, dukkan su biyu da ka gansu ka san basu da mutunci da alama ma ba musulmai ba ne.
Najeeb ya tashi ya zo gaban Farida ya ce ” for the last time, LEAVE”
“Allankatafir ba inda zan je”
Shi kam Anas baza ido kawai yai yana kallon wannan dramar.
Najeeb ya dubi securities ɗin ya ce ” throw her out of my company, i dont want to see her here again”
Ɗaya daga cikin securities ɗin ya nufo ta yana ƙoƙarin riƙe ta, aikuwa ta yi tsalle ta faɗa jikin Najeeb ta cukwuikuyeshi tana ihu tana faɗin wallahi ba zan fita ba ko za a kashe ni.
Najeeb ya rintse ido lokaci guda kuma hankalinsa ya tashi. Cikin zuciyarsa ya ke mamakin abinda ya faru, ba wai rungumeshin da ta yi ba, sai dai effect ɗin da rungumar ya jawo ma sa. He cant believe he got erection because of this crazy girl.
Security ɗin ya kai hannu zai janyo Farida daga jikin Najeeb, Anas ya daka ma sa tsawa ya ce su fita daga office ɗin.
Najeeb har lokacin idonsa a rufe, ya rasa ya zai yi, he’s afraid of pushing her away saboda Anas da securities za su ga yadda engine ɗinsa ta miƙe. He cant embarrass himself infront of this crazy girl dan haka cikin hikima ya sa hannu ya turata da ƙarfi before you knew it ya juya da sauri yai hanyar banɗaki.
Anas da ke recording abinda ke faruwa yai kan Farida da ta faɗi ƙasa warwas. ” sorry ‘yar uwa, tashi” da ƙyar ta miƙe da taimakon Anas saboda ƙugunta da ya bugu sosai…
Ya ƙara zuba ruwa a fiskarsa a karo na ba adadi. Ya kalli kan sa a madubi sai lokacin ya ga yadda jacket na shi ya ɓace da janbakinta.
“This girl is a witch. How could this possibly happen?”Rabon shi da shiga yanayi irin wannan ma ya manta….
“Oga ka fito ayi magana, ka haƙuran ne ko dai” muryan Anas ya katse shi.
Ajiyar zuciya yai sannan ya fito riƙe da jacket a hannunsa yadda ya riƙe ka ce kashi ne ajikin jacket ɗin. Yana fitowa Anas ya sa dariya.
“Get out Anas, i dont want to see anyone”
“Ka huta mutumina irin wannan al’amari sai da hutu ai”
Najeeb ya wurga ma sa jacket ɗin. Anas ya chafe ya ce ” wannan jacket ɗin ta tarihi ce”
Sai da ya kai bakin ƙofa ya ce ” kar ka manta za ka saurari presentation daga Team D ƙarfe goma. Zan sa sakatariyarka ta tuna ma ka idan lokaci ya yi”
Najeeb ya ce ” Anas i’ll kill you”….
Anas na fita ya samu Farida ya ce ” gaskiyar Yaks da ya ce ke da Najeeb fire and fire ne sai dai gaskiya ta ki wutar ta fi tasa zafi. Kar ki bari kowa ya shiga office ɗin sa sai nan da 1hr kafin nan ya huce”
Farida ta amsa da ” ok”
Ko ajikinta dan ta san haƙarta ya cimma ruwa…
Yana zaune ya sa hannu a ƙirjinsa yana shafawa ashe yarinyar nan har cizonsa ta yi, da ya duba wajen a madubi yai wani jaa abinka da farin mutum.
“She’ll pay for this, i’m not sending her away. Not until she suffer, i’ll make sure she cry and cry and cry”
Yana zaune ya kunna laptop ɗin sa ” lets see what the witch is doing”
Tana zaune tana danna waya ga biscuit agefe tana ci. Har zai kashe sai ya tsaya saboda shigowar Khalidah da ya gani. ” another bitch” ya faɗi a ran sa…
Kai tsaye hanyar office ɗin Najeeb ta yi Farida ta ce ” Malama tsaya”
A gadarance Khalidah ta juyo “and who are you?”
“Idon ki dai bai makance ba ina?. Kin san dai aikin wanda ke zama a kujeran nan ko”
“Ya kamata ki sani, matsayin ki bai kai ya hanani shiga office ɗin Najeeb ba”
Farida ta taso ” Sir Najeeb ya ce bai son ganin kowa sai nan da awa ɗaya dan haka. Ko ke wacece sai dai ki dawo anjima”
“Ki hanani shiga idan kin isa?” Khalidah ta faɗi tana ƙoƙarin shiga. Farida ta sa hannu ta jawota da ƙarfi.
“Ki riƙe matsayinki Malama, ko kuma wallahi ni da ke sai mun kwashi ‘yan kallo”
“Ki matsa na shiga. Ke kin ma san ni wacece a kamfanin nan?”
“Najeeb constructions na gani ba Najeeba constructions ba dan haka duk matsayinki a ƙarƙashin mai kamfanin nan ki ke”
“Hmmm za ki sha mamaki yarinya, ko kwana ɗaya ba za ki ƙara anan ba Najeeb zai koreki, wanda su ka fi ki nitsuwa ma ba sa daɗewa balle ke shashasha”
“Eh na ji dai. A bi doka a zauna lafiya”
Khalidah ta yi tsaki ta fita. Sai da ta tafi Farida ta ja numfashi ta ce ” wai! na sha da ƙyar. Wannan matar fa ta riƙe ni ba ƙaramin jin jiki zan yi ba. Allah ya yi halitta anan”
Najeeb da ke kallon komai ya ce “scary bitch”…
…………..
Ƙarfe goma saura minti biyar ya fito daga office ɗin sa.
“Sir na biyo ka ne?”
Bai kulata ba ya fita bayan ya harareta.
Da ya tafi ta ce ” ka ji dashi, ni kam kujeran nan tawa ce ina nan daram da kai”
Lokacin da zai dawo tare su ka dawo da Khalidah. Su na shiga office ta cigaba da bayanin abinda Farida ta ma ta sai dai hankalin sa ma baya gareta yanaga takardun da ya shigo da su.
“Najeeb ba ka ce komai ba”
“She’s doing her job” ya faɗi ba tareda ya kalleta ba
“Najeeb yarinyar nan ‘yar iska ce, ƙila ma ‘yar ƙwaya ce kaga ɗazu wai za ta yi kokawa da ni idan na ce zan shiga office ɗinka”
“So?”
“Najeeb ka koreta, ina wancan Joseph ɗin nan da ya ke aiki da kai kafin na yi tafiya”
“Look Khalidah, i fire who i want to. For now that girl stays”
“Najeeb i demand you to sack that girl”
Da ƙarfi ya buga desk ɗin gaban shi.
“Look Khalidah, dan mahaifinki yanada 8% share a kamfanin nan doesnt mean you can make rules here. I owned 75%, i make the rules here. Understand that or ask your father, he’ll explain to you. Now get the hell out of my office”
Khalidah ta fice fuuu cikin fishi.
………….
Cikin sati uku da Farida ta fara aiki a Najeeb constructions ba wanda bai santa ba. Wanda su ke tunanin ba za ta jima ba sai gashi har sati uku, shi kan sa Anas yai mamakin yadda Najeeb ya haƙura da Farida. A zuciyarsa kuma yana ganin kamar akwai lauje cikin naɗi.
Babban matsalar Farida a office ita ce Khalidah, a second floor ta ke amma kusan koyaushe tana third floor. Magulmatan kamfani su ka sanar da Farida cewa Khalidah son Najeeb ta ke, lokacin da ta zo ta yi service ɗin ta a Kamfanin ta haɗu da Najeeb tun daga lokacin kuma ta ƙi tafiya, da ke dama mahaifinta na da share a kamfanin sai ta samu ɗaurin gindi. Shekararta uku a Najeeb constructions amma ba alamar nasara sai dai ta ƙi haƙura…
Ta gaji da cin abincin canteen kullum sai kashe kuɗi ga abincin a zuba ma ka kamar kana roƙo duk da ma mafi yawancin lokuta Engr Mathew ko Arch Hamza wani cikin abokan Yakubu ke siya ma ta. Ba ma wannan ba abincin ma bai ma ta yadda ta ke so ba.
Ta zuba faten doya da ya ji ganyen alayyaho da kifi a plate. Gaba ɗaya ƙanshi ya baɗe office ɗin, ta na ci tana korawa da zoɓonta mai sanyi a haka Najeeb ya shigo. Bai ma ta magana ba ya shige office ɗin sa, yana shiga ta ji kira. Tsaki ta yi ta ce ” yana gani fa abinci na ke ci” haka ta ajiye ta shiga office ɗin sa.
“Miss Salihu. The next time you eat in the office, 10% zan cire a albashin ki. Is that clear?”